Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 20

Sponsored links

Har Kamal yaja motar Bai kuma cewa komai ba kuma daman Tun fil azal shiba mai yawan maganar Bane ba.

Ameerah ta kafe shi da idanu ta cikin madubin Motar gaba ɗaya ya tafi da dukkan Imanin zuciyarta Tsananin son shi na kuma fisgarta Jitake kamar ta dauwama a haka tana ta kallon shi Jinta take tana yawo acikin Duniyar gajimare Wata biyar Ɗin da yayi bai zo gida ba Taga yaƙara cika da kyau Hutu ya kuma ratsa shi kamar ba soja ba.

Tana jin ko a mace ta Huɗu ce zata zo masa Indai zai aure ta bata Biyu ba.

Duk hirar da su Naja keyi Ameerah bata Jinsu sai ma ƙara Tsira masa idanu da tayi tana kallon shi jita ke kamar ta Cinye shi ɗanye.

Dama Zuciyarta zata bar jin tsoron sa data tunkare shi da kalmar so! sai dai tsananin Tsoron da take yi masa yasa Ko haɗa idanu bata iyayi dashi Inda Allah ma ya temake ta Antyn ta taiwa Mama maganar ta wanda Mamar tai musu alƙawarin Ahmad dole ya aure ta bayan ya auri Matar shi ta farko.

Tuna wannan Batu yasa ta sada kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta daya sha jan lalle wanda tayi shi Jiya don Ahmad ya gani.

A haka suka ƙarasa Gida Ko parking bai bari Kamal ya daidaita ba ya Ɓalle marufin Motar ya fita yana Jan tsaki ƙasa ƙasa

Ya kula Yarinyar dake kusa dasu Naja ta kafe shi da idanu wadda bai ma gane kowa ce ba sabida yaga yaran Gidan nasu nada yawa Baya son raini ko kaɗan ya lura yaran Yanzu Idanun su ya buɗe da Son maza.

Kamal ne yabi shi da jakar shi bayan ya kashe motar Suma Su Naja haka suka fito daga motar bayan sun tashi Ameerah wanda a zaton su duk bacci take Yi wanda ita ba baccin take ba tsabar Tunanin soyayyarta ne yayi mata yawa.

Haka suka ƙarasa gida da sauri tai ɓarin su har tana haɗawa da Gudu tana kiran Anty mahaifiyarta da ƙarfi.

Cikin sauri Anty ta fito tana Kama Ameera tana cewa.

“Ke lafiyar ki? kika shigo min gida haka kamar wata sakarai?”

Janyo Anty tai Cikin falon su suka zauna sannan ta dube ta.

“Anty yaya ya ƙara kyau daga gani yana cikin kwanciyar hankali Anty dan Allah ki ƙara min ƙoƙari akan shi Anty tunda na tashi da soyayyar yaya na taso a rayuwata kina kallo bana kula kowani namiji sabida shi dan Allah kiwa Baffa magana akan shi koze sami Alhaji da maganar mu”

Ta ƙarasa maganar tana jan Numfashi mai ƙarfi.

Tsananin tausayin yarinyar ne ya kama Anty Ameerah ƴarta ce ta fari wadda tafi soyuwa fiye da dukkan ƴaƴanta acikin zuciyarta dan haka dole ta Bawa ƴarta abinda take so koda zata rasa komai nata ne a rayuwa.

“Ki ƙaran haƙuri Ami, munyi magana da uwarsa ki bari muga auran nashi daga nan sai muga gudun ruwan su, Babanki kuma kinsan baze magana ba kinsan haƙurin su yayi yawa dukkan su sanyi gare su dan haka kada ki damu nai miki alƙawari Ahmad Sai ya aure ki koda tsiya koda tsiya tsiya! dan na fahimci kamar da rainin hankali a wajan uwarsa kawai ta faɗan hakanne dan tasa hankalina ya kwanta, Shima kuma Ahmad bawai Ganin girma na yake ba Dan na fahimci Duk sanda zaizo Ko kallon sashin nan bayay bare yazo ya gaishe ni sai dai ya tari Baffan sa a waje su gaisa Duk yadda nake wa uwarsa baya gani Inma ya ganni a wajan uwarsa haɗe rai yake yayta janta da hira su barni zaune ni kaɗai”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button