Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 46

Sponsored links

Hadima Banou na fita a falon ta sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya da kai hannu ta yarce gumin dayay sharkaf a goshinta kamar wadda ta tiƙi surfen gero. Gaba ɗaya manyan idanunta masu saka tsigar jikin mutane tashi sunyi jazur. Gefe ta koma ta zauna a ranta tana fatan ALLAH yasa har Iffah ta tafi Malikat Haseena bazata nemeta ba. A ganinta ma tai zamanta anan koda an nemetan ai sai an ganta. Wannan shawarar data yankema ranta ya sata cigaba da zama a wajen har lokacin jikinta bai gama komawa dai-dai ba….

Gaba ɗaya Iffah kasa sakewa taci abincin tai saboda kunya, ganin haka cikin hikima Malikat Haseena ta cigaba da ɗan jan ta da hira domin jan ra’ayinta, itako tana amsa mata a kunyace da tsakurar abincin. Suna a haka Daneen Ammarah ta shigo, itama dai ta nuna jin daɗinta na ganin Iffah ɗin tare da jin kaunarrta har cikin rai. Zama tai itama aka ɗora cin abincin da ita suna yar hira jefe-jefi da Malikat Haseena. Iffahn dai nata saurare kawai, sai kuma murmushi. Rabin hankalinta kam nacan wajen tunanin hadima banou da yanayin ta….

Kamar yanda Barrister yayma su kaka alƙawari ya samo Ibrahim Askari ta hanyar mutumin nan da suka fara zuwa wajensa. Fuskarsa cike da murmushi yake dubansu, dan tun yana can ya sanarma Abu Zainab su haɗu a office. Sai gashi kafin ya iso ma su har sun iso. Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi ba ya fara musu bayani.

“Alhamdulh an samo Ibrahim Askari, ya kuma bani cikakken adireshin Dawood ɗin, hasalima yace shiyya sayar masa da gidan daya koma ɗin. Ga adireshin gidan ya bani”.

Sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Kaka. Ya dinga jerama Barrister addu’a da fatan alkairi. Shima dai Abu Zainab yayi masa godiya, tare da ɗorawa da faɗin, “Barrister yanzu mune zamuje can ɗin? Kokuwa kai ne?”.

“Mu duka babu wanda zai je Zakariyya”.

Kallonsa sukai su duka, ya jinjina musu kansa da buɗe wani littafi a gefensa ya yago takarda, ɗan rubutu yay da sake ɗagowa ya dubesu. “Kamar yanda na faɗa muku mu duka babu wanda zaije. Domin ita Shari’a takanzo saɓanin hankali. Sannan bamu san nasu shiri ba, zasu iya amfani da duk wani yunkurinmu a yanzu. Dan haka nayi abinda ya dace bayan barina wajen Ibrahim Askari. Akwai wani babban police dana sani kai tsaye naje garesa, nakumayi sa’asar samunsa. Nayi magana dashi da rokonsa ya bincika mana inda zamu iya samun su, Alhamdullah kuma ya amsa, yanzu haka kiransa nake jira kamar yanda yaymin alkawarin kafin cikar awa ɗaya”.

Anan ɗin ma dai farin ciki ne a fuskokin su Kaka, sai faman sauke ajiyar zuciya sukeyi…..

Zamu iya cewa gaba ɗaya yinin yau Iffah ta kare shine a neman number Malaminta Fawzan da abokinsa Ajmaal. Amma abin mamaki har yamma amsa ɗaya ce layukansu not available. Gaba ɗaya tayi firingai-firingai na damuwa, duk yanda take ƙoƙarin ɓoyewa da danne hawayenta sai da suka zubo bayan ta idar da salla. Bakomai yasata shiga damuwar akan son samunsu ba sai rashin samun number Babiy da Hanash da batai ba suma. Tana son jin wani abu game da ahalinta, dan yawan faduwar gaban da take da mummunan mafarki yasa tanaji a jikinta akwai matsala. Tama rasa wane tunani zatayi, har text message ta turama Malam Fawzan akan ya taimaketa ya duba mata iyayenta amma shiru kakeji, bama tada tabbacin ya gani ko bai gani ba. Kuka taci sosai a wajen kafin ta mike tana share hawaye bisa shawarar zuciyarta. Wayar ta sake ɗauka ta sake tura sakon data turama Malam Fawzan a layin Ajmaal abokin nasa. Tana fatan ɗaya daga cikinsu yaga saƙon koda bata samu sauran biyan bukatarta ba. Jikin window ta koma ta tsaya tana mai shaƙar iskar dake busowa mai daɗi, kamar ance kalla gefe ta hango Hadima Banou can jikin filawoyin saitin ɗakin Malikat Haseena tsugunne kamar tana tona rami, sai faman waige-waige take alamar rashin gaskiya. Da farko tsura mata idanu Iffah tai, sai kuma ta zabura bisa umarnin zuciyarta. Sai da ta tabbatar wani baiga sanda ta fito a dakinta ba sannan ta fice, kasancewar ta naɗe har fuskarta da ɗan kwalin abayar jikinta yasa babu wanda ya ganeta, balle abayar jikin nata ɗaya daga cikin natane na gida data canja bayan barowarta wajen Malikat Haseena. Da ƙyar ta gane hanyar dazata ɓulla bayan, dai-dai Hadima Banou na ƙoƙarin maida kasar data tone alamar harta saka abinda zata saka. Sauri-sauri takeyi harta kammala, ta ɗago da nufin barin wajen taja ta tsaya a kiɗime ganin mutum tsaye a bayanta. Amma kasancewar ta mai shegen tsurin ido sai ta dake a zahiri tana kallon Iffah da har yanzu bata janye mayafin data yane har fuskar ba….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button