Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 95

Sponsored links

kallon.

 

Zamansa kusa da ita da saukar numfashinsa a gefen wuyanta ya sata yar zabura harda shirin fasa kara.

 

Guntun murmushinsa din nan kamar na dole ya saki yana rikota. “Hy relax”. Ya fada cikin rada kamar mai tsoron aji su.

 

Idanunta ta rumtse da karfi ta sake budewa zuciyarta na wani irin gudu da sauri-sauri dan ta toratan fa da gaske. Cikin tura baki ta juya idanunta da har yanzu basu gama bajewa gaba daya ba tai masa yar hararar data nema tsarga masa zuciya. A hankali ta ce, “ALLAH kaban tsoro ka nema afuwa na”.

 

Yanzun ma murmushi ya sake yi, batare da yace komal ba ya gara zamansa yana daura kansa a kafadarta idanunsa akan television da take kallo. Cikin rada-dara da kamo hanunta da ke cikin popcorn din ya kai wanda ta dakko guda daya bakinsa yana fadin,

L

“Babu tayi ne?” ya kare maganar da kallonta. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallon da take masa ta maida ga tv cike da basarwa, a shagwabe ta ce, “Gashi kaci ba’a baka ba. Ina vini”.

Idanunsa va dan lumshe da budewa va tashi da kyau yana matsota jikinsa sosai kanta da bayanta suka koma saman kirjinsa, yayinda take a tsakkiyar kafafunsa. Ita duk jitai zaman ma ya bata kunya, amma ya ta iya dole ta dake dan Mamy ta mata nasiha sosai akan ta saki tiki da milinta karta bada wata kofa da zai y dana sani kan auranta ko tunanin mallakar wata mace saboda gazawarta. Kafarsa daya ya ajive a dan dogare yanda ta sake samun jin dadin zaman. Kusan mintuna biyar bai sake cewa komai ba itama bata sake ba idanunsu duk suna a tv. Yayinda yake kamo hanunta da take dibo popcorn din yana kaiwa bakinsa. Cikin maganar nan tasa kamar ta dole ya ce, “Kinci abinci?”.

Kanta ta daga masa tsigar jikinta na tashi saboda yanda yay maganar cikin kunnenta. Hannunsa na dama ya sakalo saman cikinta yana shinshinar wuyanta. “Ban yarda ba, mi kika ci?”.

Cikin yar in ina da son janye jikinta amma ya hana hakan ta ce, “Mammy ta bani gasashen jan nama da madara”

“Uhm yar gatan Mammynta. Shine baki rage mun ba kuma? Gashi ina jin yunwa sosai banci komai ba tun wanda kika tsammin”.

Ita gaba daya jitake kamar an canja mata shi da wani ba Shahan-shan din nan miskili mai shariva da magana ma sai ya jinjina ta ba kafin yayi, duk da a yanzun ma daddaya yake yinta kamar abun dole.

Kasa cemasa komai tai, dan gaba daya ita yamasa ta daina fahimtar film din ma. Shi kansa baima san mi yake ba, abinda kawai ya sani ta gama mamayesa da komansa. Tsananin begenta yake da jin kishin sake kasancewa da ita. Amma zai daure bazai aikata ba kodan tausayinta, ballema dinki da akai mala. Da. kyar ya dan dai-daita kansa, itama cikin dan rawar murya ta ajiye popcorn din zata mike. Riketa yay kamar mai tsoron ta gudar masa (g . A shagwabe tana narke fuska ta dubesa, sai kuma ta risinar da idanun da take kyakykyaftawa, “Zan samo ma abincin ne fa”. A hankali ya saki hanun nata yana lunshe idanu da sake budewa a kanta gaba daya laurun idanuma ya canja Yanda take tafiya kaman a hahharde kuma a hankali yabi da kallo, tausayinta duk sai ya sake mamayesa.

Yaso ya dakatar da ita, amma sai maganar kuma ta masa wahala dan yunwar kuma yakeji da gaske. Tan madarar da ya sha a wajenta da dan naman nan bai sake cin komai ba. Koda ya shigo bayan sallar la’asar kuwa baiko kalla dining room din ba ya shilge. Wanka kawai yay ya canja kayansa ya taho dubata tuna vasan a vanda ya barta sharban da safen nan..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button