Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 20

Sponsored links

Shiru dukkaninsu sikayi sbd daman sunsan bazai wuce Alh bilal dinba dan haka kowannensu ya sake shiru sbd basusan mafitar wannan qaddarar ba data rigayi fata.

Cikin rudewa da tashin hankali Annen batama san me dame take fada ba ta fara fada ciwonta na neman tashi sbd kanta da yayi nauyi neman juyewa yakeyi

Benazir ta taso ta dawo gurinta da sauri tana kwantar mata da hankali sbd kar ciwon ya tashi komai ya lalace asan halinda suke ciki.

Har gari yayi haske suna daki suna fama da kansu ba sauki ko kadan dole Benazir ta fito ta hau aikin gidan gabaki daya ba maganar zuwa makaranta sbd tsoron fita takeyi ma tabarsu kada kafin ta dawo Ababa ya sani ta dawo ta tadda babu su ga kuma yanayin Annen daketa surutai cikin tashin hankali da fita hayyaci

Sumayyah ma idanuwanta sunkai ko budewa basayi sosai sbd kumbura ga yanayinta na rashin lafiya.

Abincinsu na dare da basu ci ba haka suka zauna su ukun suka turasa cikinsu da sanyinsa harma ta sakewar daya fara yi sbd kada su fitar a san basu ci a fahimci suna cikin wani halin a gano.

Babu mai dadin rai ko nutsuwa a cikinsu haka kowa ya ringa diban abincin yana turawa bakinsa bame magana suna gamawa Benazir ta dauki kwanon ta fice taje tafara wanke wanke.

Annensu zaune take a dakin nasu ta kasa fitowa idanuwanta sunyi ciki ciki tsaban kuka da damuwa ta rafka tagumin da basusan yanzu kuma yanda rayuwa zatayi dasu ba.

Sumayyah kuwa ciwo ne yake cinta sosai amma tashin hankali da damuwa ya hanata nunawa itama tagumin ne ta rafka dukkaninsu kaman wainda ke jiran sakamakon mutuwa.

Benazir ma ayyukan gidan takeyi ba’a cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba kowannensu tinanin makomarsu yakeyi.

Sai bayan sallar Azahar ta kammala aikin tayi wanka da alwala tazo tayi sallah aka basu abincinsu data gama girkawa ta kawo ta ajiye musu dole sukai sallah suka zauna suka turawa cikinsu babu me jin dandanon komai a bakinsa cikinsu kowa ‘dacin bakinsa yakeji musamman Sumayyah da nata ya hada dana ciwo da laulayi.

Tsit Hande taji gidan yayi suna daki babu me iya motsin kirki sbd damuwa da tinani dan haka ta fito tana qwala kiransu tana tambayar lafiya suke zaman daki kaman masu abin kunya.

Tsit Hande taji gidan yayi suna daki babu me iya motsin kirki sbd damuwa da tinani dan haka ta fito tana qwala kiransu tana tambayar lafiya suke zaman daki kaman masu abin kunya.

Tsinkewa cikinsu yayi Anne ta kalli Benazir da itama ita ta kalla suka kalla sumayyah a tare kafin Anne ta bude baki cikin mutuwar jiki tace

“Ki zauna a dakin karki fito”

Gyada kai Sumayyah tayi tana rintse idanuwanta sbd kunyarsu dake cin zuciya da ganganr jikinta gashi ta kasa ko bude baki ta fada musu kaddara ce da shedan daya shigo ciki.

Anne da Benazir ne suka fito sbd kada hande ta tsananta maganar.

Kallansu tayi taga duk sun jeme a dare daya kaman wainda sukai kwanan zaune,

Fuskar Benazir ta kalla taga yanda ta sauya kwata kwata da alamar bata rintsa ba kuma harda alaman kuka bayan rashin baccin.

Kan Anne ta maida kallanta taga itama fuskarta tayi jajir ta kumbura,

Shiru tayi tana nazarinsu sbd da alamar akwai abinda ya samesu dan duk wuya duk tsanani su biyun nan basu cika kuka ba sbd Anne ta dade da samun rashin lafiyar rashin kuka sbd shekarun data debo a rayuwar gidan zuciyarta ta mace bata iya kukan hakama Benazir sbd taurin rai da juriya ba qaramin tashin hankali da masifa ke sakata kuka ba amma yau gashi da alama kukan suka kwana yi..

“Kodai sumayyah ta mutu ne tsakar dare?” Tayi tambayar kai tsaye tana kallan hanyar kofar dakinsu da mamaki.

Anne wani numfashi mai sanyi ta sauke zuciyarta na sosuwa da abinda Handen ta fada tayi qasa da kanta tana kasa cewa komai.

Benazir ma numfashin mara sauti mai dumi ta sauke tana girgizawa handen kai tace

“Shine kuka kwana kuna kuka ko me? Ta sake jefa musu tambayar tana kallan Benazir da idanuwanta ke sake yin qasa

Shirunsu yasata rufesu da fadan batasan dabiar koke koke a cikin gidan da ba mutuwa akai musu ba.

Fada ta ringa yi sosai sai data gaji ta dena tace su wuce ga wankin shagon Ababa can an kawo.

Wucewa sukai inda manyan kullin kayan wankin masu yawa suke suka warware suka ringa kwashe kayan zuwa inda suke wankin.

Benazir ce ta fara debo ruwa masu yawa ta tara musu

Suna fara wankin Anne ta sunkuyar da kanta qasa wani irin kuka mai sauti na subuce mata mai tafe da tsananin ciwo da quncin da zuciyarta take ciki

Benazir radadin sautin kukan mahaifiyar tata ya sata kasa wanke kayan dake hannunta tayi qasa da kai itama wasu hawaye na tsinke mata,

Me zasuyi?

Meye mafitar halinda suke ciki?

Ya Allah ka dubi maraicinsu” shine abinda zuciyarta kawai ta iya fada sbd sunsani sun tabbatar mawuyacin hali ne suke ciki mai nauyi.

Saida sukai kuka sosai kafin suka hakura suka fara wankin babu mai magana har suka wuni sunayi sai gab da magriba suka gama sbd abincin dare da Benazir ta dora tanayi tana tashi.

Daki suka shige bayan sunyi Alwala abincin dare kawai sukaci sukai ishai da akai suka lafe dakin babu wanda ya sake fitowa saida Ababa ya dawo Benazir ce ta fita taje takai masa abinci da ruwa ta dawo dakin suka cigaba da zaman damuwa.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button