Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 33-34

Sponsored links

A kasa ya zube ya gaida Umma da su Aunty ma sauran ma suka gaida shi,bayan ya zauna aka kawo Mana ruwa da lemon da su Aunty Bilki Suka siyo Bilkisu ta fita ta shiga kitchen sune suka Yi girki aka kawo mana tuwon shinkafa danya miyar egusi sai meet pie me kyau, nace mun fa koshi,Aunty Bilkisu sai bala’i ai ba sai kin nuna mana mu talakawa bane dama ai mun San bamu Kai kici abincinmu ba kunfi karfinsa amma dai ke in baza kici ba ai su zasu ci,aikin banza duk Dan gidan nan inda yake sai ya nuna hali haba,Baki na bude nace ni daga nace na koshi sai ki kamani da fada haifata Kika yi,ciki ne dani ko baki gani ba abinci sai mai da yaji nake ci gashi Nan me cikin ki tambaye shi kiji,Nawwar yace kuyi hakuri bata cin abinci sai mai da yaji,Umma tace ko kunya babu Rabi kike ko,cikin shine abin kunya ni da ba shege nayi ba da ubansa kowa yasan dai me akeyi a samu ai aure nayi,Nawwar shi Kuma yace ae da auren mu Umma,su basu Saba Jin rashin kunya haka ba da tarbiyyarsu Kuma a Arewa suke da saukin fitsara sannan a gaban Mahaifiyarsu Suka taso,Bilkisu ta share zancen tace amma ai kwana zakuyi ko? Nace a’a Ina Zan iya kwana gashi nan ku tambaye shi idan zai yarda to bai Saba barina unguwar kwana ba na tafi na barshi da wa da dare fa a’a bazan kwana ba nikam, Umma tace ke a hannun wa Kika taso ne haka Rabi baki da kunya haka,Baki na turo nace ni nace ku jefar dani da Kun San da haka kuka jefar dani sai yanzu an ganni na girma na zama abar moriya za ace bani da kunya tuntuni ba sai a rikeni a bani kunyar ba,shi waccen mutumin me Jin haushina waye ne haka,Umma tace babanku ne mahaifi,nace Ni ku bani labari na sani nice yarku ko ba ni bace,Umma Ido ta tsura min ta fara bamu labarin asalinmu.

Tace Mahaifinku dan Asalin Nasarawa Lafiya ne a wani kauyen Fulani rugar Jam,Mahaifinsu da Mahaifiyarsu Abu wacce ake Kira da Uwa su Tara Suka Haifa bakwai Mata biyu maza yanda ita kanta Abu Uwa kenan dukkan Iyayenta Mata Suka Haifa mutum Daya ne Namiji a ciki su hudu Mata namijj daya Kuma duk suna nan da rai ita Uwa itace Babba a cikin Yan uwanta sai Sa’ade,Baballe da Binta Uwa Kuma data yi aure danta daya tal ta Haifa a Duniya Muazu shine Mahaifinku Abba kenan tun yana matashi mahaifinsa ya rasu Bayan sun dawo Kaduna da Zama sakamakon fada da ya barke tsakanin Fulani da manoma gaba Daya kusan Dangin Mahaifinku suna nan Kaduna Wanda basuyi aure ba ma duk a nan suka Yi aure,Uwa ta Sha wahala da Danta sabo da bata da miji sai Yan Uwa ne suke taimakonta lokacin ma a gidan haya take,sabo da danta ta kasa yin aure Wai Kar ta auri wani mijin ya tsanar Mata da tunda mazan yanzu ba kowa ke son yayan wani ba,tana sana’oi kala kala da haka ta dauki nauyin Danta har ya gama Secondary sannan aka turashi makarantar Allo can Kano har ya Zama katon Saurayi Yana Almajirci ya samu wata Hajiya ta dauke shi Yana Mata aiken gida a can har ya Isa aure a wancan Zamanin kenan.

Ni Kuwa Yar Asalin Taraba stare ce can Gembu kusa da Cameron Fulani ne usul ,iyayena ni kadai Suka Haifa tunda aka yayeni babana ya rasu sai Mamana Muna rayuwar mu nayi makaranta zuwa matakin secondary sai karatun Islamiyya Ina tallan fura da nono har kawar Mama tace tunda bamu da kudi Muna Shan wahalar Rayuwa me zai Hana a kaini gidan masu kudi wanke wanke da shara,Mama ta amince nima ita murna Zan zauna gidan masu kudi,Allah yayini da masifa kaf kauyenmu ba a taba ni a kwana lafiya bana yarda,aka samo min aikin wanke wanke da shara a Kano aka kaini gidan da Abbanku ke musu aike da wanki da guga,Hajiyar gidan da mijinta suna da mutunci matuka suna da dansu guda daya shine bashi da mutunci gashi suna ji da shi,lokacin ya so ya lalata min rayuwa Saura kadan ma yayi min fyade Allah ya kiyaye Abbanku ya kamashi ranar ya daku a wajen Muazu Almajirinsu duk da cewa kullum cikin fada muke da Abbanku Muna kishin juna shi Yana Dan aike ni Kuma nice me girki da gyaran gida.

Dama gashi masifaffe nima masifaffiya har kokawa mukeyi dashi sabo da rayuwar yanzu da ta baya ba daya bace yanzu anfi lalacewa,Watarana idan Zan bashi abinci sai na zabo nama me tauri ko Kashi shi zan sa Masa yayi ta faman wahala da hakoransa ba zagin da baya min akan haka,idan Naga dama ma Sai naci Nawa na rage jagwalgwalona sai na dan gyara shi na Kai Masa a wulakance,Dariya Muka dinga Yi Ni da su Nawwar irin muguntar Umma data dinga hadawa Abba,taci gaba tace shima duk Sanda aka aikeni na fita to bazai bude min gate ba sai rana ta gasa ni na Sha wahalar gaske sannan zai bude min kofa Watarana ma Sai dai Hajiya taji ihu na tazo ta bude min,Watarana Ina wanki yazo ya kwaso min kayansa ya tsaya da bulala a kaina yace sai na wanke Masa shima ai ya girmeni,Ina wanki Yana tsula min bulala a gadon bayana ta Dole na wanke masa tunda shi Namiji ne ya fini karfi,Muna wannan zaman kullum fada tsakaninmu har na fada sonsa ban sani ba,shi kuwa dama bai damu dani ba duk masifa ta da rashin kunya na daina yi Masa ita sai dai kyautatawa tsakaninmu na Masa wanki abinci me Rai da lafiya,dake nice a kitchen din nama ma yafi me gidan ci da yawa duk shi nake kwashewa na bashi.

ko Jollof nayi to Abbanku shi inda yafi Mai da dadi nan nake Fara kwashe masa,albashina ma idan na kaiwa Innata abinda ta dauka ta bani sai nazo na bawa Muazu kudin,ganin haka sai yace Yana so na sabo da yanda nake kyautata masa,Me gidan da nake yiwa aiki shine ya dauki nauyin bikinmu kaf danginsa da Uwa ma sai kaunata saukeyi sosai aka sa bikinmu da Muazu Wanda me gidan shine ya dauki nauyin komai,Kafin biki Kuma aka samu matsala dansa shine yayi yunkurin lalata min tarbiyyar sanadin dukan da Muazu ya Masa shine masu gidan Suka kore mu daga aiki gaba daya,Bikin ma yace ya fasa daukan nauyi,haka Dangin Abbanku da Nawa Suka dage aka samu aka yi Mana aure Muka zauna a gidan Haya Wanda mahaifiyarsa Uwa ta Kama Masa,bikina da shekara daya dai dai na haifo yata Bilkisu anan Kuwa kowa Yana so ana murna, ban Dade da haifar Bilkisu ba Mahaifiyata ta rasu itace kadai gatana Kuma ta Kare sai Yan Uwa haka a can Tara ba.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button