Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 40

Sponsored links

Anjima kadan ya kawo kifi da nama yace ayi musu girki,tare Muka Fara aikin girkin,Auta harda yanka mana Salat ana ta hira da shi,yaran Aunty Bilki sai kallona suke suna dariya sun zaci Cele ce sabo da tana kawo musu awara tana zuwa ma ta dauke su,Babban ma harda zuwa ya zauna a cinyata Yana dariya,Nace ka sanni ne?ya zaci fa Cele ce cewar Aunty Bilki,Rahma nayiwa magana nace ke tashi ki musu wanka ku gyara gidan nan tunda Naga yanzu ma suka karya,Gidan Aunty Bilki me Dan kyau ne karami dukka dakunan uku tiles ne da kitchen da toilet tsakar gidane Kawai siminti.

Rahma tayi musu wanka Auta ya shafa musu Mai sai kace mace,karamin ma yace kawo pampers a like Masa Duwawu Kar ya ishe mu da fitsari Bilkisu tayi dariya tace sai kace Gum ta dakko sabuwa ta bashi ya sa masa da kayan ma shike nan Yara Suka likewa Auta sunga Namiji dan uwansu gani suke Kamar babansu ne.

Nazifa ce ta Kira Bilkisu a waya tace wato shine aka min danwaken zagaye Ina nan Ina jiransu shine Suka sauka a gidanku kice da Rabia wlh tun wuri su taho nan,Aunty Bilki tace to mayya zasu zo ne jaraba uwar naci ta kashe wayarta,Minti kadan sai ga Nazira ma ta shigo gidan dake ita gidanta Basu da Nisa da Bilki tace salamu Alaykum Wai Ina bakuwar ne sabo da Allah ance za a zo tun safe nake jira,dariya Suka bani wannan naci haka ashe dai suna so na na furta a raina Ina Jin dadi,Nazira sai kace irin munyi shekaru tare sai ta dage labile ta leko palon ta kalleni Muka hada Ido tace shegiyar kaya kice nan Kika baje katon tumbi Ina can Kun barni a lalace shi yasa na kwaso Yan matan kafafuna nace bari nazo na gani ashe kunzo, har mijina na tura gidan Umma yace ance Kun taho ashe nan kuka yo,Ina dariya nace ai ta nan Muka fara,to Dan ubanki baza ki gaishe ni ba nafa girmeku ke da Cele, nace Ina kwana tace lafiya lau nan mu muna da tarbiyya ba a kudu kike ba ki nutsu gashi nan hausarki duk ta lalace kina wani badan badan,dariya nayi ni bana ji ma hausata ta Fara canjawa, tace Ina su Star shegun kaya kunyi waya? Nace ai da safe dukkansu sun kirani Allah sarki kice Muna gaisuwa,juyawa tayi tace sai Kun shugo to nace to Aunty ta fice.

Sai da Muka ci Muka koshi sannan Muka je gidan Iyayen mijin Bilkisu Muka gaishe su ta nuna ni a wajensu suna ta Mata murna,muka tafi gidan Nazifa itama,Muna yin Sallama Muka sameta tana ta turaren wuta mijinta Yana Shan tea, Yana Mana Sannu da zuwa Muka shiga,Nazifa tace Auta kaga da Yar nan tawa ta girma baka ita zanyi ka aureta kalleta kyakyawa da ita,Auta ya ganta tana Wasa Fara kwal da ita taci ado gashinta yasha style na kitso,Auta yace ai yanzu Kam sai dai ki min Addua Allah ya sa na haifi kamarta da tayi tsada sai Wanda ya Isa shi zai auri ‘yata yasa hannu ya dauketa Yana cewa wlh Kamar na gudu da ita,Mijin Nazifa ana yabon yarsa har wani dadi yake ji, Bayan mun gaisa Mijinta ya fita Nazifa tace miracle ko ai nan gaba har gidan Dagaci zamuyi gayya har Umma muje amma sai mun lallaba Abba idan ya yarda sai mu sa lokaci mu je Dagaci yasan kema kina da gata kowa a cire Masa shakku cewar ke ba Yar shege ba ce,Ina dan mijin naki kyakyawa me kama da Auta,Nace Yana can tun jiya ma bamuyi waya ba Naga kiransa da safe lokacin Ina bacci,Kuma Baki kirashi back ba? Nace ae ai zai sake Kira ne, Nazifa tace baki da hankali dalla kirashi ai Wanda ya damu da Kai to ka damu da shi,dariya ta bamu Kamar itace ta hada mu harda masifa,Kiran Nawwar nayi ya daga yace an samu Yan Uwa an Mata da miji nace ni na Isa,zamu hadu ne ai taraki nake yi, ya furta,Nazifa tace bani shi mu gaisa ta kwace Wayar tare da furta Hello Kanina Auntynka ce Nazifa Nawwar yayi dariya yace ahhh Allah ya tsare Mana Aunty Ina kwana,ta amsa Suka gaisa tace a dinga hakuri da kanwar nan tamu bata ji,Nawwar yace Inshaallah Aunty ai bata ji tace zamu saitata ne Naga Kamar taci Kai, Nawwar dariya shi dai yake yi yace na gode Aunty Allah ya Kara girma,ta Mika min wayar Muka danyi hira ya kashe .

Sai yamma Muka wuce gidan Nazira, Muna zuwa harda rungumeni itama gidanta yaji gyara Dan karami me kyau,Mijinta yafi na kowa surutu da shi Muka Sha hira sai dare Muka fito tace gobe sai Dangin Umma da Abba haka zamuje a nuna ki nace Allah ya kaimu.

Washe gari Kuwa sune Suka rakani Dangin Abba Dake garin muka gaisa duk da su basu damu ba basa son Mata amma dai munje sun ganni,a kwana na Uku kuma Muka je wajen abokan arziki na Umma duk Yan uwanta suna Taraba state su sai nan gaba zamu sa lokaci muje dukkanmu da gidan Dagaci sai Kuma Dangin Abba dake Nasawara duk zamuje da su Nawwar sabo da danginsa shima suga asalina na huta da Jin kunya,Yau Auta cewa yayi Rahma,Raheema,Omaira su shirya zai Kai su yawon shakatawa,Afif da Yamma yazo da mota Suka cakare Suka tafi,ai Kuwa ba su ba mu na gida ma mun samu tsarabar kayan dadi.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button