Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 7

Sponsored links

Duk yadda Jeederh ta kai da son kamewa waje guda da riƙe kanta amma ka sawa tayi ta miƙe tsaye hannunta riƙe da Khalil, amma ta kasa motsawa sbd bata ƙara jin saukar sautin da kunnuwanta suka jiye mata ba. Shiru shiru sai kawai ta juya zata koma saman bed ta ƙara jin ance “Jee, Jee Malumana” a wannan karan muryar da aka kira sunan bata fita sosai kamar bai kiran yana cikin wani hali, ƙirjinta ya yi kyakkyawar bugawa, bugawar da sai data runtse Idanunta, me ya sa muryar ke yi mata tsananin kama data Little Son? Me ya sa hatta sunan ya zo ɗaya da wanda ya laƙaba mata sbd bashi da hausar da zai iya kiran complete sunanta Majeederh kamar yadda kowa ke faɗa, iya ƙoƙarinsa da faɗar sunan sai dai ya furta kalmar _Jee_ a sauƙaƙe?

Yaa Allah” ta furta domin tasan har abada har gaban abada idan akwai he never comes to her, amma meke damunta har haka me ya sa muryar ke mata amsa kuwwa a kunne? “Jeeeee!!!” Ya sake furtawa muryarsa bata fita sosai kamar wacce aka tsikara tayi wajan ƙofa tare da sanya hannu ta murɗa handle, tsaye ta gashi yana zabga ƙamshi daga shi sai wata kyakkyawar Arabian jallabiya brown kallo wacce tayi masa kyau sosai, ya ɗan sakar mata kyakkyawan murmushi kafin ya ce

“Kina buƙatar wani abu ne?” Tayi masa kallo ta ɗauke kai ba tare data amsa shi ba, domin bata da yawon magana Majeederh nada matsanancin aji sosai, wanda kuma halittar ta ce hakan. Gani ya yi tana leƙa waje shi ma ya leƙa yana cewa “What are looking for? Me ki ke kallo?” A raunane wanda kuma ba kowa take son yaga raunin nata ba ta riƙe kanta sosai tana sake rufe jikinta da hijabi ta ce “Allow me to go”

“Where?” Ya amsata da sauri. “Ban son zaman nan, kuma ka bari na leƙa waje” Abu-turab ya ware idanu yana shafa sumar kansa ya ce.

“Me Jiddo zata yi a waje yanzu? 2 saura ok” tayi shiru ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin tayi saurin ƙanƙame jikinta waje guda lokacin Khalil ya fara kuka..

Sosai Abu-turab ya rufe ƙofar kana ya nemi waje nesa da ita ya zauna saman kujera ya harɗe ƙafa. Malama Majeederh hankalinta ya rabo wajan kashi uku, ɗaya na waje, ɗaya na kan Khalil dake kuka, ɗaya na kan Abu-turab daya sanyata a gaba tare da kafeta da idanu. Sai ta zama ira bata ƙaunar kallo yana takura ta ainun.

Abu-turab yana ƙoƙarin magana su ka ji an daki ƙofar ya miƙe tsaye tare da kallon Jeederh ya ce

“Sorry, na ce a kawo mini abin shur ina da azumi” bata ce komai ba ita dai.

Ya nufi ƙofa yana fita ya rufe ta, kokawa ake sosai da Abraham Daniel David wanda yake son ta ƙarfi sai ya ɓalle ƙofar, gadai securities da yawa amma sun kasa controlling nasa ya jiwa kansa ciwo amma yaƙi ya yi giving up, wani irin ƙarfi ke zuwar masa. “Abraham” Abu-turab ya kira shi,ya juya kalli Abu-turab.

“Me ka ke buƙata?” Da hannu ya nuna masa bedroom ɗin da Malama Majeederh ke ciki, kana ya nuna ƙirjinsa wajan zuciyarsa ya ce.

“Jeena, nan” Abu-turab ya fahimci Abraham na son shaida masa Jee na cikin zuciyarsa ita kuma yake nema. Cikin nutsuwa yana murmushi ya ce

“My friend zo ka ji” Abraham ya kafe waje guda domin babu na biyunsa a taurin kai. Cikin tattausa harshe ya ce “Ita Jee ɗin bata nan, amma ka dawo gobe zan kaita wajanta” ya faɗi hakan cikin harshen Ingilishi yadda Abraham zai fahimci mai yake nufi.

Promise?” His Excellency ya ce “Promise” Abraham ya sanya hannu a tsakiyar rigarsa inda ya yage ya zaro wata kyakkyawar flowers sai ƙamshi take ya miƙawa Abraham yana wani irin buɗe ido ya ce “Malumana”

Ma’ana the flowers is for her. His Excellency ya amsa deep down na zuciyarsa cike da mamakina Abraham who is he to her?

.Securities ɗin za su kama shi ya girgiza musu kai tare da yin gaba yana ɗan tangaɗi yana yin gaba ya ji saukar muryar Khalil na kuka ya tsaya cak, sai ya juya kawai sai su kaga ya yi murmushi ya ce

“My pregnancy”

“An samu matsala” In ji Khamal. Abu-turab ya saka hannu ya tsige flower ɗin tare da zubar da ita ya ce

“Make sure baku sake sakaci ba, i hate noises”

 

“We’re sorry Sir, Hakan ba zai sake faruwa ba, wallahi ta sama ya hauro mahaukaci ne daya kama hannun Captain sai da ya ƙarya shi,ya sha duka sosai wajanmu amma bashi da haƙuri yana da zuciya ban san wani abu giving up ba” His Excellency bai ƙara magana ba ya buɗe bedroom ɗin har yanzu tana zaune saɓanin ɗazo Madara take bawa Khalil, Abu-turab ya jima yana satar kallonta da tayi ƙoƙarin ɗago kai sai ya janye idanunsa ya basar

“Jiddo, we need to talk please” yadda ta ƙara nutsuwa ya san cewa ta bashi dama cikin nutsuwarsa ya ce

“Majeederh kina da hankali, ko ban girmeki ba zamu iya zuwa age mate don haka duk abinda zan faɗa miki ba zai zama cutarwa a gareki ba” ya sauke numfashi ya ɗora da “Don Allah kada ki ji zafinki akan hukuncin da ya yanke miki, iyaye ba a taɓa fushi da su ki ɗauki hakan matsayin jarrabawa kuma ƙaddara wacce babu yadda zaki iya dole sai ta kasance, ba zan miki nasiha akan yarda da ita ƙaddarar ba domin kusan kin fini sani, sai dai na nemi ta barraki a wajanki” ya ƙara yin shiru ya ce “I feel your pain, kafin na zama gwana na sha wahala,ina rayuwa da mahaifiyata after my father’s died, dangin mahaifina they are so selfish sun ƙwace komai dana mallaka wajan Abbana, filaye, kadarori all the properties, mun fara yawo yawo a dangi kowa yana gudunmu sbd babu ran mahaifina sun manta alherin da ya yi musu, dangin Mamana basa kusa, na fara dako ina garuwa ban taɓa yarda ba zan iya ba, burina Mamana ta ji daɗi na zama wani abu”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button