Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 31-32

Sponsored links

Ina kusa da Auta Nawwar ya dawo ya kori Auta sit din baya shi ya zauna a kusa dani,Auta yace ni na huta ma matar taka da duk yawu gareta,nace Auta Inshaallah sai ka auri mace tana samun ciki kullum yawu da amai suna hanya yace ba Amin ba.

 

Muna sauka Auta dama ya Kira abokinsa Afif shi ya dakko mota Nawwar yace wlh bazan shiga tukun wannan yaron ba yaje yayi hatsari da mu,nace dan Allah kayi hakuri muje ba abinda zai faru Auta Kuwa har ya Shiga gaban mota ya kame,da kyar Nawwar ya yarda Muka shiga baya,Auta Wayar Omaira ya kira ta daga,yace ke gamu nan mun shigo gari Ina ne gidan naku Omaira ta musu kwatance,Umma da sauran Yan Uwa kaf an taru ana jira a gani wacece ake tunanin jaririyar da ta bata oho,Abba Yana zaune a kusa da Uwa Babarsa suna cewa wallahi baza su kawo tsintacciya a hada jininmu da ita ba ace wata Yar uwa ce bazai yuwu ba,Abba yace yanzu haka ma irin Kama ce da Allah yake halittar bayinsa da ita zamu gani ai,su Bilkisu da Umma duk suna Palo a zaune suna jira,Omaira kafin mu karaso ta fito kofar gidansu wani ginin bulon siminti tsoho tukuf da shi dama unguwar tasu gata ga irinta,Nawwar Yana ganin Omaira yace gaskiya jininku ce wannan ba sai an tambaya ba ma,Omaira ta rike kugu a kofar gida tana tsaye sanye cikin riga da wando ta dora hijab maroon ya wuce gwiwarta, suna parking Nawwar ya fito ta bishi da kallo tace tace amma daga madagaska kake ko bawan Allah, Nawwar Bai shirya dariya ba sai da yayi yace a’a daga Masadonia nake,Miracle ya zaga ya budewa kofa,Omaira tace hamshakiya mandiya kofar ma Sai an bude Mata,Kafar Miracle Omaira tabi da kallo Tasha takalmi me tsada da tsini ta fito sanye ciki wani danyen leshi me tsada Golden and White jaka da takalmi da mayafin Golden tayi kyau na mamaki sai kamshi suke na musamman,Auta ya fito tuni ya harde hannaye a kirji Yana jingine jikin mota anyi tsaiwar samari,Jakar Miracle Nawwar ya daukar mata Wai baza ma ta rike jaka ba,Omaira tace sannu Alhaji Bawa sunan wani wai Bawa to ai da Kai aka sawa sunan ma,Auta Murmushi yayi,Miracle tace ke dan Allah kin ishe mu ki Kai mu gida sai shegiyar magana.

Omaira gaba tayi tace ku biyoni a bayana suna tafiya tana juyowa tana kallonsu tana sake juyowa ni Miracle na Mata ambola nace kanwar uwarki,Omaira ta juya tana dariya Suka shiga gidan ta kwala Sallama Salamu Alaykum Umma ga yarki marar mutunci ta zo,Nace Mijin uwarki ke Omaira kike ko wa nace Mijin uwarki,tace ai an saki Umma bata da miji Nace to tsohon mijin uwarki,Abba yana zaune ya saki baki yace Kai na yarda wannan ‘yata ce babu tantama,Uwa Mahaifiyar Abba tace gayyar tsiya naji mace daga zuwa sai zagi kana zaune tana zaginka,yace ai bata San nine ubanta ba shi yasa duk yarana basa ci min mutunci suna daraja ni banda Cele kam Yar banza me Kai Kamar murhu,Kallon Abba nayi nace Sannunku ya amsa sama Sama,Uwa Kuwa ko kallona bata Yi ba Kawai Nawwar suke kallo suna washe Masa baki sunga me kudi,Uwa harda tashi ta jawo tabarma sabuwa ta shimfidawa Nawwar tana zauna,ta kalli Auta tace Dan Samari Zauna,Auta a ransa yace kin taimaki kanki da Kika ce samari baki ce yaro ba,Zama Suka Yi Abba Yana ta jera musu sannunku da zuwa sannunku,Uwa tana lale marhabin marhabin lale lale ta kwalawa Rahma Kira tace kawo musu ruwa mana,Ni Kuwa mamaki ya kamani ni sunki kulani Amma Nawwar da

Auta shi Kamar sune Yan uwansu,Abba yace Allah ya muku Albarka babarku tayi farar haihuwa gaku maza Kuma gaku Kuna Kama da alama dai wa da kani ne,Auta yace ae nine kanin shi wannan yayana amma da kadan ya girmeni Wai Nawwar ne ya girme shi da kadan shi da matan ma su Sultana sun girme shi aure kawai za a musu sun girma,domin su sun shiga University tuni ma,Auta ya kalli Rahma a ransa yace wannan kwaila ce kirjinta ba komai sai tsayin kafa,Raheema ce ta fito itama ta gaida su Suka amsa Auta itam ya Kare Mata kallo sai kace munafuki a ransa yace wannan Daya tayi Mata kwari ta tsunbure baza ta girma da wuri ba kafin ta murmure za a dade itama dai kirjin ba komai kamar faifai ita kanta nonon take bukata a shayar da ita Ina zata Iya shayar da kamata Ina,Nawwar Yana kallon abinda Auta yake Yi na kallon matan hararar Auta yayi,da sauriĀ  yayi kasa da Kai da sauri.

Ni Kuwa Ina Shiga Bilkisu Babba tace Masha Allah wannan twin din Cele ce gaskiya sun zuba min Ido suna kallon suturata da irin kyan da na tsula kudi basa buya idan akwai su,baki na zumburo nace sannunku,Suka amsa da yawwa,Umma na kalla cikin doguwar rigar atamfarta me kyau kamar Yar balarabiya,na durkusa a gabanta nace Ina kwana tana Murmushi ta amsa ta rike hannuna tace ga Yan uwanki ki gaida su, yayyenki ne na juya na gaishe su su Rahma Suka gaishe ni,Omaira ma ta gaishe ni,nace Ina wacce naga hotonta a kasko tana suya? dariya Suka Yi Suka ce Yar jarfa kenan Cele a kasko kenan sunanta Rufaida ana ce Mata Cele Amma fa Cele a kasko ita Yan biyunki ce tare aka haife ku itama ba anan gidan ta taso ba,nace mijina Yana tsakar gida,Aunty Bilki tace ai ya Zama dan gida ya shugo Kawai ayi labarin a gabansa,Nawwar na Kira nace ku shigo,Abba da Uwa Suka tabe baki yace maza da Shiga cikin Mata jeka kuje Kar ace Ina bakin ciki,Nawwar ya mike da Auta tuni kamshinsa ya cika ko Ina yayi sallama ya shigo palon Kato ne,Su Aunty ne Suka tashi suka bashi doguwar kujera shi da Auta Suka zauna.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button