Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 62

Sponsored links

Watsar da zancen tayi ta shirya cikin wata fitted bubu silk fibre, sai da ta gama feshe jikinta da turaruka masu kamshi sannan ta saka rigar, tsayawa tayi a gaban mirror tana tinanin meya kamata tayiwa fuskarta, ita ba gwanar kwalliya bace but she wants to look good for her honey, tuno yanda mami ta mata last time da zata gurin Abby yasata daukan kwalli tasa a hankali being cautious karya tsokane mata ido, eye liner ta dauko ta gwada lining saidai ganin yanda hannunta ke rawa kawai ta hakura dashi, mascara tasa ta taje long natural lashes dinta sai hakan ya kara fito dasu gwanin sha’awa, girarta ta taje da brush sannan ta saka lipgloss baki yayita maiko gwanin sha’awa, daidai nan khaleel ya kirata yace mata gashi a kofar gida yana jiranta, veil dinta ta yafa sannan ta sake feshe jikinta da turaruka, matching bag da shoes ta shafa ta kara gyara zaman veil dinta sannan ta fita, ko kafin ta bar corridor din sama veil din har ya dawo tsakiyar kanta saboda tsantsin gashinta da yalwarsa, ko a jikinta ta cigaba da tafiya batareda ta sallami su umm ba…..

 

Direct hospital dinsa ya wuce bayan ya budewa umm inda ya kulle billy, ya sani sarai bazasu kwashe ta dadi ba idan taga irin dukan da yayiwa yarinyar shiyasa kawai ya fece saboda ransa a bace yake bayasan a kara masa wani bacin ran…..

Tinda ya shiga asibitin ake ta gaishesa amma babu wanda ya kula kawai ya shige office dinsa ya shedawa secretary dinsa bayasan ganin kowa…..

Zama yayi a office chair dinsa zuciyarsa duk a jagule, sai kuma a lokacin yaji yana san sanin result din tests din, gashi babu wanda yace masa komai, kodai anyi nasara ne? Sai kuma yaja tsaki yace;

Haka yayita tinaninta, wani abun ya sashi murmushi, wani abun ya sashi watsar da abubuwan da yake kan table din, a haka duk saida ya hargitsa office din be sani ba….

 

Sai da yaji ana kiran sallar magriba sannan ya tashi ya tafi masjid din hospital din dan yayi sallah , koda cleaner din dataje gyara office din taga yanda office din yayi kacha kacha tayi mamaki sosai, sai kace wanda yayi dambe da kayan office din, haka dai taja bakinta tayi shiru tayi abinda ya kaita….

Ko bayan an idar da sallah be tashi daga masallacin ba sai ma Al-qur’ani daya dauko ya fara karantawa, a hankali ko yaji zuciyarsa ta fara masa sanyi, bacin ran daya kwasa yau na gushewa, karatun ya cigaba dayi har akayi sallar isha, saida ya sake kara 30mins yana karatu baya an idar da sallar isha sannan ya tashi ya wuce gida…….

 

Har ze shige part dinsa yaji baze iya bacci idan besan halin da take ciki ba, yasan kuma ba lallai taci abinci ba, gwara yaje ya tasata a gaba taci, ya kuma bigi ruwan cikinta yaji labarin tests din dan abin ya kasa barin ransa……

 

Yana shiga parlourn yaji ko ina tsit sai karar ac, har zai haura sama yaji wani fitinennan kamshin turare ya daki hancinsa, ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido at the same time yana kara bude hancinsa dan ya shaki kamshin turaren da kyau, sai kuma yaji takun takalmi dass dass alamun ana tawowa, guri ya samu daga chan gefe ya zauna yana jiran yaga waye haka dan yanada tabbacin me shine ya cika turare haka…….

 

Kamar a mafarki ya hangota tana saukowa daga kan step sadap sadap jikinta sai motsawa yake a cikin silk rigarta, murza ido yayi dan ya tabbatar ita din yake gani ko kuwa, mamaki ne ya kamasa ganin da gaske ita dince, sake baki yayi yana kallonta kamar ya hadiyeta daga zaune, sosai ta mishi kyau kamar ya saceta ya boyeta yana ganinta ita kadai, ya rasa meyasa kome tasa yake mata kyau, ga bakinnan sai maiko yake yana daga masa hankali, kasa jurewa yayi ya zaro wayarsa ya hau yi mata hotuna da videos, ita ko batasan yanayi ba dan bata ma ganshi ba, burinta kawai ta fice batareda kowa ya sani ba, deen kuma yanaso ya dakatar da ita amma inaa hankalinsa ya riga ya gushe a wajan kallonta, saida ta kai daidai bakin kofa yaji kamar an tsikaresa, da sauri ya ajye wayar ya daka mata wani mugun tsawa yace;

“Kehhhhh!!!!”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button