Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 56

Sponsored links

Umm zatayi magana kenan ta juyo muryar da ko a mafarki bata san karajinta a rayuwarta, muryar da bata san tina wani abu ya taba hadata da meshi, sai ta dauka kawai irin hallucination din data saba ne……

“Boddi na! Boddi na! Boddiiiiiiii”……

Abby ya sake fada da karfi yana shigowa parlourn….

Fatima zainab na ganin Abby yayi gaba ta ruga a guje ta shige ciki, kan Umm dake tsaye a daskare tayi ta rungumeta tana boyewa a jikinta, ita tayi hakan ne saboda kar Deen ya mata wani abu tinda tasan be isa ya tabata a gaban mamansa ba……

Zubewa a kasa daddy da alhaji habibu sukayi ganin wacce suke nema ido rufe gata tazo har inda suke…..

Ido hudu Abby sukayi da Umm da already ta fita daga duniyar mutane, firgit kamar wadda aka tasa daga bacci ta shiga murza ido dan ta tabbatar da shi din take gani…….

“Ni ne boddi na! Ba mafarki kike ba”…..

Abby ya fada fuska dauke da madaukakin farin ciki, irin wanda be karayi ba tin bayan barinta rayuwarsa……..

Sai a lokacin Umm ta tabbatar dagaske shi dinne, sam bataji farin cikin ganinsa ba saima hada rai da tayi ta jefo masa tambayar;

“Ina ya’ta! Ina baby tee?!!!”….

Abby zeyi magana kenan sukaji mom ta kwallara ihu kamar wata mahaukaciya sabon kamu, cire mayafinta tayi cikin ihu tace;

Fatima(mami) da samira(mom) sun kasance kawaye ne tin suna yara kanana kasancewarsu makota, haka suka taso tare gwanin ban sha’awa babu wanda besan kawancensu ba, shakuwa tayi shakuwa har suka zarce aminai suka zama tamkar yan uwa, idan har zakaga mami tabbas mom ma tana nan, harta islamiyya da boko iri daya suke zuwa, kuma tare suke zuwa, haka gurin zama ma tare suke zama, kawancensu saida ta kai ta kawo har kaya iri daya suke sawa, har ta kai idan zaa siya musu abu a gida guda biyu ake siya, sai da suka fara zama yan mata shedan ya fara shiga zuciyar mom, abun ya samo asali ne daga yanda mami take da farin jini kasancewarta kyakkyawa kuma su dama haka yan gidansu suke kyawawa, itama mom tana da nata kyan daidai gwargwado saidai rashin godiyar Allah dake dawainiya da ita, babu abinda yake daga mata hankali irin yanda kullum in suka fita sai an biyosu kuma kowa yazo yace mami in kaga tayi saurayi toh ita kadai ta fita, sosai hankalinta yake tashi akan hakan harta kai ta kawo tana bata mami a boye a gurin masu sonta, ba karamin yaki tayi ba gurin boye bakin cikinta a fili har suka shiga university ko so daya bata taba bari wani ya gane ba… Sannan mom bata kara rena kanta ba saida suka shiga university, gashi dama sun nemi admission na law mami ta samu ita bata samu ba, ga masoya da suke kara yiwa mami yawa, sai hassadar da takeyi yaci uban na da….. Saidai ko a haka suna makale a tare in sun gama lectures, kuma ko daya bata da lectures zata rako yar uwarta…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button