Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 100

Sponsored links

Sai da Soyayyar Star da Malam tayi karfi yace zai turo manya sannan itama Star muka shirya Dan bala’i ana gobe zamu tafi sai ganin Wise Muka Yi tazo Wai da ita za a Kai kowa,Washe gari Sai Yobe state,nan ma gidan su Star dama daga babarta sai Saima Yar uwarta Star tace ta samu Miji amma sai bikinta zata zo Saima an girma an Zama Yan Mata itama da Saurayinta a nan Yoben Nawwar yace sai a hada ayi bikin,Star wato Aisha ta hakura a nan gida aka barta tare da kanwarta da Mamanta.

Tunda Muka dawo Wise ta koma gida ita da Star,Rannan Sabeer abokin Nawwar Wanda da shi aka je bikina yazo wajen Nawwar yaga Seraline ya nace shi ita yake so,Reraline sai Murna take matashi haka hadadde me kudi da shi itam me zata ce da Allah sai godiya,zance ya Fara zuwa,Sera anci gayu anje tace ni gaskiya Allah ka canja suna sabo da Naga me irin sunanka marar mutunci sam halinta bai da kyau,Sabeer yace to fa Yana wani nishadi ana Masa shagwaba,yace wacece? Sera an goge da bariki harda gyara Masa kwalar riga tana cewa Sabreen mana wacce Nawwar ya Fara aure, Kai Sabeer ita Sabreen gaskiya ka canja please My Man tana wani narkewa,Sabeer gani yake duk duniya ba Wanda ya kaishi dace yace Eyya sorry su Daddy sun riga sun yanka min rago a haka, Sera ana wani dire diren kafafu ni Allah…Allah….uhum..uhm….farin ciki ya cika Sabeer ta gama tafiya da shi a rayuwa,Sabeer shi mamansa da Kannensa suna can asalin state dinsu Katsina,Amaryar babansu Hajiya Sumayya tana nan a wajenta Sabeer yake sun Shakur, Baban Sabeer a nan ya kawo Amaryarsa tunda anan yake kasuwanci idan Kuma yayi wata Daya ko biyu sai ya koma Katsina wajen Uwar gida,Hajiya Sumayya yaranta biyar Yan Mata dasu duk suna University,Hajiya Sumayya da Yaranta kaf basa son Sabeer ya auri Sera su basa son talaka,tunda Suka je kauyen su Sera Kai kudi Suka ga garin da gidan Suka Fara sukan auren amma Maman Sabeer da Babansa duk suna so sabo da haka ma aka sa ranar aure,duk kuwa da sunbi didigi sunji da a baya ance karuwa ce,shi aure haka yake da tone tone.

Yar Zabil da Mandula Suka ce to mu ko wa zamu samu oho Kinga munyi kwantai mu duk shegen degree faranti na cewar Mandula,ana haka Katsam tsohon saurayin Mandula wani Igbo kyakyawa ne sosai fari gashi da rufin asirinsa matashi da tana zuwa tayashi kwana,bashi da Iyaye baida kowa sai dangi shi kadai iyayensa Suka Haifa Yana kaunar Yar Zabil a duniya shikam bai bin ko wacce mace sai ita,shine yazo Wai Yana sonta suyi aure tace a’a bai halatta mace ta auri Wanda ba musulmi ba,kayi min komai naka yayi na yarda da Kai amma mu a addininmu bai yuwuwa mace ta auri Wanda ba musulmi ba,Saurayin Yar Zabil Michiel ya damu Nawwar Kamar me shi Yana sonta Nawwar yace a’a sai dai ya musulunta idan Yana so,ya tafi ya dade bai dawo ba an zaci ma ya fasa aurenta sai gashi ya dawo dauke da carbi a hannunsa cikin Jallabiya fara da Yar hularsa tashi ka fiye naci,Nawwar ya dinga dariya a ransa yace kaga sabon tuba,Ashe tafiya yayi ya musulunta ba tare da ya fadawa kowa ba,Nawwar yace karfa ka aureta muji ka koma addininka na baya wlh sai ka sakar Mana ita,yace ai nayi niyya dama ni musulunci ya dade Yana birgeni Kuma ko Bata aure Ni ba bazan fita daga musulunci ba na musulunta sabo da Allah, Nace wlh idan ka aureta Muka ji matsala wallahi sai ka gwammace kida da karatu sai mun kaika Sambisa forest yace Inshaallah Inshaallah,Nawwar yace ya sunanka yanzu? Yace Ahmad Kuma Ina zuwa wajen malami Yana min karatu yace okay idan kunyi aure sai kuci gaba da zuwa tare da ita itama ta Kara ilimi yace to.

Yar Zabil harda rawa Nima na shiga na shiga nayi kasuwa eh eh eh ya Kika ce ta sanadiyata an musulunta nazo duniya a sa’a ni San Sanda za a haifeni kukana ma haka nake cewa Allah Allah Allah,Mandula tayi dariya,ana haka Nawwar yace Wai zai hada Mandula da Santana aure tace kwarankwatsa dubu bana sonsa,yace Santana yace yarinya kinwa kanki santalelen yaro son kowa kin Wanda ya rasa, ni dama me zanyi dake, Mandula tace baki kamar kana hura algaita bada ni ba,ka gama tambadewa dan Iska ta duma Masa dundu a baya,Nawwar Muna ta dariya Santana yace ni Ina da budurwata ma su nanta Karima tana can a garinmu Adamawa ance bata Yi aure ba har yanzu tuni ma na samo number dinta mun daidaita kije can Mandula Karuwar banza

Mandula tace Yaya Nawwar ni dama da Baffa ka hadani,yace Allah ya kiyaye min wlh baki Isa ba ki Zama uwata bada ni ba,Muna ta dariya su Mandula dai ba a samu Miji ba har Baffa yaje ya kai kudin auren Wise wajen iyayenta na Papa,aka sa biki cikin sati biyu sabo da Papa ya matsu Kuma a shirye yake,Wise cokali basu siya ba,Test din aure anyi lafiya Wise take Papa ma Haka.

 

Munyi Shirin biki Papa harda hada dinner bayan an kawo Amarya,Mama da Sabreen sun hada kansu sai wulakanci sukewa Papa basu San ma an kusa biki,sai ana gobe daurin aure sannan ya sanarwa Mama gobe daurin aure na,Mama tace wallahi sai na tona maka asiri Matukar ka Kara aure,yace ai Kuwa sai dai ki tona in Kinga dama ki Zama kaza sabo da tone tone,Wise anci gyaran jiki ciki da waje ko Ina an matse gam,ana gobe Muka tafi can Jigawa washe gari su Nawwar Papa da Baffa da sauran dangi sunzo 11:am aka daura auren Yusuf da Amaryarsa Hauwa’u,shi dai Papa tun daga kallon gidan su Wise yasan kudin da suka dinga nuna masa babu shi,Kawai suna da rufin asiri,mukus yayi yace ko ba kudin dai na more da sabuwar Amarya matashiya,gaba Daya da Yamma da Dangin Wise Muka taho ranar Yamma likis aka wuce Dinner, Papa an dauki wanka Kamar matashin saurayi haka ya hade ga amaryarsa,Wise ta dinga fitsara tana Masa kiss,Papa Kawai yabi yarima shima aka Sha kida,ya lika kudi na hauka agaban su Nawwar,Auta Nawaf Kuwa tunda ya tabbar budurwarsa Papa ya aure shike Nan yace ba shi ba Papa ya daina kulashi ko ya ganshi baya gaishe shi,Papa ya rasa dalili,daga wajen Dinner aka wuce da Amarya gidan angonta,bangaren Iyamami Muka fara kaita tayi nasiha sannan aka kaita bangarenta.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button