Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 13

Sponsored links

Zaune yake a office dinsa yana daddanna system cike da kwarewa,kallon wani hotonta dake bangon office dinsa yayi ya kama murmushi kamar wani wawa,hotone da yayi mata da hijab har kasa da kuma niqab harda hangloves kamar dai yadda ta saba shigarta,baya ganin komai na jikinta,dukda hakan ba karamin farinciki hoton yakesa masa ba,musamman inya tina irin masifar data masa akan hoton,wai dan me ze mata hoto?…………

 

Wayarshi ce tafara ringing da wani kida me dadin sauraro,a mamakance yabi wayar da kallo,dan yasan ita kadai yasawa wannan ringtone din,da mamaki da farinciki ya daga wayar yana bin wayar da kallo,baze iya tina when last ta kirashi ba?,kuma shima kafin ya sameta a waya sai yayi dagaske,har ze katse ya kirata back sai kuma ya fasa dan yasan tsap zata iya kin dauka,tace akan me ze katse ya kirata tinda ita taga daman kira,dauka yayi da sauri kar call din ya katse………..

 

Daddadar muryartace ta daki dodon kunnensa tana cewa “Sai yanzu zaka daga wayata Khaleel?”…. Cikin murya me sanyi yace“Sorry wifey,nashiga kogin tinaninki ne har bansan wayar nata ringing ba,gashi farinciki ya lullubeni ganin sarauniyar zuciyata ta kirani yau”….. Wani abu ne ya daki zuciyar momma jin hakuri yake bata akan be dau waya da wuri…… Fatima zainab ce ta katse mata tinaninta da cewa”Ina gida,ina tsakona?” Murmushi yayi me sauti sannan yace “Haba sweetheart bazaki tsaya mugaisa bama?,sakonki kuma na gurin abdul,yace yanata kiran wayarki baya samunki”………. “Ok,ni badan gaisuwa na kira ba,bye”….. “I love you so much”… Ya fada batareda ya damu da abinda ta fada ba….. Tsaki taja ta kashe wayar……… Abdul jiki na rawa ya maza ya tashi ya tafi dauko sakon kafin ta juyo kansa….. Shigowa yayi dauke da wani katon box ya ajye a center table,ya russuna yace”Ga sakon anty”….. Kallon box din tayi tace”Bude”….. Budewa yayi wasu rose flowers masu shegen kyau suka zubo,saiga wasu cards anjera su daga gefe,sai wasu box guda biyu a ciki,da babba da karami,nuni ta mishi daya bude su suma…. Budewa ko abdul yayi saiga chocolates iri iri a cikin babban box din,dayan karamin box din ko waya ce kirar iPhone 14 pro max a ciki,tashi tayi ta zare wayar tasa a jaka,sannan ta dibi sauran kayan ta watsa musu a parlourn,ta dauki jakarta tayi hanyar waje…….. Abdul naganin ta fita ya bita da sauri,momma na kiranshi ko sauraranta beyiba…… Ajiyar zuciya momma tayi cikin kunan rai tace nida haihuwa,wata da juya min yara,khaleel dama yazama sallamamme akanta,shiko wannan da zarar ya ganta kamar an sashi a aljanna………..

 

Tafe suke abdul na binta a baya yarasa ta ina ze fara fadamata abinda yakesan gayamata….. Saida suka shiga parlournta yana biye da ita sannan ta juyo tace “Lafiya abdul?”…… Numfasawa yayi sannan yace “anty dan Allah wani favor nakeso kimin,na dade ina nemanki na rasa yanda zan sameki gashi inna kira wayarki bana samunki,dana fadawa yaya kuma saiya fara zagina wai uban me zan miki da nake nemanki”………. “Ina jinka”… Ta fadi haka Tana kallonshi….. Sunkuyar dakai yayi yace “Dama motatace taketa bani matsala,inata gyarata,kullum ni kenan hanyar garage,shekaranjiya ma na sake kaita amma haryanzu bata gyaruba,nayiwa Ya khaleel magana akan ya taimaka ya siyamin wata ko ya bani daya daga cikin nasa,amma yaki,wai wallahi baze bawa unserious being irina ba saboda na sakeyin spill two a school,dana fadawa daddy sai ya goyi bayansa wai ai gsky ya fada,bawanda ze tsaya yana kashewa irina kudinsa a banza,dan Allah sis ki taimakamin nasan ke kadai ce zaki yiwa yaya magana yaji”…….. Ba yabo ba fallasa tace “Kawai saboda ka sake spill two sai a hanaka jin dadin rayuwarka?,ai ba akanka aka fara unseriousness ba da zaa takura maka haka”……. Wani dadi ne ya lullbeshi,shiyasa yaketaso tazo,saboda yasan indai tazo duka matsalolinshi sun warware….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button