Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 99

Sponsored links

“Kayi kadan in fadamaka damuwata, just mind your business!!”…….

Zeyi magana kenan sukaji sallama a bakin kofar, Deen ne ya amsa ciki ciki ko sunji ko basuji ba shidai yaga sun shigo…..

Akanta eesha da billy suka fara sauke ido, zaro ido sukayi a tare suna karasowa inda take, itako fatima zainab yi tayi kamar bataji alamun mutane sun shigo ba……

Da sauri billy ta rungumeta tana fadin;

“Wow kece or am dreaming? Eesha dama kinsanta shiyasa kikemin wulakanci ko? Wayyo Allah naji dadi dana biyoki eesha, ashe alkhairi ke kirana inzo inga pretty girl dinnan”…. Sai kuma tashiga taba gashinta tana fadin;

 

“Wayyooo Allah kinada gashi sosai gashi da laushi wallahi, kai I’m already obsessed with you! Ina sonki wallahi, nima…”….

Wani tsawa Deen ya daka mata tsabar yanda ransa ya baci, ya taso kamar ze mareta yace;

“Saketa!!!!”…….

Sosai tsawar ya shiga billy saboda daga sama tajita dan batasan da wani a parlourn ba, ta saketa da sauri jiki na rawa……

“Out!!!!”….

Ya fada yana nuna musu kofa…..

Tinda suka karaso eesha tayi sumar tsaye saboda tozali da Deen da tayi, ashe pictures basa masa Justice? Dama haka ya hadu sosai? Wannan ai saidai tadinga boye kayanta dan wallahi ko irinsu billy ba zata bari su gane matashi ba, ta dade bataga captivating namiji irinsa ba dan ko ita da takejin tanada kyau sannan kuma gata mace tasan sai a daukeshi sau hamsin baa dauketa ba, ashe akwai maza masu kyau irin haka? A take taji zata iya mutuwa akansa, ga wani kishinsa da yazo mata lokaci daya ta kumaji babu abinda bazata iyayi ba akansa, ta kuma tabbatarwa zuciyarta Deen nata ne ita kadai…….

“Ke mahaukaciyar inace ina magana zaki tsaya kina kallo na, oya bita ku bace daga gurinnan! Kananun yan iska kawai!!!”…….

“Saifff menene haka? Wani irin rashin hankali ne wannan, daga ganin mutane sai ka fara zaginsu?”…..

Umm ta katseshi tana shigowa parlourn mami biye da ita a baya…..

Bece komai ba ya juya ya haura sama rai a bace….

“Karku kulashi dawo ku zauna kunji?”….

Zama sukayi a daddare dan harga Allah tsawar daya musu ta tsoratasu kadama billy taji labari….

Cewar Mami tana typing message akan a kawowa su eesha refreshments…..

Komawa ciki yayi da sauri yashiga nemanta baji ba gani, cikin toilet ne store ne babu inda be duba ba, haka kawai yaji hankalinsa be kwanta ba tinda ya hau samannan shiyasa ya dawo ya dubata sai prediction dinsa ya zama daidai ya rasata…..

Dawowa parlourn yayi cikin tashin hankali yace

“Mami banganta ba fah!”…

Hankali tashe suka mike suma suka shiga nemanta a ko ina na gidan, su kansu su eesha sunyi mamakin batanta dan basuga sanda tabar parlorn ba…..

Babu inda basu duba a cikin gidan ba, har securities da mai gadi sun tabbatar da bata fita ba amma sama da kasa sun nemeta sun rasa……

 

Deen da yazama so frustrated yanaji kamar ya shake su eesha da suka zake ana nemanta dasu yace;

“Ni nasan so take ta fita shiyasa na tsareta, wayennan idiots din sukazo suka sani tashi gashi yanzu she’s no where to be found! Allah idan banganta in the next 30mins I’ll hold you guys responsible!, waya sani ko turoku akayi! Musamman ke! you’ll tell me why you hug her!!!”…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button