Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 45

Sponsored links

Haba Danbinni a matsayinka da kudinka ka kalleni Kamar ni zaka biya Sadakina dubu talatin da biyar ko waliyyai na ne Suka yanke haka a matsayina ai ka kara yanzu dan wulakanci ma ka cike biyar din Mana su cike dubu arba’in amma Wai wani talatin da biyar mece dorin biyar din,da ilimina da komai ko yara Muka haifa kasan fa ABCD da sauransu duk Zan koya musu su Alif,ba’un,ta’un duk a dubu talatin da biyar nufinka Zan zauna na koya musu to wallahi ka shirya iya kudin daka bayar iya abinda zaka gani a gidanka,Danbinni yayi Murmushi yace ke me Kika dauki aure ne?Ashe ilimin da kike ikirari Baki da shi to an fada Miki siyen mutum ake a aure shi,Ibada ce fa Zaki yi, ke yanzu Indai har kina da tunanin akwai Dan Adam da zai iya biyan kudinki to lallai baki San me kike ba,ai ko silin gashinki Dan Adam Bai iya siyansa a duniya bare sauran jikinki da komai ma,domin silin gashinki daya idan ya cire duk duniya babu me iya fito Miki da shi sai Allah to akwai Wanda zai iya biyan wannan kudin ke kina tunani? Tsaki ya ja tare da kashe wayarsa,Gaji tace ka gama dani Kawai tun daga nan Gaji ta daina shagali.

Sai Yamma ana Shirin Kai Amarya Dagaci ya shigo gidan ransa a bace ya Kira Gaji ta fito daga cikin kawayenta ya irga dubu talatin da biyar cas yace Gaji gashi kudin sadakinki sai ayi hakuri,Gaji tace Wai Baba da gaske talatin da biyar idon Gaji ya ciko da kwalla,Dagaji yace Hmmm Gaji yaron nan yau ya gama kunyata mu a idon duniya ki godewa Allah ma da aka daura auren Saura kadan a fasa

 

Gwaggo ta dafe kirji sunja gefe suna ta kuskus Yan biki suna kallonsu kowa yasan ba abu me dadi suke tattaunawa ba

Dagaci yace Danbinni da Suka zo da danginsa Muka yanke sadaki dubu dari mu a tunaninmu mun Masa sauki da karamci sai kuwa danginsa Suka Yi tsalle Suka dire Suka ce ai su dansu baida halin haka mamaki ya kamamu Suka ce a musu ragi,Gaji Zo ki ganmu inda kisan an jika biri a ruwa haka na koma na zaci karya ne, ke yo ba sai aka Fara ciniki ba wallahi Gwaggon Mairo inda kisan na kai Akuya kasuwa haka a bainar mutane Muka dinga cinikin yarki Gaji,Muka sakko dubu tamanin Suka ce Albarka,Muka dawo dubu sittin Suka ce Albarka,dubu hamsim, arba’in duk Albarka a talatin dinma sai da Liman yasa baki yace wallah idan basu Kara ba bazai daura aure ba Taya zasu Zo Masa da zancen radio da kullum ake fadar farashin Sadaki Suka ce Basu da ciko da kyar aka samu wani a wajen cikin abokai ya cika musu dubu biyar sannan aka daura aure,duk garin nan labarin mu ake Yi yanzu Maganar muce take trending inji yan media Suka ce trending, Dagaci ya kalli Gaji yace da alama akwai karya a lamarin Danbinni duk yanda akayi Danbinni ko airport bai sani ba shi da kanshi ya sawa Kansa Alhaji Danbinni makaryacin banza,Dagaci ya sake kurawa Gaji Ido dake Hawaye yace Gaji ta Yan kudu Suka ce you are in Soup,gaji ba Miya Kawai ba Hot Soup me zafin bala’i sai dai Allah ya tsare yanzu za a kaiki mu Kuma Muna nan Muna jiran tsammani muji me zai faru a can gidan Danbinni,Gwaggo tace na shiga Uku ni Gwaggo Anya ba mafarki nake ba,Dagaci yace bude idonki tar yamma ce karfe Uku da minti goma biki akeyi na Yar mu Gaji Muna cikin tararrabi,Gwaggo tace ba Danbinni ba ko Dan Madina ne Gaji in kinji wuya ki dawo gidan ubanki karki zauna bance kiyi hakuri ba karki sake kiyi hakuri a zaman aure a wajena ba hakuri kina Jin ba dadi ki gudo,Dagaci yace af da kaina zanje na dakko ‘yata.

Gaji tunda ta koma wajen kawaye take faman rusa kuka an zaci kukan rabuwa da gidane basu San abinda Gaji taji ba shike damunta,Mairo ma taji labari Gwaggo ta fada mata itama sai da tayi hawaye,Aunty Amarya Kamar yaranta sabo da su zamansu da Gwaggo lafiya sukeyi basa kishi basa fada sai bacin rana matsalar kowa ta kowa ce Kamar Yan Uwa sabo da tsiyarsu tazo daya halinsu yazo daya rashin Imaninsu daya,Yamma nayi motoci biyu kanana kacal Danbinni ya turo Daya ta Amarya da kawayenta Daya ta dattijai Amarya tayi wanka ta canja wani material me kyau ta Sha kyau aka tafi kaita dakin miji Nasihar Gwaggo da Gaji Kawai idan taji wuya ta gudo gida,Shima Dagaci yace ni da kaina zanzo na taho da abata,Aunty Amarya kuwa tana kusa da Gaji itace zata kaita daki da wasu dattijai sai Mairo da wasu kawaye su hudu.

Mu Kuwa washe gari da asuba bayan munyi Sallah bacci Muka koma sai 9 karar wayata ta tashe ni Ina dubawa Naga Saurayina wato Nawwar dagawa nayi cikin muryar bacci sallama nayi masa ya amsa cikin muryarsa me dadin saurare sannan yace hope dai kinyi Sallah,Murmushi nayi ba kunya ba komai nace a’a wallahi diga nake a bule nake yau Jini nake ka gane,na rasa dalili sometimes Kawai sai naji magana fit ta fito daga bani ko bana so na fada sai na fada Ina so na dinga Jin kunya amma na rasa dalili na kasa,Ina so ko Yaya na nuna cewar ni ta gari ce amma abin yaki, yace naji to ko kunya bakya ji,nace ai magana ce ta gaskiya kaga ma yanzu…katse ni yayi yace anjima kadan Zan kawo muku breakfast,nace to kayi sauri yunwa nake ji, wayarsa ya datse,wanka na shiga nayi da brush na fito na shirya cikin wata Yar Riga Yar kanti har kasa wata me hannun vest daga sama Tasha roba ta same kasa ta dan bude kadan,nayi kyau shape dina ya fito sosai,Baba Kulu na samu ta fito ta dakko tsintsiya zata fara shara,da sauri na karbi tsintsiyar nace haba Baba ga yarki yaushe zaki shara Ina nan ki zauna ki huta zanyi komai,

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button