Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 49

Sponsored links

Ita sai yanzu tagane Deen kamar playing dinsu yake daga ita har uban nasa, kullum sai tadinga ganin kamar ubansa ne ya janyesa shiyasa baya zuwa wajanta kwata kwata, ashe haka ubannasa shima yake tinanin ita ta janyeshi? Zatako kyaleshi har sai yagane kurunsa, sai ya tabbatar da bata da amfani a rayuwarsa, saita tabbatar masa da this woman ce ita……

Wayarta ce ta fara ringing, special ringtone din dataji ne yasata dauka da sauri……

“Really?, okay ganinan, ina kusa dama”..

Mami ta fada tanajin kamar anyaye mata duk wata damuwarta ganin wacce ta kira…..

Nnamdi Azikiwe International Airport ta nufa tana dan kara speed din motar…..

Hugging juna sukayi kamar wasu yara ko wacce na farin cikin ganin yar’uwarta……

“Bansan haka nayi missing dinki ba saida naganki”….

Cewar mami da murmushi ya kasa barin fuskarta….

“Wallahi nima haka yaya, ya Allah I never thought zanshigo Nigeria anytime soon, but anything for my saif”……

Dan bata rai mami tayi tace….

“Dana sani na fadamiki duk wani case da akayi dashi, ashe da tuni kinzo, why’re you telling me this just now!”……

“Sorry yaya, ai wannan ya kai azo, yanzu ya ake ciki da case din? Ina Saif din yake? And where is the girl they had accident together?”…….

Tuno da yanda suka rabu da Deen yasa mami fadin.

“Hmmm ki rabu da senseless son dinnan naki, the girl is still in the hospital, ya kamata muje mu dubata ma, mukarasa mota ko?”…..

Haka kuwa akayi sukasa aka daukan musu luggage dinta akasa musu a mota, shiga sukayi mami taja motar… Suka cigaba da hirarsu ta yaushe gamo…..

“Yauwa what do you want to tell me da kikace sai nazo?”…..

Jamila ta fada abun ya tsaya mata a rai….

“Hmmm it’s about yarinyar da sukayi accident tare da Saifuddeen, zamuje ki ganta ai, zakiga abinda nake fada”…….

“Okay Allah ya kaimu”…..

Ta fada tanajin kamar su tafi gurin yarinyar a lokacin…..

“What are you doing about the case, ni nasan Saif baze iya kisa ba!”….

“What are you doing about the case, ni nasan Saif baze iya kisa ba!”….

 

“Na cire hannuna akan case din!!”….

 

“Bangane kin cire hannunki ba?, kinsan me kike fada kuwa? Mubarshi a kasheshi akan abinda nidake munsan be aikata ba?”……

Haderai mami tayi tace…..

“You heard me right! Na cire hannuna, ubansa ya dauko masa lawyer, in kuma an kashesa Allah ya jikansa!!!”

“Ai dama you never take anything serious, bakya san lefinsa na riga nasan wannan karatun”……

 

Dariya ta karayi tace;

 

“Niba haka nake nufi ba, yanzu dai we’re so sorry, in kika cire hannu a lamarinmu bamu san ya zamuyi ba”…….

 

Mami batace komai ba, amma har zuciyarta maganganun Jamila sun sanyaya zuciyarta…

Jamila is the real definition of a calm person, gata very jovial da wuya kaga tayi fushi amma fa intayi fushi ba wanda yake iya controlling dinta……

Parking mami tayi a harabar mansion dinta da kallo daya zaka masa kasan ba karamin dukiya aka narka gurin ginashi ba….

 

Fitowa sukayi a tare, mami tayi leading dinsu ciki….

 

Bayan sun gama kintsawa sun gama komai suka sake fitowa….

 

Direct hospital suka tafi domin su dubo yarinyar ganin yanda Jamila ta kagu taga abinda mami take fada akan yarinyar…..

 

Office din Doctor suka nufa straight dan already mami tayi waya dashi akan suna hanya, shi ya dauka patient ma zasu kawo…..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button