Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 47

Sponsored links

Daidaita nitsuwarta tayi tana tinanin wanda ya fadama daddy ta mutu? Gashi yanzu ya ganta ya dauka fatalwa ce, dole ta mishi bayani yanzu dan yasamu nitsuwar daze fahimci abunda tazo dashi sosai…….

“Relax daddy! Banfa mutuba, ina part din momma sanda mama ta kona part dina”……

Girgiza kai daddy yayi cikin rashin yarda yace….

“Are you sure?”……

“Yes tambayi abdul!”…..

Bece komai ba ya dauki wayarsa ya fara dialing number abdul daya manta when last sukayi waya dalili kuma shine yake ignoring calls din abdul, yanzu ko dole ya kirasa tinda yana bukatar tabbaci akan wannan al’amari, bayan haka ma yanata so ya kirasa guilty conscience ya hanasa……

Saida wayar ta kusa tsinkewa sannan abdul ya daga bayan yagama mamakin kiran da daddy ke masa yau……

“Son how’re you?”….

Daga daya barin abdul da har lokacin be dena mamaki ba yace….

“I’m good! Ina wuni”….

“Alhamdulillah son, kazo part dina yau da daddare I want to see you, meanwhile I want to ask you a question now

Wani ajiyar zuciya daddy ya sauke kana ya kashe wayar…. Sai yaji kamar anmasa albishir da gidan aljanna, ashe shiyasa befara facing consequences din mutuwarta ba? Wato dai tana raye!… Sai kuma yaji haushin kansa na rashin tambayar abdul, to inama abdul din yake? Yaga baze iya wahala ba yabi uwarsa!…..

“I’m so happy that you’re alive daughter, ni kadai nasan irin tashin hankalin dana shiga, yanzu haka hafsah na police station, maganar nan da nake miki gobe zamu shiga court akan case din!”……

Mamaki ne ya kamata ganin yanda daddy yayi taking abun so far,ita tananan tanawa mama shiri ashe har ana chan ana hukuntata bata saniba, well Allah ne ya kamata akan ramin muguntar data gina gashi ta rufta da ita batareda wacce tayiwa tashiga ciki ba… Amma fa dukda haka bazata hakura akan kudirinta ba, dole sai ta nunawa mama iya karta sosai,..

“Can I proceed with my request?”….

Fatima zainab ta fada batareda tayi magana akan case din mama ba, tinda dai yaga she’s alive ruwansa ne ya fito da mama, ruwansa ne ta cigaba da zama achan, ita bashi bane a gabanta ba…….

“Sure! Inajinki daughter”…..

Daddy ya fada yana danne danne a wayarsa, message yake kokarin turawa abokinsa daya kasance DPO akan zezo ya dauki mama anjima, idan yazo ze masa bayani kawai so yake a fara filing bail dinta…..

“Inaso ka aureni!”…….

Ta fada kai tsaye……

Sakin wayar dake hannunsa yayi yana tinanin kunnensa ne beji daidai ba,yace…..

“Kikace me?!!!!”….

“Yes you heard me! Aure nakeso muyi!”….

Ta kuma fada batareda taji ko dar ba…

“No, you must be joking daughter, khaleel din fa? Ya zaayi tsofai tsofai dana in auri kamarki, this is a joke!”……..

Daddy ya fada with an unbelievable look….

Marairaicewa tayi tace…..

“Forget all that, dan Allah daddy ka taimaka ka aureni koda na dan wani lokaci ne”…..

Sakin baki yayi yana kallonta ganin dagaske take, hardasu dan Allah kuma? A iya saninsa da ita in zaayi mata abu ayi in baza’ayi ba she always got alternative, da wuya kaganta tana roko, curiously yace mata….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button