Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 135

Sponsored links

A yanzun kam sarakunan biyu sun baje filin hirarsu a nutse ga matansu a gefensu. Har takai ita dai Iffah ta fara ma hamma. Cikin mamaki Tajwar Eshaan yake mata kalion nan nasa na kasan ido, dan ya fara sakama yawn barcin nan nata alamar tambaya. Abu kadan ta fara hamma, yanzu zata tashi anjima kadan ta sake kwanci. Kuma bazaka taba ji tace barcin yaisheta ba. Anya kuwa? (Sa a bincika mana mai rumawaja🚴).

Duk da dare yayi kai tsaye massalacin MANZON ALLAH (S.A.W) suka wuce, inda nan ma suka samu tarbar da ga shugaban garin na Madina da tawagarsa cikin girmamawa ga Sultan din nasu a Saudiya gaba daya da kuma babban bakonsa shugaban kasar ruman. sai da suka gabatar da salla raka’a biyu sannan sukai zaman jira karasawar lokacin asubahi Basu bar mascalacin ba sal bayan sallar asuba. Yanzun ma dai wani katafaran gida aka kaisu. Gida daya amsa sunansa gida bawai muna gida ba. Gajiyar da ke tattare da kowa yasa ruwa kawai suka watsa kowa ya kwanta musamman ma Iffah dake jin kamar zatayi adungure tun a massalaci

 

68

 

 

………….Lokacin da azhar ta gabato Tajwar Eshaan ya tashi yay wanka ya kimtsa babu alamar Iffah zata motsa, kwance take sharkaf tana kwasar barci kamar wadda ta mutu. Zama yay a bakin gadon ya zuba mata ido, tare da kai yatsunsa saman goshinta da

 

wuyantan amma babu alamar wani zafi da ke nuna tana a cikin ciwo. Da kyar ya tadata tana faman tura baki gaba, ya kafeta da kaifafan idanunsan nan, sake tunzura bakin tai ta kauda kai. Sai shima ya dan girgiza kan a fusge ya furta, “Ki daina turamin wannan bakin na dinga kai azumina lafiya batare da ya raunana ba. A haka za’ai ibadan Nigar?”.

 

Kwalkwal tai da idanunta kamar zata saki kuka tace, “Nima zuwa fa barcin kawai yake, konace bazanyi ba sai na kasa”. Shi dai kallonta kawai yake zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Amma sai bai furtaba ya ce, “Okay tashi ki shirya muje massalaci ga su Sultan na jiranmu”. Babu yanda ta ia dole ta tashi ya taimaka mata ta shirya din, dan a hakan ma sai faman lumshe masa idanun take da sakin hamma. Shi dai lallabata yay suka wuce dan ya fahimci abin bana lafiya bane. Kilama Aljanun nata ne ke sakata barcin dan kar tai ibadar….

Rayuwa a Saudiyya wani rubutaccen al’amari ne da Iffah bazata taba mantawa da shi ba a rayuwarta, dan rubutaccen labarine tsakaninta da Maleek dinta mai zaman kasan ga ma’abocin bibiyar labarinta, amma ta tattara ta killacema zuciyarta kawai kuma sai ku kiyasta da hasashenku. Duk da dai ta samu nakasun raunana a dalilin barcin da bata san kansa ba balle karshensa. Amma duk da haka tana matukar yaki da shi da ganin tayi cikakkiyar ibada. Dan abu mafi birgeta shine yanda Tajwar Eshaan ke tsaye akan kafafunsa koda yaushe babu wasa tattare da shi ko nuna gajiyawa a dare da rana. Gaba daya ya maida hankalinsa a bautar Sarkin sarakunan nan mahaliccin duniya da kayan cikinta, mai rahama da mukullin aljanna. Sarkin da babu kamarsa kai koda kwatankwacinsa ma babu. Gaba daya ya mika lamuransa garesa cikin kaskantar da kai da zubda gwiwunsa bisa kasa. A duk sanda yake addu’a zaka samesa da hawaye share-share da inba gaban UBANGIJINSA ba bazaka taba gani ba. Kullum cikin gayama ALLAH yake kan samun warwarar al’amuran da suka shige masa duhu musamman akan mutuwar yaran da basujiba basu gani ba a daliln aurensa. Duk da wannan jajircewar tasa kuma yana bata kulawa a dan kankanin lokacin da suka daukarma kansu na hutawa. Dan ko bayan kammala Umrah din su bai lamunce su zama a karkashin inuwar lalaci ba.

A gefe kuwa wata Irin shakuwace ta shiga. tsakaninta da uwargidan Sultan. Mace hamshakiya ma’abociyar kyawawan halaye da nuna tsattattacen iko saman na kasa da ita. Nutsuwa sosai Iffah tai tana koyan abubuwa, yayinda itama bata tsaya boye-boye ba ta fito tana gyarama Iffah’r duk abinda zai bata martaba da kima a wajen mijinta da al’ummar da mijin nata ke shugabanta. Dan tayi dubi ne da karancin shekarun Iffah’r da ma labarin data bata na cewar ita iyayenta basu da alakan mulki. Ba halayyar Iffah da dabi’u ba hatta jikinta wani irin gyara yake samu na musamman ga uwargidan Sultan din.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button