Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 76

Sponsored links

“How can you even believe a stranger? Dan iskan ai da yasani ya tsaya danaci ubansa a gurinnan, Well zan baka shawara karka kara bawa shedaninchan face if not kai zaka kwan ciki, ruwanka kuma ka yarda dani ruwanka ka yarda dashi”…..

Cikin zaro ido dan harga Allah har lokacin a tsorace yake yace;

“What do you mean by shedani?”……

“You’ll see for yourself if you keep on believing him har kana zuwa kana min shouting, kaga bacewar nan dayayi? Kadanne daga cikin abinda zaka gani, just give him chance and see”…

“Boss why’re you doing this to me? Kana nufin ba mutum bane, stop giving me uncompleted statement pls, bakaga yanda na tsorata ba wallahi”….

“Bakaga komai ba! I’ve said enough!”…

“Yanzu gidan waye wannan toh?”..

“Mami, ko zaka shiga ku gaisa? Dama nemanka take!”….

“Ni? Haba? Inaa.. Bazan shiga ba, yauwa why are you here? Tagane ka gudu ne?”…

Sameer ya fada a rikice kamar ze zura a guje, be gama fita daga wanchan rudanin ba ga wani kuma, shiko ina zesa ransa?….

“Yes ta kuma gane dasa hannunka, she traced me even before I get to your house, Allah ne ya rufa maka asiri dan har base taje nemanka baka nan, I’ll advice you ka rufawa kanka asiri ka bar garinnan because she’s taking this thing beyond your imagination!”……..

“Innalillahi kace muna ruwa, yanzu haka tana ciki kace?”….

“You can go in and see for yourself, duk abinda ya faru kuma don’t blame be”…,

“Naji naji let me start leaving, but what about the girl? Naje base banganta ba, thought kai ka tafi da ita a daura auren”….

“Wani irin nina tafi da ita? Ina fadamaka ko base banje ba mami tayi attacking dina, kaje dai ka duba inda ka ajyeta, da zaka rufawa kanka asiri daka rabu da yarinyar nan cuz wahala kawai zaka sha a gurin wanchan dan iskan”…..

Cikin kwarin gwiwa sameer yace;

“Wani irin wahala, I’ll know how to handle everything too, bari dai na tafi yanzu inje in kara duba yarinyar”….

“Ok, don’t forget to leave abuja today! If not kasan sauran!”…..

“Yes I’ll, yanzu zanje in duba yarinyar, I’m very sure tana gidan, kawai saina koma US da ita”….

Daga kafada Deen yayi yace;

“As you wish”…..

Sannan ya juya ya shige batareda yajira amsar sameer ba…..

Harya shiga mota wani dan shakku ya shiga ransa akan maganar da Deen ya fadamasa, idan har mami ta kamasa da gaske kamar yanda ya fada zata barshi ya fito kuwa? Sannan dayace a masa sallama da mai gidan meyasa Deen ya fito inba gidansa bane?…. Sai kuma wata zuciyar tace masa Deen baze maka karya ba, musamman bacewar da mutumin chan yayi yasasa karyata abinda ya fada masa, ya dauki maganganin Deen ya yarda dasu…..

Sai kawai ya tada motar yayi ya bar layin…..

Driving yake da sauri yana tsara yanda ya kamata yabar kasar da yarinyar, kamar ance juyo kawai yaga mutum a zaune a bayan mota yana masa murmushi….

Taka burki yayi da sauri yana fadin;

“Na shiga uku, dama Deen saida kace zanga abinda yafi wanchan”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button