Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 50

Sponsored links

Bayan sun gama kintsawa sun gama komai suka sake fitowa….

 

Direct hospital suka tafi domin su dubo yarinyar ganin yanda Jamila ta kagu taga abinda mami take fada akan yarinyar…..

 

Office din Doctor suka nufa straight dan already mami tayi waya dashi akan suna hanya, shi ya dauka patient ma zasu kawo…..

 

Knocking sukayi ya basu izinin shiga…….

 

Zama sukayi suka dan gaggaisa sannan mami tace;

 

“Doctor ya patient din tamu? Kajimu shiru ko, wallahi muna dan settling abubuwa ne”….

 

Murmushi yayi yace……

 

“Yeah nasan dole zaku shiga busy dama, I hope dai sun sakeshi?”….

 

“Zadai su sakeshi Insha Allah”…..

 

“Ok, Allah ya yadda, about the other patient, wani yazo ya dauketa yace shi dan uwanta ne, na dauka ku kuka turoshi”……

 

“Ayyah Allah sarki, toh ba damuwa”…..

 

Mami ta fada tana mikewa ganin tinda ba sanin yarinyar sukayi ba tayiwu yan uwanta sunji labarin accident din sunzo sukazo suka dauketa, so ba amfanin jan maganar kuma, saidai har zuciyarta bataji dadin yanda basu sami yarinyar ba, taso ace yar’uwarta jamila ta ganta wallahi…….

Godiya sukayiwa Doctor din sannan suka fita…..

Suna shiga mota jamila tace;

“Gaskiya banji dadi ba da akace an dauke yarinyar, kinsan gidansu toh muje dan gaskiya I’m eager to see the girl gashi haryanzu baki fadamin abinda kika gani atattare da ita ba”…….

Ajiyar zuciya mami ta sauke tace;

“Wlh bansan gidansu ba, gashi Deen yace shima besan ‘WACECE ITA BA’ even though he has met her before, sannan na manta abinda nagani a tattare da ita wallahi! Kamar wacce aka rikewa baki naji na kasa gayamiki ranar kuma shiyasa nace kizo ki gani da kanki”………

Zaro ido tayi tace;

“Ikon Allah! Toh dan Allah muje gurin Saif din sai ya fada mana inda ya taba haduwa da ita, I’m so curious right wallahi, hankalina baze kwanta ba inba ganin yarinyar nan nayiba nima”…….

“I want to teach him a lesson! Bayanzu zamuje ba, sai ya gane kuransa!”….

“No sis, this is a serious case ko yaya muka matsa akai zaa iya cin galaba akanmu, kiyi hakuri agama case dinnan then punish him later, hannunka baya rubewa ka yar fah”…..

Girgiza kai mami tayi tanajin ko two days ne ya kamata tabashi ta yanda sai yayi losing hope kafin suje even though tasan ba lallai ya damu ba…..

“Kinji sis, ko bazaki ba ki kaini pls, do it for the sake of baby tee inni bazakiyi dan ni ba”……

Shiru mami tayi jin an tabo dayan weak point dinta ko tace weak point dinsu duka, haka sukewa juna in suka kula dayansu bayasan abu, sai suyi using baby tee as a weapon……

Tada motar tayi batareda tace komai ba…..

 

Bata tsaya ko ina ba sai cell din da Deen yake ciki……

 

Zaune yake abun duniya ya ishesa, so yake ko yayane ace masa she’s fine, tinda yazo ba abinda yakeyi sai tinaninta, kota farka yanzu? Is she alright? Isn’t she injured? Ana kula da ita?….. Wa’yannan tambayoyin su suka taru suka cika brain dinsa, hakan saiyasa masa ciwon kai, yana cikin wannan hali kuma saiga mami, yaji dadi sosai saboda yasan koyaya ze samu information a gurinta dan yasan mami da tausayi dole zataje ta kara duba yarinyar, amma sai stupid mistake dinsa ya janyo mami ta wuce ta barsa, abun dariya tana tafiya ya chanja sunan daga ‘this woman’ to ‘birth giver’ (ni ko nace daga baya kenan😹)…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button