Hausa Novels and Stories

Idon Naira 8

Sponsored links

Wata biyar da yin bikin Maryamah Zainab ta shiga Ss1 alokacin Kuma Allah yabata ikon saukar hizifi talatin na alqur’ani daga Nan zuwanta islamiyya yafara qaranci sosai sbd ayyukan dasukai mata yawa na gida,

Barin Maryamah gidan memakon yasa Umma janta ajiki ko yayane dakuma samun saukin ayyuka sai hakan bai samu ba don kuwa Umma tsakaninta da umman umarni da aiki ne sai aikenta datakeyi kaman engine Sam duk nisan anguwa yanada wuya tabata kudin mashin ko a daidaita da qafa take zuwa wani lokaci idan nisan nada yawa sosai shine zata Bata kudin zuwa ta dawo da qafa.

Tariga ta saba aikin Bata mata rai hakama batajin qyashin yinsa,

Akan lokaci takeyin komai tunda safe Idan ta tashi aikine kaman jaka sai dare take samun damar kwantar da kafadunta taji sanyi sanyi ajikinta,

Shara,wanke wanke,wankin kayanta Dana umman,girki da sauran ayyukan komai itace hatta yankar farcen umman itace takeyi mata duk qarshen sati tareda tsifar Kai danma Bata iya kitsoba da itace zatayi mata har shi din.

Duk wannan bautar Batajin haushin umma sbd Bata rasa ciba ko sha hakama sitirar sakawa ana Bata kwancen maryamah ta rage ga karatunta tanayi Alh Barr ya dauke nauyin komai nasu Babu abinda suka rasa na Jin dadi duk da ita Yar kallo ce kawai.

Dangin mahaifiyarta mutum daya ya taba zuwa dubata so daya daga qauyensu

Koda yaga alamar batada gadon komai da mahaifinsu yabari aka raba sai ya tattara ya tafiyarsa batareda ya sake waiwayotaba Dan haka itama batasan Ina sukeba bare inda zata samesu kota sani batada ikon kanta sai abinda umma ta zartar akanta.

Maryamah nacika wata bakwai a gidanta tasamu ciki mai tsananin wahalarwa da laulayi mai wuya Dan haka hankalin ummanta ya tashi Dan kuwa tuni aka kwantar da maryamah din a asibiti gashi basa gari itada mijin nata suna Abuja Dan dawowarsu daga Umrah kenan suka tsaya Abuja sake hutawa kafin su dawo.

A wahale tayi sati daya a asibitin suka sallamota suka tattaro a ranar suka biyo jirgi suka iso gida.

Dawowarsu da washe gari umma ta tafi dubota acan ta wuni Dan haka sai kusan dare tadawo gida lokacin zainb tagama zaman jira a tsakar gidan harta shige daki bacci ya dauketa.

Rashin lafiyar maryamah yasa komai ya rikice a gidanta gashi masu aikinta biyu duk ta koresu sbd rashin tarbiya da nutsuwarsu gashi Alh Asad mai ilimin addini ne sosai Kuma har lokacin duk bayan sallar magriba zuwa ishai karatun addini sukeyi sosai shida malamansa a harabar gidan wani lokacin kuma a masallacin kofar gidan Dan haka idan akai sallar magriba bamai iya shigowa gidan sai bayan ishai.

Ayyukan gidan Dana rashin lafiyarta suka taru suka cakude gashi lafiyayan abinci ake fiddawa idan sungama karatu shida malamansa suci acan Dan haka ba shiri takira umma akan a nemo mata wasu masu aikin.

Kafinma a samo masu Aiki sai gata an sake kwantarwa a asibiti Dole umma ce taje tayi jinyarta a wani babban tsadadden private hospital Alh Asad ya ringa zuba kudi sosai ana kulawa da matarsa wadda itama yanzu koina haj maryamah ake kiranta dashi.

Kwanciyar Maryamah asibiti yasake tsananta ayyukan Zainab sbd itace take abincin safe driver yazo ya dauka,

Hakama tayi na Rana hakama tayi na dare,

Tun shekarunta Basu gama kaiwaba ta iya kusan komai daidai gwargwado.

Ranarda aka sallami maryamah suna kawo umma gida Basu wuceba tasaka Zainab hada Yan kayanta tasakata binsu sbd ayyukan gidan maryamah din dakuma kula da cimar maryamah daketa fama da laulayin zabar abinci.

Zainab batada zabi ko ikon kanta sai yanda akai da ita Dan haka jiki ba qwari ta debo Yan kayanta da Basu fi kala biyarba ta fito tabi driver zuwa gidan maryamah da Bata taba zuwaba cikin wata lafiyayar Jeep black data gama daukan sanyin AC.

Babban gida ginin masu arziki na zamani sai daukan ido yakeyi ga masu gadi har biyu a gidan Nan zainab taga sun shige ta tabbarda Nan ne gidan ‘yar uwarta maryamah Dan haka Bata wani qure koina da kalloba ta sauke kanta tareda sauke numfashi sbd duk wani abu daya shafa maryamah baya baya takeyi dashi tareda nutsuwa sbd yanda alaqarsu take Sam idan ba gaisuwaba Babu abinda maryamah takeyi da ita Dan haka ko yanzu dinma sanyi jikinta yayi Tana tsoro tsoron idan maryamah din tasan da zuwanta da umma tasaka.

Har kofar shiga babban palon dazai sadaka da cikin gidan yakaita ya babbuga kofar tareda juyawa yabar gurin.

Yana barin gurin wata dattijuwar me Aiki da aka kawowa maryamah daga gidan hajjar Alh Asad ta bude kofar Tana kallon Zainab da a Dan fizge Tana diban kama da maryamah Amma ba’a ganewa Kai tsaye.

Shigowa sukai bayan Zainab ta gaida matar kanta a qasa..

Babban palon alfarma ne da kusan Babu abinda ya rasa na tsarin gidajen masu arziki,

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button