Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 26

Sponsored links

Har ze nufi part din Deen ya fasa,ya nufi na mahaifiyar Deen,ze iya cewa ya dade bege mutum me kirki kamarta ba shiyasa in dai yazo gidan saiya fara zuwa ya gaisheta…..

Knocking yayi bakinsa dauke da sallama sannan ya shiga dan shiga yake kai tsaye tsabar yanda ya zama kamar dan gida saboda abokantakar su da Deen….

Zaune take ana mata yankan farce,jin anshigo yasata dagowa…. Murmushi tayi sosai tace “Lah ya sameer yaushe a gari”…. Karasowa yayi yana mayar mata da murmushin yace “Yau dinnan,ina mom?”… Tana ciki asabe tashi ki kirata ta landline.. Mikewa asabe tayi da sauri domin aiwatar da abinda aka sata…..

Da sallama ta shigo parlourn fuskarta cike da fara’a na ganinsa…. “Lale marhaban,son yaushe a gari haka ba labari?”……

“Wlh yau nazo kano,jiya dai na iso”…..

“Ah masha Allah,munyi kewarka wlh,sai katafi kayi zamanka a UK?”

“Yanayin aiki ne wlh mom”…

“Gaskiya ne kuma,amma dai ya kamata ana lekomu,Khadija kuje da asabe a shiryama son abinci”…..

“Okay” Khadija ta fada tana mikewa da sauri…..

Juyowa mom tayi ta fuskanci sameer tace “Kuna waya da Deen kuwa?”….

“Wallahi bamuyi waya ba for the past one week,idan na kira baya picking,yanzu gabadaya wayarma bata shiga,abinda ya kawoni kenan inji ko lafiya”….

Fashewa da kuka mom tayi tace “Sameer na rasa yanda zanyi da Deen,nema yake kawai ya lalata rayuwarsa da gatansa da komai nasa”…..

 

“Mom pls stop crying dan Allah kimin bayanin abinda ya faru”… Ya fada cike da tausayinta,abun da ciwo ace ka haifi yaro baka haifi halinsa ba,bawai Deen yanayin wani abun banza bane saidai sam Deen bayajin magana,in dai yasoyin abu to fah ba wanda ya isa ya hanasa,kamar wanda ake zugawa sai yayi abinda yayi niya,sam bayajin maganar Dad sai yaga dama,har gwara ma mom yana dan shakkarta,shiyasa kullum basa shiri da Dad……

“Saida mahaifinsa ya basa warning akan zuwa abujan nan ya kiji,infact a ranar daya dawo ma ya koma,sai kawai mukaji kira wai Deen yayi accident,Haka na lallaba alhaji na nuna masa hannunka baya rubewa ka dauka kayar dan da alhaji cewa yayi yaje ya karata tinda bayajin maganarsa,niko bazan iya jurewa ba a matsayina na mahaifiyarsa…..Da kyar na samu ya yadda muka tafi abujan,in kaga halin da muka samu Deen wlh saika tausaya masa saboda sam baya cikin hayyacinasa,haka likitocinnan suka taru a kansa,a washegari kuma aka nemesa aka rasa can you imagine?” Mom ta fada still tana kuka

Girgiza kai kawai Sameer yayi dan shi ya rasa ma me zece,hango khadija da maids biya da ita dauke da trays ne yasa mom tashi tacewa sameer bari na baka guri kaci abinci…. Binta da kallon tausayi yayi sanin kuka zataje ta cigaba dayi……

 

Saida suka shirya dining din tsap sannan maids din suka fita,khadija ce tace “bari nima na baka guri kaci abinci,inka gama mayi hira”….. Daga mata kai kawai yayi yana tinanin to ina Deen ya shiga……..

Zaro wayarsa yayi ya sake gwada number Deen,cikin ikon Allah ko sai gata tana ringing amma harta katse baa dauka ba,sake gwadawa yayi ko Allah zesa a dace,kamar a mafarki ko yaga andaga wayar……

 

“Who is disturbing my sleep” Deen ya fada daga daya bangaran dan daga wayar kawai yayi batareda ya duba suna ba….

 

“ Amma dai wallahi kaji tsoron Allah Deen,muna nan a cikin tashin hankali muna nemanka,kai ashe kanachan hankali kwance har complain kake an dame ka”…. Sameer ya fada rai a bace ganin ashe Deen dinma yana lafiya

 

Jin muryar sameer yasashi cewa “Bangane kuna cikin tashin hankali ba, kai ba mun aikaka UK ba,toh meye hadinka da abinda ke faruwa a naija?”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button