Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 177

Sponsored links

Washe gari an tashi masarautar a rincabe da tashin hankali kala-kala matuka. Dan haka kawai aka samu gawawwakin hadimai da Ghazi da jami’an taro sama da hamsin an musu kisan gilla a daren jiya. Ga Iffah tun fitar aljanun nan jiya da ga jikinta barci kawai take, lokacin salla ne kawai idan yayi take tashi da kyar tayita. Tana idarwa kuma zata sake komawa ta kwanta kamar wadda tasha wani abu ko batun abinci ma ba’ayi. Tashin duniya Tajwar Eshaan yayi amma taki tashi in har ba lokacin salla ne yayi ba. Ga a jiya da dare yaje ya duba Malikat Bushirat dake ta faman zabura da ihu sam batai barci ba itama jikin ya sake rikicewa. Hakama duk wanda ke zagaye da ita bai barci ba. Safiyar yau kuma kawai ta tashi da wasu irin manya-manyan kuraje masu radadin azabar zafi dana kaikayi. Kuka kawai take tana rokon a cire mata. Ga sunayen Zawjata-almilk da suka rasu sai lissafowa take daki-daki wai sunzo zasu kasheta, sun zo daukar fansa.

   Gaba daya kowa ya kasa fahimtar komai da ga zantukanta, sai dai duk mai imani ya ganta sai ya ji tsoron ALLAH ya sake kamashi. Kusan a tare babban yayansu da Kaka da akaima kiran gaggawa cikin masarautar suka iso. An fara taruwa an ma gawawwakin wadanda aka rasa salla harda Tajwar Eshaan, bayan an kammala biznesu ne kuma aka rufu kan Malikat Bushirat da zuwa yanzu kurajen duk sun rure da ruwa. Duk wanda yay mata kaikayi ta sosa kuma azabace mai zaman kanta. Shiru kawai kaka yay yana kallonta, yayinda duk wanda ke cikin dakin dan yan uwanta duk sunzo kuka suke sosai. Babban yayansu da shima ke kallonta ya juyo yana duban kaka. Cike da girmamawar kasancewar ya fisa shekaru ya ce, “Baba wannan aikin jinnu ne kam tabbas. Amma miya hada Jinnu da Bushirat duk da dal an sanar min da dambarwar da ake fama da ita a gidan.

   Ajiyar zuciya kawai kaka yayi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da fadin, “Wannan al’amari ne kam da ya kamata muji a bakinta, dan babu rami babu abinda zai kawo rami kam. Ambaton sunayen wadanda suka mutu da fadin karsu kasheta da take babbar ayar tambayece a gareta Abni”.

Babu wanda bai gamsu da zancen kaka ba a wajen, sai dai kuma hankalinsu ya tashi da jin abinda ya fada din. Dai-dai yana fiddo wani magani Tajwar Eshaan ya shigo dakin rike da hanun Iffah da farkawar ta kenan ta zabura. Riketa yay amma ta rokesa ya barta sashen Ammie zataje. Shima bai jima da baro sashen ba, dan tafiyarsa babu jimawa su kaka suka shiga. Zaunar da ita yayi sannan shima ya kai zaune, take aka shiga mata sannu sai dai babu wanda ta amsawa. Kaka da babban wan su Malikat Bushirat din suka sake mika gaisuwa ga Shahan-shan dan sun gaisa tun shigowarsu masarautar. Da ga haka Kaka ya bada maganin da ya fiddo yace amata hayaki da shi. Cikin sauri suka amsa aka zuba a burner da aketa bulama turaren wuta saboda kurajen Malikat Bushirat din duk wanda ya fashe wari yake yi kamar an tono rubabben nama a cikin kasa. Wani irin fisge-fisge ta dingayi da hun da ya saka Tajwar Eshaan lumshe idanu kawai idanunsa sun kada jazur abin tausayi, shi Iffah ta tsurama ido, ji take da’ace tanada damar sashi ya bar masarautar nan a yau data sakashi, dan sam bata son ai wannan tone-tonen a gabansa. Amma yaya ta iya, bazai yuwu ace a wannan dambarwar babu shugaban wanna kasar gaba daya a cikinta ba. Malikat Bushirat ta jima tana fisge-fisge gashi babu damar taba ta saboda kurajen jikinta itama in ta taba radadi take ji, dan kanta ta lafa bayan ta gama jigata. Yanda ta nutsu yasa kowa tunanin ma Kota mutu ne. A razane Jasrah ta shiga kiran sunanta tana kuka, sai da Kaka yace ta kwantar da hankalinta tanada ranta, turaren zai rage mata radadin kurajenne matuka. llai kuwa sai gashi ta bude ido. Gaba dayansu tabi da kallo daki-daki, yayinda wasu keta tofa mata addu’oi kamar yanda yayanta ya basu umarni tun dazun. Wasu. hawayene masu radadi suka shiga zaryar zubo mata lokacin da idanunta ke sauka akan Tajwar Eshaan da Iffah. Ta jima tana kallon su, sai kuma ta sake fashewa da kuka.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button