Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 18

Sponsored links

Awan khaleel biyu a toilet sannan Allah ya bashi ikon farkawa daga suman daya yi,kalle kalle ya shiga yi tsabar rudewa sai yaga kamar ita yake hangowa ta gurin windown toilet,wani ihu ya rusa yana cewa “Wayyo Allah,azo a taimakamin,dan Allah kiyi hakuri na tuba,bazan sake ba wallahi kimin rai sharrin shedan ne,ki tausayamin ki rabu dani”……. Sai kuma yaga ya daina ganinta kamar wacce ta bace,ai saiya kara fashewa da kuka….. Kamar ance ya kalli gefenshi,sai yaga kamar ita,ihu ya sake zawo na zubo mishi ya kuma sumewa (nan ko duk hallucination ne tsabar yanda yasa abun arai,amma bata gurin,ita tana chan tana shan baccinta)……….

After one hour khaleel ya sake farkawa daga suman wucin gadin da yayi,sai a lokacin ya fara karanto addu’oi,nan da nan ko yaji wani nitsuwa ya saukar masa,sai a lokacin yaga wautarshi na mantawa da Allah tintini……….

 

Mikewa yayi da niyar kunna shower,gabadaya yaga jikinshi ya baci da zawo da fitsari,he couldn’t believe wai shi classic khaleel ne a haka…. Girgiza kai kawai yayi ya sakarma kansa ruwan sanyi,sannan yayi wanka…… A hankali yake leka dakin sadap sadap dan ganin ko tana cikin dakin haryanzu,ajiyar zuciya ya sauke ganin bata dakin,fitowa yayi ya nufi kofar dakin ya rufe da sauri sannan ya shirya………

2am dot kamar an tabata ta farka,alwala ta dauro,tazo ta tada sallah,sosai take hawaye tana tsawaita dukkan sujjadanta,nafilfili ta cigaba dayi har saida taji kafafuwanta sun fara mata nauyi sannan ta haqura ta dau qur’ani ta fara karantawa,saida taji alarm din dake dakin yayi ringing alamun sallahr asuba tayi sannan ta hakura ta tada sallah,tana idarwa ta daura da azkar……… Mikewa tayi ta sake yin wanka,drugs ta kuma sha,wani baccin ya sake kwasheta………

Karfe goma na safe khaleel ya fito parlour,dube dube ya shigayi yana nemanta,a tsorace ya kalli dakin dake gefen nasa,yasani indai tana sama to tabbas tana ciki…. Da sanda ya sauka kasa,har wani hamdala ya sauke ganin bata kasa,kwasar takalmansa yayi a hannu ya fita daga parlourn a guje😹………..

 

Zaune take a katafaren parlourn nasu,hannunta dauke da remote,idonta kur akan tv,idan ka kalleta a haka zaka dauka tabawa kallon dukkan hankalinta,saidai sam hankalinta baya kan tv’n,ta nitse a kogin tinanin da tasan baze Fissheta ba,anfi sati kenan da bata ganta ba,tin bayan ta hankadeta ta fita bata sake dawowa hostel ba ,ita kuma tinda tayi tozali da hannayenta taji tanasan sanin WACECE ITA?,babban abinda yake damun eesha shine meyasa ta hankadeta bayan nufin taimakonta da tayi?….. Tin bayan wannan rana bata kara samun nitsuwa ba,burinta kawai taga ta dawo ta samu ta tambayeta meta mata ranar data ture ta sannan ta bata hakuri,amma shiru kamar wanda taje kai bawa garinsu,bata kara dawowa hostel ba,ita kuma eesha sai tasa a ranta itace silar rashin dawowarta hostel,shiyasa abun ke damunta sosai…….

“Aisha,Aisha!”…… Firgit ta dawo daga duniyar tinanin data fada,karasowa wacce ke kiranta tayi ta zauna kusa da ita,dafa kafadarta tayi tace “tinanin me kikeyi haka?,sai magana nake bakyaji,what’s wrong with you?”…….. Sallamar mahaifiyar eesha ce ta katsesu,karasowa tayi tace “ah toh tayani tambayarta dan ni dai nayi iya yina taki fada,maybe ke ta fadamiki”………… Murmushi kyakkyawar matar dake late 50s dinta da tsabar gyara da hutu sai kayi tinanin batafi 38 ba a duniya,ta dubi eesha tace “look daughter,you know I’m a good listener plus I won’t judge you,ki fadamin damuwarki karkiji komai,okay?”………. Mamaki ne ya kamasu ganin eesha ta fara hawaye,nan tashiga basu labarin little she knows about fatimah zainab dako sunanta bata sani ba,har zuwa ranar data hankadeta,da neman da take mata amma taki dawowa har yau……….

 

Gabadaya sai suka zama speechless suka cigaba da bin eesha da kallo……. Chan aminyar mahaifiyar eesha tace “As a judge,the girl is suspicious!”…… “Yes she is!” Mahaifiyar eesha data kasance itama judge ta kara da cewa…. Murmushi aminiyar ta sakeyi tace “amma ga wani tactics,nasan Insha Allah in kikabi a sannu zaki san WACECE ITA,just keep me updated,I’m interested too!”….. Gyada kai eesha tayi tace”Take you mom”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button