Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 2

Sponsored links

 

Jin wannan bayanin daga bakin hajajju yasa jikin Sehrish yin sanyi , bata ce mata komai ba sai ma ta ci gaba da wasa da yatsun hannunta. Ci gaba da magana hajajju tayi “abunda za’ae tunda dai naga sisters din naki kuma munyi magana da gwaggo da take kula daku , ynx ki koma ki ci gaba da kula dasu saboda suna bukatarki kafin Allah yasa asamu aikin ,”

 

Kamar an dasa ta haka tazauna idonta suka ciko da kwalla, kiris take jira ta fashe da kuka , dama bata jima da gama wancan kukan ba

 

Wayar dake hannun hajajju ce ta soma ringing , picking tayi tare da karawa a kunnan ta tana fadin ” Manyan manyan gari ! Abban sojoji ashe kana nan ba’a neman mu , koda yake dama ku hamshakan masu kudinnan ganin ku sai an cike file.”

 

Natsuwa sehrish tayi tana sauraranta , ta lura da yadda hajjaju ke washe baki da alama koma wanene take wayan dashi Babban mutum ne ,

tuna damuwar da take ciki yasa ta daina sauraron wayar tasu ta shiga tunani kala kala a cikin zuciyarta , har hajjajun ta kammala wayar bata sani ba sai da taji tace “Ga samu ga rashi !!” dagowa tayi da idonta tayi tana kallon , hannu hajjaju tasa ta dafe kanta alamar takaici.

 

Sehrish tace “Hajiya meya faru?” Hajajju tace “Aiki ya samu mai tsoka , jin hka yasa sehrish ta soma murmushi “amma sai dai kash Namiji suke so mai aiki ba mace ce ba !” lokacin da hajajju ta idasa maganar tuni sehrish ta gumtse fuska hankalinta ya tashi.

 

Hajjaju ta ci gaba da cewa “ina tayaki bakin ciki gsky, sbd kinga mutumin nan daya kira ni ba karamin mai arziki bane , cos they can pay u 50k as your salary after that zasu dauki dukkan responsibilities din ! Ci da shan ki wurin kwana lafiyayye sannan har school zasu iya saka ki ga sutura ya kike gani “?

 

Takaici ya hana tace komai ga samu ga rashi , ji take kamar ta cire takalmanta ta watsa da gudu saman titi kota rage radadin da take ji a zuciyanta ,

 

“Sehrish kinyi shiru baki ce komai ba “? ta jima ba tare da ta ce wani abu ba sai da tayi zurfin tunani kafin tace “ZanJe ! Zan yi aikin a matsayin NAMIJIN akan y’an uwana babu abunda bazan iya yi ba don nayi basaja a matsayin namiji wannan abune mai sauki a wurina ,”

 

In serious matter take mgnan ba tare da jin wani dar a zciyarta ba dagaske take dai , murmushi hajjaju tasaki don ba karamin burgeta tayi ba saboda tana da confidence akan komai da take so , ” hmmm sehrish kenan how can u change ur creator frm a girl to a boy i dont think u can act like a male zasu gane ki ne , ”

 

Matsawa tayi kusa da hajiyar tare da rike kafarta tace “Don Allah hajiya ki taimake ni wlh zan iya , indai za’a samu makeup artist din da zai tsara ni ya mayar dani kamar namiji this is a simple thing , kawai amincewarki nake bukata,”

 

hannu hajjaju tasa ta cirewa Sehrish hannunta data rike mata leg dinta dashi sannan tace “Babbar magana ! tun da nake bantaba yin wannan kasadar ba , natura house maid mace a matsayin namiji , sannan wannan mutumin da kika ji ina magana akan sa wato Abban Sojoji , y’ay’ansa maza goma sha takwas kuma dukkansu sojoji ne masu rike da manyan mukamai , dalilin dayasa yace namiji suke so a matsayin d’an aiki saboda ba yadda za’ai mace ta iya , bai ma dace ba , balle ma yaransa da kwata kwata basa da sauki , zafin rai ga ji da isa ,

Kamar zata yi kuka ji take in har hajajju bata amince mata ba zata iya rasa ranta , cikin kasalalliyar murya tace “Hajiya ki amince mun kawai ae ni nace zan iya wlh idan baki amince ba shinkafar bera zanci kawai na mutu kowa ya huta don bazansu naga mutuwar y’an uwana ba , ” zaro ido hajajju tayi jin ta anbaci zata je taci shinkafr bera , kuma dagaske take ba alamar wasa a mgnrta ,

 

ruko hannunta tayi saboda harta mike zumbur zata figi hanya , “Meya yi zafi haka dawo ki zauna kinji , ni bazanso nayi sanadiyar mutuwar wannan innocent face din ba ,” komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya ,

 

Shiru suka yi na wani lokaci daga ita har hajajju , jin shirun yayi yawa yasa tace “Hajiya baki ce komai ba am so eargerly to hear frm u ,” ta karasa maganan tana kallon ta ,

Wan nan shirun da hajajju tayi sake sake takeyi a cikin zuciyarta “taya zan kai yarinyar nan gidan soldiers a matsayin namiji ! duk ranar da asiri mun ya tonu daga ni har ita kashin mu ya bushe , maganar da sehrish tayi ce ta dawo da ita , ” Sehrish i dont know what to do am just comfused ina tsoron hakan fa ,”

 

“Nima ina goyon bayan yarinyar nan” larai ce tayi maganar shigowarta kenan taji suna tattauna wa , bin ta su kayi da kallo , wuri ta samu ta zauna kafin taci gaba da magana “Wurin samun biyan bukata rai ba abakin komai ya ke ba , tun da har tace zata iya kawai ki amince mata ! saboda ni na taba kallon wani korean film irin haka actress din ciki ta yi shigar namiji ba tare da wani ya gane ta ba kuma tacimma nasara ,” jinjina kai hajajju tayi tare da watsa hannayen ta tace “Shikenan Finally i agree tunda har larai ta Jefa miki kuri’a kun rinjaye ni ,” dariya sukayi su duka ba karamin dadi sehrish taji ba , ynx hajajju ta yarje mata sauran shirin yarda abun zai kasance

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button