Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 12

Sponsored links

Tinda Deen ya tafi yake Allah Allah ya dawo yaga me sallarnan,shiyasa yana zuwa nan da nan ya dibi portion na sample din yasa a microscope sannan yayi detecting duk wani abu da yake cikin sample din,ya fitar da result,ya fita daga asibitin da sauri,abokinshi safwan ya bishi da kallo ganin yanda ya mayar da hankali akan aikin dayazo dashi,a iya saninshi dashi yasan aikin lab ma saidai ya bayar ayi badai yayi da kanshi ba……. Shiko Deen bema san yanayi ba,abunda yake gabanshi ma ya ishe shi………

 

Da sallama ya shigo parlourn yana dube dube kamar me neman wani abu,burinshi kawai yaga me sallah,sai kuma yaga wayam ba kowa a wajan ga kuma abun sallahn na nan…. Alhaji ne ya hangoshi yace “karaso mana son, harka dawo?” Daga kai yayi yace “Eh dad” Yana mikoma alhaji result din….. Sai alhaji ya umarceshi daya bude ya sanar dashi menene result din…. Numfasawa yayi yace “Anyi injecting food din da botulinum toxin injection”… Kallonshi yayi yace “Expand Doctor”….. Dan shiru yayi sannan yace “Shi ake cewa ‘miracle poison’,wanda idan mutum yaci abincin da aka sakashi a ciki,ko five minutes bazai kara a duniya ba,it is so deadly”…… Jin hakan yasa gabadaya wa’yanda ke parlourn suka zaro ido suna kallon Doctor,shiko daddy dafe zuciyarsa yayi yace “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” sannan ya danne zuciyarsa yace”Thank you son,you can go”…… Ai ji yayi kamar ya cewa alhaji ze zauna,saidai bazai iyaba,shi in an tambayeshi me yake damunsa yanzu ma bayace gashi ba……. Sallama yayiwa alhaji ya fita yana tafiya kamar wanda beda laka……….

 

Fitowarta kenan daga part dinta bayan tagama bawa cikinta hakkinsa,taga anja mota an nufi gate,bin motar tayi da kallo tanajin wani iri a ranta,chan kuma saita danyi tsaki ta nufi parlourn tana dan wani sake sake a rai………

Tana shigowa kowa ya zuba mata ido,banda daddy da yaketa girgiza kai yanata salati,gabadaya yaji ya zama speechless dukda tarin abubuwan dake ranshi…. Karasa inda daddy yake tayi,sai tace “wai haryanzu baa kawo result din ba”….. Kasa bata amsa daddy yayi saboda besan ta ina ze fara ba,tabbas saiya hukunta mama amma kuma zai so ace Fatima Zainab baza taji wannan magana ba…….. Itako ganin ya mata shiru yasa ta dakawa ameera tsawa tace “ke dan uwarki meyafaru akayi shiru haka kamar gidan mutuwa”………. “Ehm eh daman mmm mama ce,mama ta saka poison a abincin” Ameera ta fada a kidime,harji take kamar ta saki fitsari tsabar yanda tsawar ta daketa,gashi dai tsawar ba wani me sauti bane amma har cikin kwakwalwarta tajita………. Tsare ameera ta cigaba dayi da kallo alamun tana bukatar karin bayani,ameera ko bata san lokacin data zayyano mata duka abunda Doctor yace ba…… Sai a lokacin daddy ya fusata yace “kin bani mamaki hafsah,ashe har zaki iya kisan kai? Ashe da muguwa nake zaune tsawon wannan lokacin bansani ba?,meta tsare miki a duniyarnan? Kinsan ko WACECE ITA?,kinsan gangancin da kike neman tafkawa kuwa?,bazan taba yafemiki abunnan da kika so aikatawa ba,domin da kin kasheta daba karamin masifa zaki jawo min ba,Allah ya isa tsakanina dake hafsah,kije NA SAKEKi!!!”….. Alhaji na fadin haka mama ta fashe da kuka ta durkusa a gabansa,sai ihu take tana cewa “Alhaji dan Allah dan annabi kamin rai,na tuba,wlh kuskure ne da sharrin shedan,idan kace in bar gidanka bansan inda zani ba”…. Ko kollonta beyi ba ya fice daga dakin….. Sai a lokacin Fatima zainab ta fashe da wani mugun dariya tana tafa hannu tace “Wai da ni zaki kashe?,Ina miki kallon shashasha ashe kinada hankali har haka? Wow” Ta kuma fashewa da dariya sannan tace “Dadin abundai kika kasheni danku kika yiwa asara,dan na tabbata ina mutuwa ze hadiyi zuciya ya biyoni”…… Mama kam in banda kuka ba abunda takeyi,ya’yanta na tayata,ganin Fatima zainab ta nufi hanyar fita yasa ta bita da sauri ta riko kafarta ta fara rokonta tace “Dan Allah dan annabi fatima zainab kiyi hakuri,na tuba,wlh sharrin shedan ne,ki taimakeni kiyiwa alhaji magana ya mayar dani dakina ,nasan ke kadaice zakiyi masa magana yaji”…… Hankadeta tayi tace”mu zuba nida ke,bakiga komai ba”……….. Koma tayi ta zauna tana zaro wayarta daga cikin bag,call log dinta tashiga tayi dialing numbersa sannan tasa a hands free,mama ta bita da kallo cikin idon tausayi tana addu’ar Allah yasa alhaji zata kira ya maida ita dakinta……..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button