Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 89

Sponsored links

Daganan bata karan jin abinda sukace ba amma hankalinta ya tashi, duka taji sunayen da aka fada saidai bata sonsu ba bare tace zata taimaka musu, toh wani taimako ma bayan ance an kona inda suke?… Ta dade da sanin daddy is doing something illegal saidai batasan abin nasa ya kai haka ba…..

Tana cikin wannan hali daddy ya sauko, da sauri ta saita kanta kamar bataji komai ba, shima be damuba dan beyi tinanin taji ba…..

Mika mata zobe yayi yace;

Yanda yaga rana haka yaga dare ranar, duk yanda yaso ya rintsa kasawa yayi dukda yayi tracing din inda akayi parking motar yaga bakin hostel hakan kuma ya tabbatar masa school ta tafi kenan, zuwanta school din ya fiye masa kwanciyar hankali amma ya rasa meyasa ya damu sosai, hakanan yakeji kamar something isn’t normal and it’s about her, abun mamaki sai gashi ya dauro alwala ya shiga sallah akanta yana mata addu’ar Allah ya kareta, abinda ko kansa bayama addu’a sai gashi yau ya bata night dinsa akan wata shakatafi dan shi dai be taba sata a jerin masu hankali ba, har aka kira sallar asuba hankalinsa be kwanta ba…..

Yaso ya fita tunda asuba amma dayake bacci barawo ne sai ya sace sa, bashi ya farka ba sai after 9….

Da sauri sauri ya shirya yana duba tracker ko tabar hostel……

Parking tayi a Hilton idonta na sauka akan disposable nose masks dake center motar, zaro guda daya tayi kai kace nata ne ta fito tana kokarin daura wa, kamar ance juyo tagansa few inches away from her, batasan sanda ta saki nose mask din a kasa ba irin kayiwa mutum abu ya kamaka red handed yanz..

Tun kafin ta fito yake tsaye a gurin tun tana kokarin zaro nose mask, badan yasan motar bane cewa zeyi ba ita bace ba, he has always imagine how she’ll look under that hijab, ashe haka take, very very breathtaking? Could it be the reason why she’s always covered? Besan ya yar da wayarsa a kasa ba saida yaji tace;

“Mallam bani hanya in wuce, ba abunda ka iya sai tarewa mutane hanya”…..

Sai a lokacin ya dawo daga suman wucin gadin dayayi ya shiga kallonta sosai tundaga sama har kasa, sosai yaji ransa ya baci ganin yanda abayar ke nuna shape din jikinta, dan kallon gefe yayi yaga ko akwai wa’yenda suke kallonta….. Nannauyen ajiyar zuciya ya sauke ganin ba mutane a harabar gurin……

Sai ya dawo da idonsa kanta, ya haderai sosai yace;

“Ko kunyar kin sace min mota bakiji ba? Saima wata magana da kike fadamin?”…..

“So nawa zan fada maka abun kunya gaba na basa ba baya ba?”….,

Kwafa yayi ya duka ya dauki wayarsa da screen din ya dan tsage kadan yace;

“Ni bama wannan ba meya hanaki sa hijabi yau?”

Sosai maganarta ya basa dariya ya daure yakiyi dan da gaske bayasan rashin kunya, dole kuma ya saita ta tana bashi respect……

“Zan saita ki very soon! And what took you to Alhaji Ibrahim’s house?”…..

“Wannan kuma kaika san shi!”….

“Zanyi maganinki, sannan zaa fara exam next week, I don’t think kinyi test ko guda daya, wata kalan unserious student ce ke?”….

Murmushi tayi da saida ya jingina da motar dake gefensa aranshi yana ce mata“seductive bitch” sannan tace;

“Sai yau kasani? Banyi test ba exams dinma idan naga dama bazanyi ba and I’m not gonna fail any course!”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button