Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 20

Sponsored links

Ko bi takan khaleel batayi ba ta sauka kasa,ta nufi hanyar fita da niyar taje ta ci abinci sannan,tinani ta shigayi to ina ma zata fara,sai kawai ta yanke shawarar duba kitchen din khaleel ko zata samu abinda zataci,tana shiga ko ta tarar da abubuwa dayawa saidai duk basu mata ba,kawai saita fita daga kitchen din…….

 

Bude kofarta kenan shi kuma yana kokarin knocking…… Karo sukayi shades dinta ya fita daga idonta ya fadi kasa,kallon kallo suka shigayi a tsakaninsu kafin a hankali yace “Fata barakallahu ahsanil khaliqeen” saboda arba dayayi da kyawawan lumsassun idanuwanta,da gashin gefen kunnenta daya kwanta kamar dasasa akayi a gurin,gashi sai sheki yake,kafin ya gama tantance yanayin da yake ciki yaji ta hankadasa,amma ko gezau kamar baa tabashi ba,saima kokarin cire nose mask dinta da yake domin yaga fuskarta da lokaci daya ya kwadaitu da san gani……..

Rikicewa Deen yayi yanaji kamar yayi karamin hauka,fadi yake tabbas da zai iya dawo da moment dinsu baya daya dawo dashi ya tsige niqab dinta,infact dayasani sace ta yayi kawai ya huta,ya killaceta har sai ta fadamasa WACECE ITA?,amma how could he be so foolish hartayi fooling dinshi haka?,shi har zuciyarsa ya dauka aljanu ne da ita,ashe he was mistaken kawai ta masa wayo ne,be manta da abunda yaji ba,be manta da laushin jikinta da haryau ya kasa tantance wani irin laushine haka kamar wacce batada kashi a jiki?…. “Ya Salam” Ya fada yana dora hannu akai,sai kuma ya koma street din da suka hadu,still be ganta ba,sai ya cigaba da tafiya a kafa batareda yasan ina ya nufa ba,saida ya shiga duka streets din dake area amma begantaba,takaici ne ya kamasa kawai ya zube a kasa a tsakiyar titi dayake irin isolated area dinnan ne da baka samun mutane sai tsiraru,lumshe ido yayi ya cigaba da tinanin inda ze ganta……… Yana cikin wannan halin yaji phone dinsa na ringing,wayar dayayi abandoning for days,yana ganin ana kiransa amma baya dagawa,yana sane kuma yaki kashewa…… ‘This Woman’ ya gani akan screen din kamar yanda ya mata saving,for the past two months tana kiransa amma baya dagawa,yau kawai yaji yanasan dauka….. Picking call din yayi yasa a hands free….

Cikin muryarta me cike da kamala tace “Assalamu alaikum Saifuddeen”….. Shiru yayi yana me jin wani sanyi a ransa,sai kawai ya amsa sallamar a zuciya…

“How’re you doing?”…

“Gida”… Ya bata amsa a gajarce

 

“Baka gida saifudden!, kabar inda kake”…. Kashe wayar kawai yayi jin zata fara rainin hankalin data saba….. Cigaba da kira tayi babu kakkautawa,yana gani kuma yaki dagawa,daya gajima sai ya kashe wayar gabadaya…..

 

Cigaba da zama a gurin yayi kamar me neman gafara,ya lumshe ido yana tinanin yanda ze bullowa alamarin daya damesa…….

 

Kamar ance ya bude ido kawai yaga mutane kusan 20 sun zagayesa ko wanne dauke da bindiga a hannunsa fuskokinsu rufe da mask,kafin ma ya motsa suka fesa masa wani abu dan sunsan tsap zece zeyi kokawa dasu and he can play very smart,a take ko abun da suka fesa masa ya sumar dashi,suka kinkimesa suka sasa a mota sukayi gaba dashi……… Ogan su ne ya dauki waya ya shiga kiran wanda yasasu aikin….. Ana daga wayar yace “Deal done!,ko a kashesa kawai boss?”…. Banji me aka ce a dayan side dinba,ogan su ya sake cewa “Your wish is my command”…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button