Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 15

Sponsored links

Tinda aka shiga da Deen emergency likitoci ke kansa,taimakon gaggawa suka bashi ganin yana internal bleeding,iya taimako sun bashi sannan kuma suna expecting farkawarshi anytime soon,amma shiru ba labari,tini Dad da Mom sunzo abuja,Dad sai fada yake akan yayi warning dinshi akan dawowa abuja,amma dake kunnen kashi ne dashi be jiba,toh zeyi maganinshi very soon,ze mishi abinda dole ya zauna guri daya…. Mom dai lallaba dad take tayi,tana kuma bashi shawaran yanda zasu shawo kan abun…… Ansamu komai ya daidaita har anfita dashi daga emergency amma kume be farka ba,mom da dad na zaune a aminity din da aka dawo dashi…….. A hankali Deen ya fara bude idonsa,sai yaji kansa ya sara masa,kokari yayi ya bude ido yana tinanin ina ne nan,chan kuma sai ya tino yarinyar da yake bi a mota,kalle kalle ya dingayi ta ina ze hangota,ganin ya farka dad yayi maza ya kira doctors,taruwa sukayi a kansa daga su dad har doctors din,binsu da kallo daya bayan daya yayi,mamaki ya shigayi ganin mom da dad a tare dashi,a hankali cikin muryar marasa lafiya ya kallesu yace “dan Allah ku fadamin WACECE ITA?”…… Kasa gane me yake magana akai sukayi,sai kawai aka mishi allurar bacci,nan da nan ya koma bacci kuwa………

Khaleel binta yayi da kallo yana mamakin yanda ta shanye duka,wani farinciki na kara mamaye zuciyarsa,yau hakarsa zata cimma ruwa,dariya yake a zuciyarsa yana tinanin first night dinsu ze tabbata tin baa daura aure ba,ciki siyasa irin tasu ta yan duniya yace “wifey are you okay” ganin sai jujjuya kai take…… Gyada Kai kawai tayi alamar she’s fine,cije lebe yayi ya matso kusa da ita yace “toh ko zakije ki kwanta ki huta”…… Girgiza kai tayi sannan cikin muryarta data chanja tace “no need”……, Wani killer smile yayi jin yadda muryarta ya chanja sannan ya sunkuyo daidai fuskarta yana bin lips dinta da kallo,kokarin hade lips dinsu yayi sai yaga taja baya tana ware idanunta sosai akansa….. Saida yaji gabansa ya fadi ganin irin kallon da take masa,a da idan tana mishi irin wannan kallon sai ya diririce amma yanzu ko a jikinsa sanin cewa bata hayyacinta…… Sake yunkurin kissing dinta yayi ta kuma jan baya…… Kamar a mafarki yaji ta kwashe da wata muguwar dariya,ta kalli cikin idanuwanshi tace “Why do you have to drug me when I can willingly comply?”….. Shiru yayi yama rasa me zece jin furucinta

Fatimah zainab ko ita kadai tasan meke going a mind dinta,an dade baa mata abunda ya tabata ba from someone she atleast cherish,she’s so disappointed,of all people wai khaleel,wannan shine betrayal of the highest order,tinda tasha first cup tayi sensing wani abu,saboda koma wani kalan drug ne it adds sweetness to the yoghurt,tanan kuma tayi detecting something is wrong,domin ta tabbatar da hakan,yasa tashanye tass,tabbas this is one of her mission coming here,gashi khaleel is making it easy for her…….Katse tinaninta yayi bayan yayi summoning courage yace “ I never thought you can give it to me easily,pls forgive me wifey,I just can’t control myself tonight,Allah ne kadai yasan me nakeji akanki”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button