Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 93-94

Sponsored links

Baffa yace da kuwa bani da kamarki a duniya Allah ya Miki Albarka bana so ma ta fito ta hanyar da ba daidai ba Indai Allah yayi za’a saketa ne again Kinga dama kuskurena nake so na gyara,cikin magana kasa kasa nace an gama Inshaallah zata dawo muyi ta Addua Kuma zan tsaya maka iyakar iyawata Baffa ai Kai namu ne tun a baya,Baffa Yace daina tuna min na tuba wlh, Nawwar ne ya sakko daga sama ya iske mu Ina zaune Baffa ma Yana kujera a zaune Muna ta hira, yaji dadi a ransa sosai ya rasa alakarmu da Baffa da muke hira sosai, Yana zuwa na mike na kawo Baffa kayan ci da sha,Kuma ya zage yaci ya koshi,Nawwar sai mamamaki yake Suka gaisa da Baffa,yace yau ziyara na kawo muku,shi dai Nawwar yasan ko Sabreen bai taba zuwa gidan ba sai Rabiah da baya son auren.

Haka shima ya zauna Muka dinga ta hira,ya Dade a gidan sannan ya tafi,Yana tafiya Auta Nawaf yazo tsabar tsaurin Ido na yaron nan mota ya dakko ba a sani ba da kyar yake kallon gabansa haka yazo har gidanmu na fito zanje part din su Star na ganshi harda jakar kayansa, Nawwar ya fito zai fito shima ya ganshi yace Kai motar ubanwa ka dakko motar Baffa fa yaushe ma ka iya ganin gabanka? Auta yace Yaya Ina kallon gabana Mana idan naje fitsari,dariya ta kamani Nawwar harda min dakuwa ya min ambola Yana dariya,Jakar Auta na karba nace wata daya zanyi Aunty,Nace oyoyo muje ciki muka koma na Kai Masa jakarsa part din Sabreen data bari ya Sha gyara,yana zuwa harda cire agogo ya ajiye a saman gado yace kawo min shinkafa ni idan banci shinkafa ba bana Jin dadin duniya,kawo Masa nayi da ruwa da lemo wai yace ki kawo min fresh milk nace wannan Kuma baka Isa ba sai dai kaje da kanka,Zan fita yace Ina kawayenki ne Aunty? nace ai suna gidan nan an basu part guda amma wasu duk sun mutu na bawa Auta labari yace Allah sarki Allah yaji kansu fatan dai ba wannan Wise din ni kin San ita nake so,Kai Amma da tsaurin Ido kake Nawaf tafi karfinka ai nawa kake,yace wallahi da za a aura min ita Zan iya Zama Kuma na riketa tsaf nifa a SS2 nake fa ai na Isa aure,to girman aji ne aure,ke dai ba ruwanki ki hadani da ita, nace Indai itace gata gaka ba ruwana idan ka Sha mari.

Part din su Wise na Shiga Ina dariya na basu labarin Nawaf,Wise tace kaji shegen yaro sai dai ubansa,nace ke karki zagar min uba wallahi uban miji uba ne,to Allah ya baki hakuri Mrs Nawwar nace Ameen Ina masifa,Wise tace wannan Ina zai iya dani, Wai ba yaron nan da yazo da biki ba? Nace ae Suka Yi dariya Sera tace karki kawo shi wallahi yaro haka Kawai a koya Masa fitsara nace hauka nake Nawwar yace mun lalata Masa kani domin bakin nan naku da babu sakata,shi kuwa Auta Yana Gama cin abinci sai ganinsa mukayi a part din ya shigo yayi sallama yana wani iyayi,su Star sai kunshe dariya suke,Wise tace Dana yau kazo,Auta yaji haushi yace a ransa wannan ta Isa ta haifi kamata ita din wa,a fili kuwa ya basar ya zauna a gefe,Santana ya fita baya gida ya tafi kasuwa Wai girki zai musu a part dinsu na musamman su Star duk zaman da suke kenan su ci girkin Santana ya kware da girki.

Wise tace Nawaf Naga kana hamma,yace bacci nake ji Yana ta kallonta ta dakko zanin Atamfa tare da furta zo dan ubanka na goyaka na jijjiga ai Kai a wajenmu jariri ne,Nawaf harda harara ance za a goya shi da zani ana maida shi yaro tashi yayi ya fice ya tafi kallon ball wai yayi fushi,Mandula tace yau Naga balagaggen yaro,wlh Yana Isa aure suyi Masa Kar ya lalace cewar Seraline.

Dagaci kullum ramewa yake Yana tumburewa sai dan ciki kwajaja a gaba wuya Kamar Sandar kiwo,Gwaggo ma duk sun rasa sukuni,suna haka manyan garin kowa yaji asirin Dagaci ya tonu an gama gane gaskiya yanzu,su Star da shigigi har kotu Suka je a kano,ni naji suna yawan tafiya kano ashe Kara suka shigar akan abinda Dagaci yayi min ni Rabiah,aka Nemo hukumar gidan reno da su ake zuwa kotu har garin Suka je Suka ji gaskiyar labari abinda ya faru da yarsu nan da nan aka fara kawo labarin karar a gidajen Radio,sakayya ni ban San me akeyi ba sai ji nayi kotu na nemana a Kano lokacin Suka bani labarin komai suna cewa wlh baza su kyale ba, da Nawwar Muka je sai da Muka halacci kotu sau biyu sannan aka samu sarki da Kansa yasa aka tugewa Dagaci rawani aka sauke shi daga sarautarsa tare da cinsa tara ta kudade masu yawan gaske,Haka ya siyar da gonakinsa kusan gaba daya gonarsa ta gado ce kawai ta rage, ya bani kudi ni Kuma ba mutunci na karbe na Kai tallafi gidan marayu gaba daya kudin, Dagaci harda cewa Rabi babu tausayi? Ki tausaya min,nace Ni Sanda kuka min mugunta tun Ina yarinya Kun tausaya min ne,abinda Zan iya muku Kawai yafiya ce amma ni bani da hadi da ku bani ba ku kuje Kuma abinda kuka min kanku kuka yiwa,gashi ban fasa ci gaba ba na juya Muka tafi ,Gwaggo tayi tsumu tsumu itama, da kotu cewa Suka yi za a kaita prison nice na nemar musu Alfarma aka kyale su a haka

Dagaci fa duniyar ta Masa zafi Aunty Amarya Kuma sun daura gaba da Gwaggo kullum basa zaman lafiya,Dagaci ya Gaji ya saki Aunty Amarya, da Gaji da Gwaggo Suka nada Mata dukan tsiya ta fito zata tafi Suka bita da duka ko kunya basa ji har gefen babban titi suna kokawa mota tazo wacce birkinta yaki tsayawa Kawai ta banke su gaba daya har Gaji.

Mutane Suka cika wajen aka kwashe su zuwa asibiti,Dagaci ya tafi asibitin Yana kuka abubuwa sun Masa yawa Yana zuwa ya samu Aunty Amarya tayi karaya wajen biyar itama Gwaggo karaya ta Kai hudu,Gaji Kuwa Allah yasa motar kadan ta shafeta bata karye ba.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button