Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 18-19

Sponsored links

Maheerah kwafa ta ja ta manta ta kori Ayusha ta kwanta baccinta ta barshi a kasa saman Sallaya, sai 11am ya tasheta yana fada Mata yunwa nake ji ya kamata ki sama min wani Abu naci tunda kin kori mai aikin naki,ko kulashi bata Yi ba Wai bacci take yi bayan tana jinsa, a hankali da lalube ya samu ya fito Palo tare da Zama a kujera,lokacin Cele ta gama girkinta tsaf ta fito ta ganshi yana hamma,tace karka cinye ni da hamma haka yunwa yake ji ne,tarkacenta ta kawo gabansa ta rike hannunsa tace Cele Rufaida,Murmushi yayi tace Sabahul khair,Kai ya jinjina Mata kawai, tea dinta data hada tasa spoon ta rike hannunsa tare da dawo da shi kasa ya zauna saman carpet yanda Suka saba cin abincinsu, Shayin ta ebo a Spoon sai da ya huce ta Kai bakinsa yaji spoon a saman lips dinsa bakinsa ya bude ta zuba Masa ya shanye,Ahsan a ransa yace Anya Kuwa bazan Yi Mata biyu ba,ai Mata biyu sunyi a rayuwa idan wannan ta Bata maka sai wannan ta faranta maka Allah yayi gaskiya mu larabawa da kudin ma Sai dai mutum ya Kara aure a boye bayan ga abinda Allah da manzo Suka ce,Rufaida ta Zama Masa Kamar matarsa sai kace kishiyar Maheerah,a ransa yace gata da tsafta ga tausayi da Imani,nan take ya maida sunan Cele Iman wai tana da Imani, Cele Kuwa tana bashi shayi ga chips da kwai sai da yaci da yawa sannan ya nuna Mata ya koshi, Cele dai harda Dan zuba ruwa kadan a hannunta tare da gogewa Ahsan baki yanda akewa Yara a Nigeria sabo da ko da bakinsu ya baci,Tissue ta sa ta sake goge masa bakinsa Yana ta dariya marar sauti,Cele tana kallonsa tace kaga idan kana gani kayi magana wannan Ido tangararan ace bawa baya gani da su gwara ka sa glass dinka ai sai ka hanani sukuni na zaci kana gani haba Ido fess haka Anya ba salon Iskanci bane wannan amma bari zan kureka sai dakko Allura nazo Zan tsira a idon Indai kana gani ai Zan gane shu’umin bawa.

Hannunsa ta kamo ta Dora a cikinta tace cikina kaji sai tauri yake na shiga uku ni kam,Cele ganin Wai baya gani ta taba boobs dinta tace gaskiya Ina Jin Dadi a gidan nan sai wata uwar kiba nake ji kirjina haka tabashasha dariya tayi tace an cuceka bakwa Jin hausa wlh kalmomi iri iri na iya shege bakwa ji.

Maheerah ta leko taga Sanda Cele take bawa Ahsan abinci kishi kamar tayi ihu,Fitowa tayi Kawai ta shiga dakin cele ta kwaso Mata kayanta kaf tace gashi nan ta dauka ta bar musu gida ciki basa so,Cele ta gane nufinta duk da bata Jin me take cewa,Murmushi Cele tayi tace wallahi Zama daram ba inda zani in tafi inje Ina ai Naga gidan zama inci me kyau Insha me kyau a Sadaka ba tare da na Zama takari ba Zama daram,Maheerah ta nunawa duwawu ta zauna tace Zama dole,Ahsan ne ya musu magana yace su daina fada,Cele ba jinsa take ba sai Maheerah da ta dage tana masifa na gaji kana kallo ai wannan bakuwar tana taba ka yanda taga dama ko Haram baza kace ba dama kana so ta taba maka jiki to sai ta bar gidan Nan,yace sau nawa kike ji Ina ce Mata Haram Haram ba inda zata je wannan ai zulunci ne an sa Mata ciki kuma a koreta to gida nawa ne ba inda zata je ko ta haihu sai ta zabi tafiya ko Zama amma tana gidan Nan,Maheerah tace baza ta zauna min a gida ba tana masifa Ahsan ya farara laluben Maheerah Wai zai mareta tana Raina Masa hankali,Cele ce ta jawo Masa ita ta karfi ta danno fuskarta jikinsa Wai gata ya daketa, Dan Marin ma wani tas kadan ko yaro bazai ma wannan lalataccen Marin na Ahsan ba,amma Maheerah sai kuka tana yarfe hannu ta shiga uku yau miji ya mareta shima Ahsan a Dole Namiji yayi bajinta,Cele taja Tsaki tace Kai dai ko wani Salahu wani Sahanunu da kai wannan Zama a gidanku akwai takaici Yar iskar yarinya tana ma Iskanci ka kasa komai,Kan Maheerah ta juya tace Yi Mana shuru shegen hakora Kamar katangar kwalabe, Dan iskan hakora Kamar kwano yaji lamba dakinta ta wuce tace irn wannan bakin ciki a gidan Ahsan ai ya baci wannan ba karamin dakikin balarabe bane haba.

Mami tana gama Idda Auta yaje har dakin Baffa,ya shiga ya gaida shi,Baffa Yana shan lemo a zaune Yana tunanin duniya yace Autan Mami ya akayi ne Naga kana ta smiling yace Albishir Zan baka Baffa amma sai ka bani goro,yace me kake so za a baka idan fa me Dadi ne Albishir din,yace deal zamuyi Zan fada maka amma nima idan na Shiga University zaka Yi min aure,Baffa ya bude Baki yace aure kuma wace matar? yace me rabo ce dariya Baffa yayi ya dauka Wasa yake,Auta yace satin Mami biyu da aure aka saketa fa ta dawo gidan Yaya Nawwar a can tayi Idda yau ta fita,Baffa Yana daga zaune bai san sanda ya mike tsaye ba,yace yanzu Auta tana gidan Nawwar? Ina gaya maka kuma tayi Idda ma ka yarda dani mana,wow Alhmdllh amma naji dadi yanzu ta ya Zan Mata magana ta yafe min ta dawo gidana, Simple cewar Auta abu me sauki idan zaka cika min Alkawari na to Zan wuce maka gaba,Baffa yace Auta manya to Zan cika maka yace to karka je yanzu Baffa ni nasan ya zanyi in lokaci yazo zance kaje,Auta to Ina so na ganta,to ai kaji Kuma Baffa zaka bata show kana da gaggawa,so kake ta ja ma aji ta rainaka kayi zamanka Zan ma magana,Baffa yace to Auta na sanka ba Wasa yace sure ya fice Yana fita wajen Mami yazo,ya iske tana girki yace Mami tace naam ta juyo tace Auta sai taga Auta Yana hawaye shaaaa shaaa tace Kai lafiya,harda sheshekar karya yace a…ab..abin takaici…..Mami ta tsorata tace Wai mene? …hawayensa ya goge na karya yace ba komai ba sai ma na fada Miki ba tunda nasan baza ki damu ba ke,Mami tace bafa na son Iskanci idan zaka fada min ka fada min which kind madness be this,Auta yace wani satin za a daurawa Baffa aure,Ido Mami ta zaro ta tsaya kamar gunki tace aure Kuma tsofai tsofai da shi sabo da budurwar zuciya,Auta yace Kuma budurwa ce zata Kai sa’ar Aunty Rabi baki ganta ba Wai abokinsa ne ya bashi ya aura.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button