Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 109

Sponsored links

Har gaban hall din da zasuyi exam ya rakata, saida yaga tashiga sannan ya koma inda yayi parking nan kusa da hall din yana binta da addu’ar samun nasara, shiga mota yayi ya hau danne danne a waya yana jiran fitowarta.

Sai karfe tara ya shigo school din kamar yanda ya tsara sai sun fara exam din sannan ze shigo…. Direct hall din da suke exam ya nufa dan saida yasa aka turo masa duka venues din exam dinsu……..

Tun kafin ya karasa ya hango invigilators din idonsu kur a guri daya ko zagayawa basayi kamar yanda ya kamata ace sunayi…. Ko kula da shigowarsa basuyi ba tsabar yanda suka bawa guri daya mahimmanci da kallo, kallon inda suke kallo yayi nan yayi tozali da ita looking as beautiful as ever, take ransa ya baci yaji kamar ya shake duka masu kallonta, wato da gangan suka sata a gaba saboda su kare mata kallo gasu yan iska ko? Amma bega laifinsu ba tana sane taki sa hijabi dan su kalleta, bama hijabi ba har niqab yaci ace tasa….

“Get up!”….

Taji an daka mata wani mugun tsawa…..

Kin tashi tayi kuma bata dago ba, bata gansa ba amma zuciyarta tagama tabbatar da shine, tayaya zata kasa gane masifaffiyar muryarnan?”……

Kawai ji tayi ana yaga abu, da sauri ta dago ta ganshi yana yaga booklet dinta kamar wacce aka kama da examination malpractice, kasa motsi tayi tsabar shock din data shiga, an dade baa mata abinda ya mata ciwo irin wannan ba, take taji wani tsanarsa ya ninku a ranta……

Sai kuma taji ya kamo hannunta yana janta, kokarin fizge hannunta tayi amma ta kasa, janta ya cigaba dayi harya fita da ita daga class din ta daya kofar, a take hall din ya hargitse da hayaniya kamar ba exam akeyi ba kowa sai mamakin metayi yake…….

Be saketa ba har saida ya sadata da office dinsa sannan ya wurgata kan couch ya koma ya rufe kofa ya dawo ya zauna yana kallonta……

Sosai ta galabaita dama batajin karfin jikinta kwanannan gashi kamar wacce akayiwa baki takasa zuwa asibiti…….

Daurewa tayi ta mike tana haderai ta nufi kofa da niyar ta bude ta gudu, da sauri ya taso ransa na kara baci da taurin kanta gashi zuciyarsa a kusa take dama dan idan ya fara irin wannan fushin sai yafi sati a haka…….

Hannunsa yayi maza ya daura akan nata datake kokarin murda mukullin….

Hannunta tasa tana kokarin zare nasa dake wuyarta at the same time fighting for her breath dan ji take kamar numfashinta ze dauke…….

 

“Tell me who the hell are you or I kill you here! Nace WACECE KE?!”…

 

Kakarin amai ta farayi amma yaki sakinta, saida yaga kamar numfashinta na janyewa sannan ya zare hannunsa daga wuyanta da sauri still yana manne da ita a bakin kofar, yana sakinta ta sulale a kasa, haka shima ya bita suka zube kasa tare yana tareta akan cinyarsa…….

 

Hannun yasa a hancinta yaji bata numfashi, da sauri ya dagota yana jijjigata, sai a lokacin yayi realizing stupidity din dayayi, just like she said he’s indeed stupid, meya kaishi shaketa, ya akayi ya kasa controlling kansa? Yanzu idan da mutu ya zeyi da ransa?….

 

“Dan Allah karki mutu, in kika mutu nima binki zanyi, Forgive me please, ki taimakeni ki tashi, I can’t live without you!!”…….

 

Yayita sambatu da karfi yanajin kamar ya fashe da kuka, tinda yake be taba feeling remorseful akan abinda yayiwa wani irin haka ba, sosai yake nadama da danasani akan abinda ya aikata, da ze iya dawoda hannun agogo baya da tabbas ya goge wannan abun daya faru, addu’a kawai yake kar wani abu yasameta if not he’ll never forgive himself…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button