Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 36

Sponsored links

“I am getting resistance to codeine, sai nasha dayawa yake min abinda nakeso, how do you see if I try alcohol?”…….

“A’a karki sha giya dan Allah, gwara codeine din, let me go get it for you”……

“Ok, ka siyomin dayawa”……

“Your wish is my command love”…..

Karfe bakwai na safe suka iso house kamar yanda daddy yace su hadu achan…..

Su biyar suka tarar dasu zaune parlour, bayan daddy akwai alhaji habibu sai sauran mutanen…..

Gaisawa sukayi sannan ogansu ya fara bayani;

“Alhaji gsky duk inda kace muje munje bamuga yaronnan ba”……

“Bangane ba? Khaleel din da muka rabu dashi jiya, sannan me gadi ya tabbatarmin da be fita ba tin jiya sai yau da asuba, be isa ace yabar garinnan ba”….

“Alhaji kasan dai iya aikinmu ko? Saidai in mutum baya garinnan amma babu inda bazamu nemoshi ba, toh mun dubashi a ko ina bamu ganshi ba!”……….

“This is impossible! Dole ku nemo khaleel duk inda yake dan shima barazana ne a garemu yanzu, na baku nan da kwana uku a nemoshi ko ina yake a fadin kasarnan, sannan zan zuba ido ta gurina idan ya dawo gida”…….

“Karkaji komai alhaji, kasa a ranka anyi kidnapping khaleel angama!”……..

Tinda yashiga ciki ya rasa abinda ke masa dadi, yariga yayiwa kansa alkawari ya fita sabgarta gabadaya amma daze ga khaleel yanzu sai ya masa jina jina, idansa ne ya sauka akan wayarta daya dauka wani lokaci data sume masa, dauka yayi ya shiga gallery ko Allah zesa yaga hotonta, deep down bayasan sake ganinta, a hakan kuma yanajin ganin hotonta zesa yaji sanyi a ransa, saidai me? Yana shiga yaga pictures din khaleel birjik babu nata ko guda daya kai ka dauka wayar khaleel dinne, buga i14 pro max din yayi a jikin bango ta fashe tass, dukda haka beji sanyi a ransa ba ya cigaba da tattakawa a kasa, wata zuciyar ce ta shiga zugashi akan yanzu fa suna tare da khaleel, kilama tana kwance a jikinshi yanda ta kware akan seducing din mutane, kila shi kuma yana chan yana kissing lips dinta……

Ya fada da karfi yanajin zuciyarsa kamar zata fado daya tina khaleel zeji abinda yaji shima, what if sunje an daura musu auren da gaske kamar yanda suka shirya? Mere thought dinnan ya sasa fara fasa duk abinda ya samu a dakin, dama ya saba indai yana fushi saiya fasa wani abu yakejin dadi shiyasa lokacin daya batawa fatima zainab rai yace ze kaita biggest mansion dinshi tayi fashe fashen da taga dama tinda irinsa ce……..

Knocking din daya faraji a parlor ne ya sashi dan dawowa hayyacinsa, sai kuma ya cigaba da sanbatu yana fadin “bazeyiwu ba! Bazeyiwu ba, wallahi bazaka aureta ba!”……

Chan kuma sai yaji knocking din ya kara karfi, cikin fitar hayyaci yaje ya bude, Umm ya gani tsaye a bakin kofa Allah ya taimakeshi iya daki yayi fashe fashe…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button