Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 12

Sponsored links

Ta bata doguwar riga sleeping dress mai short hand marar kauri ta Sanya a jikinta bayan pant babu komai a jikin ta sai wannan longer shirt, zama tayi kusa da mommy wacce ta d’auko magunguna tana ‘ko’karin bud’e mata su ta bata lokaci guda ta Kora su, daga baya Mom ta d’auko Allura tana ‘ko’karin yi mata, tabb d’in Ayush taga makiyarta wato Allura da gudun gaske ta nufi toilet ta danna sakata tana fad’in “wallahi baza’a mun Allura ba, Dan Allah Aunty kiyi hakuri ki ban ko wani irin magani amma banda Allura”

Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah kwashewa da dariya tayi tana fad’in “Ayush da girman ki kike tsoron Allura? Nake ga Allurar zaifi miki amfani cikin gaggawa KO!”

Ba yanda mommy bata yi da Ayush ba akan ta fito amma furr Ayush ta’ki Allura sai hakura tayi tace “toh shikenam ganan Abinci kizo kici tinda kin’ki Allura”

Momy cikin fushi tabar d’akin ba wai saboda Ayush ta’ki Allura bane, tana so taje ta samu Junaid ne akan Abunda yayiwa Ayush, Sam bai kyauta mata ba,

 

Bayan fitar Mommy daga cikin d’akin Ayush ce ta bud’e ‘kofar toilet a hankali ta lalla6o ta d’auki Alluran da mommy ta ajiye saman table tasa a cikin boxes ta rufe, sannan ta d’auki flask din abincin ta zuba a plate paten doya ne da wake, sai ta tsiyayi ruwan tea a cup tana ci tana Kora tea, daman ba ‘karamin yunwa take ji ba, tinda ta shugo gidan nan take had’uwa da ‘kaddarorinta bata samu tasa komai a cikita ba, Ayush fah ansamu eating kamar ba gobe, tana ci tana yarfa hannaye tsabar zogin da Nononta yake yi mata kawai dai jurewa take…..

Mommy

Kamar zata dungura haka take hawa upstair nan tana zuwa ta bangaje ‘kofar d’akin tana shirin yin masifa, abunda ta gani ne yasa ta tsaya cakk ta zaro ido waje bakinta na kakkarwa take fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, JUNAIDDD”

wani irin gigitaccen ihu tayi ta fad’i ‘kasi sumammiya….

 

Ikon Allah mai Mommy ta gani haka???

 

Duk yanda akayi taga abunda yafi ‘karfin tunaninta ne!.

*TO* *BE* *CONTINUE* *INSHA* *ALLAH*

Mommy fad’uwa tayi sumammiya ganin halin da Junaid ya shiga, tinda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin wannan al’ajabin ba sai yau akan d’anta wanda ta haifa.

Junaid ne a manne da jikin gini an d’aga shi sama yayi cross kamar yanda akayiwa Jesus Christ, jikinsa yayi jawur sai tabo-tabon ‘kunar wuta ga shatar bulala ajikinsa duk ya faffashe babu kaya a jikinsa sai jageren wando wanda baije gwiwarsa ba, kansa a sunkuye wuya ya karye kamar wani matacce ko numfashi bayayi, sai gumin da yake gangaro mishi daga cikin sumar kansa,

Abunda ya faru da shi shine 👉. Naushin AYUSH da yayi a rashin sani shi ya jawo masa wannan bala’i, domin Naushin ba iya ita kad’ai taji ciwo ba hatta mahaifinta sarkin matsafan duniya sai daya jijjiga da wannan naushin! hakan yasa ya turo mutanensa wato Manya-manyan Aljanu guda uku don su hukunta shi,

Allah sarki bawan Allah yana cikin baccinsa yaji sau’kar bulalar kaca wacce aka cirota daga cikin wutar su na tsafi, duka d’aya fatar jikinsa ya fashe a razane ya tashi yana waiwaye amma baiga kowa ba su kuma suna tsaye a kansa, cikin fushi babban aljanin cikinsu ya yi wurgi da shi sai da kansa ya bugi jikin gini, kafin ya Ankara an sake d’agashi sama aka buga shi a ‘kasan tiles, haka suka cigaba da buga shi da ‘kasa tsabar wahala ko kuka ya gagara yi balle ihu, har sai dayayi jina-jina suka d’aga shi kamar tsumma ko motsi bayayi sai numfashi sama-sama, suka d’aure hannunsa d’aya da kacar wuta haka d’ayan hannun, wannan aljanin ya ri’ke hannun dama shima wannan ya ri’ke na 6angaren hagun sawayensa suka had’a biyu suka d’aure guri d’aya, suka manne shi a jikin gini.

Cikon na ukun kuma bulala ya fara zabga masa shi kuwa hatsabibin uba wato Ayush father watsa masa garwashi ya Fara yi ajiki ta cikin madubin tsafi, ana jibgarsa kuma ana watso masa garwashi, haka jikinsa ya koma ba dad’in gani jiki duk ya farfashe suna cikin gana masa wannan azabar wuyansa ya karye ba alamar motsi, shi Ogan yasan bai mutu ba doguwar suma yayi domin tsafin Damusar su bazai bari ya mutu ba sai dai yasha iya wahalarsa.

(Innalillahi wannan ai gwara mutuwarsa).

Haka *BOKA* *ZALIMU* ya bada umarni a cigaba da hukunta shi har na tsawon kwana uku 👌

Farin Bafulatani mai Ba’kar Zuciya, Sarkin Matsafan Duniya (Boka Zalimun) Baban AYUSHH

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button