Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 108

Sponsored links

Dad daya keta zazzaga masa masifa tun bayan sun hadu a parking space har suka shigo parlournsa ya tamabaya…..

“Nace naji!”….

“Kace kaji kamar wani sa’anka? Rashin da’ar da aka sake koya maka kenan achan? Wani kalan irresponsible man kakeson maida kanka ne? Toh a yau basai gobe ba ka tabbatar kaje kun daidaita da Hamida!”……

“I’m not ready for marriage!”…..

“Na gaji da jin wannan zancen banzan! Whether you’re ready or not aure saika yishi very soon! Sannan banaso kafarka ta kara takawa abuja, don’t try me!”……

“Naji”…..

“Karma kaji! Daidai nake dakai, now out!!!”…..

Tashi yayi ya fita yanajin kamar duka damuwar duniya akansa aka tara, Fisabilillahi mezeyi da wata Hamida? Aiko a kafa aka daura masa ita sai ya kwance kuma yafi karfin yaje gidansu su wani daidaita, ai saita raina shi ma….

“Keep dreaming ba inda zanje wallahi!”….

Ya fada kamar Dad na gurin……

Ko zama beyiba bayan ya shiga part dinshi yaji anturo kofar tare dayin sallama…..

Dagowa yayi ya kalleta yana kara daure fuska kamar itace ta gama masa masifa……

Mikewa yayi ya shiga ciki yana jinjina wautarta, shi be taba sanin rashin wayenta yakai har haka ba, me take tinanin tayi masa da kai tsaye zatace masa dole saiya auri wata hameeda, yana sane yayi playing along don kawai ya gane abinda yake san ganewa, and alhamdulillah ya gane kuma saiya nuna mata bata da wayo…..

“Ko ina take yanzu?”…..

Ya tambayi kansa jin tinaninta kawai is making him feel reckless, zeso ya koma abuja yanzu kodan ya nemeta amma yasan kome zeyi baze iya fita daga gidan ba yanzu dan idon dad nakan duk wani motsinsa, gwara ma ya bari da asuba idan ya fita sallah daganan ya kara gaba……

Wani dan murmushi yayi tunowa da gobe zaa fara exam a school dinsu so probably yasan dole zatabar duk inda take taje tayi exam, sannan kuma course din dayayi lecturing dinsu ne he needs to be there….. A take yayi booking flight na karfe shidan safe…..

Sanye take cikin lilac lifaya me ratsin pusher pink, sosai take san lifaya dan tanajin dadin sasu dukda yanda takeshan kallo idan tasusu dan ba karamin kyau suke mata ba da kuma fitar da shape dinta me daukan hankali…

Khaleel da tun dazu ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi ya cigaba da kallonta be kulata ba, ana ganin sonda yake mata yayi yawa amma waye baze haukace akan wannan flawless creature din ba?….

“I have seen beauty but this is a discovery? I need to see your mom, dan Allah a gurinwa kika kwaso wannan kyan?”…….

“Hand me the key bansan shirme”……

“I’m sorry you’ve got me hooked with your beauty!”…

Ya fada yana bude mata motar, shiga tayi shikuma ya zagaya driver seat har lokacin be dena santinta ba……

Har gaban hall din da zasuyi exam ya rakata, saida yaga tashiga sannan ya koma inda yayi parking nan kusa da hall din yana binta da addu’ar samun nasara, shiga mota yayi ya hau danne danne a waya yana jiran fitowarta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button