Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 13

Sponsored links

“Rabu da maganar Lami bata da amfani Allah dai ya ganar da Hadiza kawai”

Daga haka taja bakinta tai shuru bata bawa Anty ƙofar taba da haka zata ja gulmar Ummah ai tayi da matan gida.

Har la’asar suna gidan anan suka ci abinci ban da mama da take azumin alhamis.

Haka har ranar suna tazo ƴan uwan Amatullah basu yanke ba umma tai mitar zuwan nasu amman Amatullah tace mata arziƙine kuma tun daga wannan Dubarar shan tea da mama ta nuna mata shikenan ruwan Nono ya kawo yarinya ta sami abinci.

Anyi suna lafiya Yarinya taci Sunan Ummah Khadijatul Iman amman Iman ɗin za’a ke ce mata.

Kuma har lokacin Babu wani daga cikin ahalin imran daya zo gidan Amatullah bata sami fuskar tuhumar shiba a daddafe umma tai zuwan sati bayan suna.

Daga nan kuma Amatullah ta koma cigaba da kula da yarinyarta.

Lokacin datai kwanaki ashirin agidan Imran ya soma Tsiro mata da wasu halaiya na daban Son kusantarta acikin Jinin Biƙi ji wani jahilci ƙin amincewar da tayi shine ya tsiri hanata abinci tare da Kulleta a ɗaki tun safe har sai ya dawo zai Buɗeta………

_EKEJA BARRACK LAGOS STATE_………..

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.

Juyi kawai yake a saman kujera hannun shi riƙe da wayar shi yana duba posting Ɗin da aka turo mishi yanzu na zuwa Kano wanda zai ɗauki watanni kusan uku acan, Shine zai jagoranci rindunar sojoji ta farko da zasu shiga wasu daga cikin ƙauyukan Kano

waɗanda ake tunanin wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suna haurawa cikin dare suna kwashe musu dabbobin su tare da ƙona musu Gidajen su wannan tasa Aka buƙaci sojoji kusan Rinduna Biyar don ta shiga ƙauyukan ta bawa mutanan dake ciki kariya

Duba Map ɗin ƙauyukan ya shiga yi wanda suke Cikin Ɓangareron Kano maso kabashin Gudu Batare da wata shakka ba ya tura shaidar Gani tare da aje wayar tashi yana Cike wata takarda dake gaban shi.

Tura Ƙofar Office ɗin nashi akai tare dayin sallama Abokin Aikin shi Captain Khalil ne ya shigo sanye Cikin kakin su na soja Miƙa masa hannu yayi suka gaisa sannan ya nuna masa Kujerar dake kallon Shi.

“Khalil yanzu nake ganin Wani posting letter ko kai ma ka gani?”

Captain Khalil yaja tsaki tare da cewa.

“Kai dai Bari Makama nagama Shirin tafiya zamfara kasan Gida ce amman Mutanan nan suka sauya mana rinduna”

Murmushi Ahmad yayi tare da cewa.

“Au kaifa gida aka tura ka ko? to ka sani Ko kanon ce alheri gare mu?”

Khalil bai yi magana ba ya janyo wayar shi yana nunawa Ahmad cikin ta.

“Kaga nan zamu sauka a Bakabo barrack fa na can janguza wannan posting sam bai min daɗi ba wallahi”

Ahmad yace.

 

“Na gani mana Allah ya zartar mana da alheri haka kwanakin Baya Nai shirin katsina naga an mayar dani Barno haka na tafi kasan a rundunar mu ni kaɗai nayi rai”

Haka suka ɗan tattauna akan tafiyar tasu wadda Shida Abokin aikin sa Khalil sune zasu jagoranci Rindunar sojojin ɓangaren su, sauran tawagar ukun daga wata tawagar ta daban take.

Bayan gama maganar tasu Khalil ya tashi ya koma office ɗinsa.

Bayan sallar azahar suka soma training da tawagarsu sai wajan yamma ya koma gidan shi duk ya gaji haka ya watsa ruwa ajikin shi ya kwanta agado yana mai jin wayar shi tana ringing!

Idanun shi a rufe ya ɗaga wayar yana sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.

“Tunda mukai magana rannan Shikenan ka share ni ka manta dani wato dani da Babu duka a ɗaya a rayuwar ka Ko Baby?”

Muryar Zee wadda take maganar cikin shagwaɓar da take masa a koda yaushe idan suna waya.

Ya janyo pillow ya matse a kirjinsa ya gaji Hutu yake buƙata amman yasan idan yace mata haka wata rigimar ce zata kuma tashi.

“Kiyi haƙuri zainab wallahi ayyuka ne suka sha kaina yanzu ma haka”…..

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button