Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 7 Complete Hausa Novel

Sponsored links

Security suna ganin hakan suka nufi ‘katon falon gidan daga nan suka haura up stair yanda zai Kai ka d’akin Junaid,

Samun Doc. Fatima sukayi tsugune a gaban Junaid tana ta rera kukanta, shi kuwa yana kwance ‘kasi bacci mai nauyi ya d’auke shi.

“Lafiya kuwa Hajiya? Kodai Tiger ne ya samu matsala”

Dake sunansa Tiger a wurinsu, Direct sun tabbatar da Tiger ne shi domin basu ta6a ganin ikon Allah nan ba, in ba a film ba.

Cikin sheshshekar kuka Doc. Tace “na mishi Allura babu wata matsala yanzu, you can go”

Suka amsa mata da “OK” sannan suka koma gurin tsayuwarsu.

Bayan ta gama kukanta ta rarumi wayanta tayi dialing call wata number

Lokaci guda ta Kara a kunnenta murya ‘kasa-‘kasa tace “please I wanna that girl to come my house right now”

Daga 6angaren d’ayan shima yayi magana,

Sai ji nayi ta kuma cewa “yeah! Her Name is Ayushmat, room 4.”

Lokaci guda aka bata amsa ta katse ‘kiran.

Mi’kewa tayi tabar room d’in

‘Dakinta ta mi’ka jikinta duk sun mutu ga wani matsanancin ciwon Kai dake damunta, toilet ta shiga ta watsa ruwa a kanta, ta fito jikinta d’aure da towel ko shafa mai bata tsaya tayiba ta zura doguwar riga marar nauyi mai hannun breziya, fad’awa tayi saman ‘katoton gadon ta bacci ne yayi awun gaba da ita.

A can asibiti kuwa murna Ayush ta shigayi za’a kawota gidan Doctor Fatima,

“Daman kuwa har na gaji da zaman asibitin” tana fad’in hakan tare da shigewa cikin motar da za’a d’auketa.

Cikin ‘kan’kanin lokaci suka iso gidan, horn sukayi mai gadi ya bud’ai musu daman already sunsan da zuwansu,

Mi’kewa motar tayi har sai data je gurin parking tukun,

Doctor Hasheem yayi mamakin ganin motar police a gidan amma sai dai ya kafse kawai baice komai ba.

Har cikin falo suka shiga amma basu tarar da kowa ba, sallama Doctor Hashim yayiwa Ayush sannan yayi tafiyarsa,

Ba komai ne yasa Doctor Hashim tafiya ba illa tsoron Junaid.

Guri Ayush ta samu ta zauna cikin d’aya daga cikin jerin kujerun falon,

Tana ta kallace kallace,

Flowers dake manne a jikin bangon d’akin ne yaja hankali ta zuwa gurin

Ba karamin burgeta flowers sukayi ba,

Ita kad’ai take sau murmushi a kan kyakykyawar fuskarta har sai da dimple d’inta ya lotsa.

 

Bata ankara ba taji wani irin gurnani ta bayanta irin na namun daji,

A tunanita a cikin television ne ake nuno namun daji,

Sai tada juya zata koma gurin mazauninta karaff ta had’a ido da Junaid tiger still yana wannan yanayin nasan

Idanunsa kuwa irin na asalin *TIGER*

ya tsaya cakk yana mata wani irin kallo kamar wanda ya samu nama.

Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ayush

Wani irin ‘Kara tayi mai toshe kunne a take ta sume a gurin yaraff ta fad’i ‘kasi.

 

Duk mutanen gidan naan ba wanda baiji ihun Ayush ba

Hatta Doc.Fatima da take bacci saida ta razana da wannan ihun……Ayush tana kwance saman gadon Doctor Fatima tin sumar nan datayi bata farfad’o ba,

Abin duniya yabi ya ishi Doc. Fatima itama tana zaune a bakin gadon da Ayush take, tana dafe da goshinta Kai a sunkuye, “Allah yasa dai ba wani abu yaron nan yayiwa yarinyar ba” tana maganar zuci

.“Dodo, wayyo Dodo zai kamani, gashi nan idonsa wani iri, wayyo Allah na, Ku fitar dashi daga cikin gidan nan banason ganinsa”. Ayush ce ta farfad’o tana wannan sambatun

 

“Lafiya kuwa Ayush meyake damunki ne haka kodai kina tunowa da mahaifiyar ki ne?”. Ta rirri’keta domin taga niyyar ta so take ta gudu tsabar tsoro.

 

Ayush tana maida numfashi sama-sama kamar wacce tayi gudu

“Wayyo Alhamdulillah, mafarki nayi ashe” ta juyo tana kallon Doc. Fatima gumi duk ya ji’ke mata KO Ina kamar wacce ta fito daga wanka, duk A.C dake d’akin amma ko kad’an bata jin wannan sanyin AC.

Doc. Fatima itama amsa ta bata cewa “e fa mafarki kikayi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki,

Yanzu dai tashi ki shiga toilet kiyi wanka sannan ki ci abinci saina kaiki d’akin da zaki zauna”

Mi’kewa Doc. Fatima tayi tare da nufan gurin da jerin kayanta suke tana fad’in “Bari na za6a miki kayan da zaki saka kafin gobe muje shopping”

Mi’kewa Ayush tayi ta tsaya cak, tana sa’ke- sa’ke a ranta!

Ji tayi ance go and enter mana.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button