Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 106

Sponsored links

“Allah yasa Jamila, muna fama da batan yarinya ga wani abu kuma, ni narasa tinanin da zanyi ma”….

 

“All is well Insha Allah, karki tada hankalinki, mushiga ciki musan abinyi”……..

 

Ba karamin shock fatima zainab tashiga ba ganin su eesha da har yasa ta kasa ture billy data wani rukunkumeta, tariga ta kudirta aranta kome zaayi nunawa zatayi batasan su ba, haka idan ta koma hostel nunawa zatayi ba ita suka gani ba, tana cikin wannan lissafi taji tsawar daya daka musu, ba shiri ta mike tsaye ta koma chan gefe, tana tsaye harya haura sama bayan su Umm sun fito, ganin hankalinsu baya kanta ya sata ficewa da sauri dama mayafinta na hannunta…….

 

Bata nufi ko ina ba sai kofar baya, idan da zaa tambayeta batasan ya akayi tasan da gate a baya ba kawai jitayi kamar ana janta ta fita daga gidan, tana zuwa kuma taga wani key a kasa, dauka tayi batada tabbacin key din gate dinne kuma batasan ya akayi yazo gurin ba, tana zirawa gate ya bude, luckily tana fita taga wani cab ta tsaidashi da sauri tashiga…..

 

Suna zaune a parlourn daddy har lokacin babu wanda ya motsa ko nan da chan, jira kawai suke suga zuwanta dan boss ya fadamusu su saurari zuwanta any moment, sai tattattaunawa suke akan yanda abun ze kasance da kuma wasu abubuwansu daban da suke shiryawa… Har malamin da ze daura auren sunzo dashi ita kawai suke jira tazo a daura auren a parlourn…..

Suna cikin wannan halin sukaji knocking, da sauri daddy ya tafi ya bude ko wannensu na addu’ar Allah yasa itace….. Ilai kuwa itace, murmushi yayi sosai yana mata sannu da zuwa, batace komai ba tabi bayansa suka shiga parlourn……

Guri daddy ya nuna mata ta zauna ya shiga tambayarta ina tashiga sunata jiranta……

“Ina school”….

Haka kawai taji batasan gayamasa daga inda take dukda yanda takejin bazata iya masa karya….

“Shikenan yanzu zabi wanda kikeso ya zama waliyinki anan”….

Kallonsu tashiga yi daya bayan daya har idonta ya sauka akan alhaji habibu, nunashi tayi akan shi takeso ya mata waliyyi……

Gyada kai mallamin yayi nan daurin aure yashiga gudana a cikin parlourn!!…….

Alhamdulillah Alhamdulillah Allah yasawa wannan aure albarka!…….

Daddy ya juyo muryar mallamin na fadin haka… Sai kuma ya farka firgit daga dan baccin daya kwashesa, ashe mafarki yake har lokacin baa gama daura auren ba, ajiyar zuciya yayi yana jin kamar ya janyo lokaci, burinsa kawai a daura auren a wuce gurin, chan sai yaji gabansa na faduwa kamar wanda yayi tsere, babu wanda ya kula da yanayin da yake ciki aka cigaba da hidindimun daurin aure……

Alhaji habibu na shirin bada shedar an basu ita a matsayinsa na waliyyinta sukaji karar kofa…..

Sai kuma baa shigo ba, tinani sukayi ko iska ne hakan yasa suka cigaba da harkokin gabansu

Alhaji habibu na shirin kara yin magana kenan sukaga an banko kofar parlourn da karfi……

Kallon juna suka shigayi kowannensu na tinanin waye dan meshi be shigoba har lokacin…….

“Dama baka rufe kofar ba dazun?”……..

“Wallahi na manta, ashe ban rufe ba, bari na duba naga waye sai mu cigaba”…….

Daddy ze mike kenan idonsa ya sauka cikin na khaleel da kallo daya zaka masa kasan har lokacin be dawo daidai ba…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button