Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 38

Sponsored links

At first nitsuwa yayi yanason tantance muryar waye but it gets to a point daya sake baki yana kallon system din……

Kamar yanda ta bukata haka khaleel ya siyo mata pack din codeine me dauke da 12 bottles a ciki, kamar wacce bata tabacin abinci ba haka ta bude kwalbar tanasha ta baka ta hanci, tass ta shanye kwalba daya ta sake bude wani ta kafa kai khaleel na zaune yayi tagumi yana kallonta kamar yayi kuka, ba abin ya hanata ba taji haushi, ko minti biyar baa kara ba bayan ta shanye kwalba biyu ta zube a kasa tana bacci, har ze dauketa ya kaita ciki ya fasa gudun karta tashi tace meyasa ya tabata, shida zasuyi aure very soon meye abun damuwa toh? He can wait ya tabata da hujja, murmushi yayi yana ayyana yanda zasuji dadin honeymoon a dubai…..

Yana zaune yana kallonta har bacci ya kwasheshi shima akan kujerar dayake dama a gajiye suke sosai….

Karfe sha biyun rana ta farka a gigice tana dafe da mararta, wani irin masifaffen ciwo taji mararta nayi mata itada bata taba ciwon mara ba sai gashi yau rana tsaka abu yazo mata, ko meyasa oho, biting lips dinta na kasa tayi jin yanda ciwon ke dada karuwa, har wani ji take kamar tayita birgima a kasa kota samu salama, a haka khaleel ya fito ya tarar da ita tana mutsu mutsu shi dama ya dade da tashi daga bacci, cikin tashin hankali yace;

“Wifey menene?”…..

Hannunshi ta kamo ta daura akan cikinta a raunane tace;

“Marata!”……..

Wani irin shock khaleel yaji dukda da hijab a jikinta amma ba karamin tasiri hakan ya masa ba, daurewa yayi ya janye hannunsa cikin muryar lallashi yace;

Shiru tayi dan bataso ya dauketa amma kuma tanajin kamar kafafuwanta bazasu iya tafiya ba, bawa kanta kwarin gwiwa tayi ta mike a daddafe, taimaka mata yayi suka nufi hanyar fita daga dakin…..

khaleel na rike da ita kamar wanda yake tsoron a kwace masa ita suka shigo asibitin, lokacin ta kara galabaita, hankalin khaleel in yayi dubu ya tashi sai sambatu yake besan meyake fada ba, shidai burinshi kawai kar wani abu yasa meta…….

A hankali yake tafiya shi kadai kamar yana tsoron taka kasa, kana ganin yanayin tafiyarsa kasan irin na yan koyo ne, for the past two weeks da sanda yake takawa kuma sai an rikeshi amma yau yace abarshi ya gwada tafiya shi kadai, cikin ikon Allah sai gashi yana tafiyar kuwa, ji yayi kamar an hankadasa saura kadan ya fadi Doctor din dake biye dashi yayi saurin tarosa, kallon khaleel daya bige mutumin batareda yasani ba Doctorn yayi da niyar yi masa magana mutumin ya hanashi yace ya rabu dashi kamar matarsa ce batada lafiya…….

Suna zuwa suka samu sukaga Doctor, a take akamata allura aka kara mata ruwa…….

Khaleel ne ya tambayi Doctor abinda ke kawo ciwon mara dan shi ya tsorata da yanda ta dingayi lokaci daya……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button