Hausa Novels Complete Documents

Yar Aikin Karuwai 6-7

Sponsored links

NAWWAR SULAIMAN RAJ shine cikakken sunansa asalin Shuwa ne,Sulaiman Raj iyayensu su biyar Suka haifa Sulaiman shine na farko sai kaninsa Yusuf Raj, Sunusi Raj,Fatima wacce ake Kira da Binta sai Autarsu Rukayya,Allah yasa suna da wadata irin ta da suna da arzikin dabbobi da noma,sun taso cikin gata amma basu Yi ilimin boko ba sai na addini Kawai,sun girma sun Kai shekaru 27 lokacin tuni an aurar da Binta da Rukayya suna auren masu kudin gaske Yan kasuwa a cikin garin maiduguri,mazan Kuma da girmansu Suka koyi karatun hausa da rubutu harda turanci suna dan iya karanta wani abin sabo da Business da sukeyi, gaba daya mazan Rana Daya aka daura musu aure irin na gata Kuma cikin family aka zabo musu matayensu Sulaiman aka hada shi aure da Yar uwarsu Salma Mami kenan wacce ke da yara biyar Nawwar shine na farko,Sultana,Nasira,Hamra sai Autansu Nawaf suna ce Masa Autan Mami, daga baya bayan Nawwar ya gama degree na farko sai ya karo Amaryarsa itama Yar dangi shuwa ce dukkansu jininsu daya Safarau suna ce Ummin Haidar, tana da Yara biyu Haidar dan 8yrs sai Ahmad 5yrs, Yusuf Papa kanin Baffa kuwa aka aura Masa Mariya Mama kenan Wanda yarsu daya tal Sabreen Allah kuma bai sa ya Kara aure ba har Suka manyanta sai Sunusi aka hadashi da matarsa Zuwaira wanda shi baiyi tsawon rai ba Allah ya masa rasuwa wanda matarsa ko haihuwa bata yi ba, daga Baffa sai Papa sai Kuma kannensu da suke gidan Aurensu Binta da Rukayya, gaba Daya sai kasuwanci yasa Sulaiman Baffa ya tattara da matarsa Suka koma can kudu garin Inyamurai da Zama Onitcha inda take bakin ruwa a Anambra state shekara daya matarsa Suka koma can kudu garin Inyamurai da Zama Onitcha inda take bakin ruwa a Anambra state shekara daya matarsa Salma ta haifo danta Najimiji katon gaske kyakyawa na nunawa sabo da su din jinin kyau ne,ranar suna yaro yaci suna Nawwar, Yusuf lokacin matarsa tana da tsohon ciki bayan watanni kadan ta haifo yarta mace zankadediya taci suna Sabreen, Bayan Mahaifinsu ya rasu, ganin haka Sulaiman ya dakko Mahaifiyarsu da suke Kira Iyamami ya dawo da ita gidansa nan Onitcha suna zaman su lafiya.

Nawwar kuwa tun Yana yaro Baffa ya koya Masa kasuwanci ya dorashi akan harkar sosai har ya tara dunbin dukiya da tarin kadarori.

 

Bayan an raba gadon Sunusi Wanda ya rasu papa gaba daya ya handame dukiya har ta Kannensa mata yace zai dinga juyawa,shi yasa dukiyar shi sai taki albarka wannan yasa ran Yusuf ya baci bakin ciki ya kamashi ya tura Yan Daba har gida Suka yiwa Baffa fashin milliyoyin kudi babu Wanda ya sani ya ci gaba da bushasharsa,Babarsu tayi bakin ciki amma bata San danta bane yayiwa dan Uwansa turen yan fashi ba,Yusuf sai kukan karya ya samu dukiya ya tattara duka yaci gaba da juyawa Yana samun kudi a ciki yake biyawa Sabreen kudin makaranta da komai nata bayan Baffa shi ke masa komai ,Iyamami bata San komai ba ganin danta Namiji Daya Yana da kudi na fitar hankali duk da Yusuf shima yana da nasa rufin asirinsa sai tafi tausayin Yusuf ya koma dan gwal a wajenta sai abinda yace,duk abinda yace shine dai dai part dinta guda a gidan,sai Yusuf shima Baffa a gidansa ya warewa dan Uwansa part guda shi da matarsa Mama,Arzikin dai baya ci gaba kullum sai karewa suke,ganin haka tun Sabreen tana primary ya hada milliyoyin kudi ya kaita Italy tare da matarsa Zuwaira Mama ya kaisu can Kan ta kula da Sabreen ta samu Ilimi me kyau zai dinga zuwa musu ziyara,bayan sun tafi shi Kuma Nawwar a nan kasar can maiduguri aka maida shi wajen Rukayya can yayi makarantar secondary sabo da ya samu tarbiyya da ilimin addini tunda arewa ba Kamar kudu ba.

Har Nawwar ya gama Secondary Sabreen tuni ma a Italy ta dora da degree lokacin Mama ta dawo Nigeria shi Kuma Yusuf ya siyar da wani katon gidan Baffa a Abuja million dari a ciki yake turawa Sabreen kudi na hauka Baffa bai sani ba sam,Sabreen kuwa bata da aiki sai shaye shaye makarantar ma da kyar take zuwa tana gidan Saurayinta Lorenzo sune shekewa.

 

A wajensa ta koyi shaye shaye,sai club sai wajen Lorenzo tana sonsa shi yasa ta bashi kanta yake lalata da ita.

 

Shi kuwa Nawwar da bai San komai ba akan Sabreen sai Allah ya dinga hada shi da turawa masu kudi Suka Fara aiki a kamfanunuwa daban daban ya Fara samun mahaukatan kudade na shigo da Kaya da fitarwa ta fannin jirgin ruwa,Yana gamawa ya dora da masters yana Kuma Harkar business Allah ya sa Masa albarka,abokinsa kwaya daya ne dan gidan wani Sanata,

,guy ne hadadde shima dan masu dashi shima a kudu suke da Zama tare sukayi Secondary Suka tafi Uk tare Kuma amma shi Khaleel bai dora da masters ba babansa ya sama Masa aiki a NNPC,ya dawo gida Nigeria ya auri matarsa Sufia.

 

 

 

 

Alhaji Yusuf sun San komai abinda yarsu ke aikatawa na shaye shaye da bin saurayinta da sauran abubuwa marasa kyau sai Alhaji Yusuf Wanda Nawwar suke Kira da Papa yaje wajen Iyamami tare da matarsa Zuwaira yace tunda kowa yasan Sabreen ta lalace Babu me iya auranta a haka Kawai a hadata aure da dan uwanta Nawwar nasan Nawwar bazai ki jininsa ba,abin yayiwa Kaka Iyamami dadi a ranta tace ka kawo shawara ai tunda ya kusa dawowa sai a fara Shirin aure,Nawwar shi kuwa sai da ya kafu ya Zama me kudi na kirki ya Blbude kamfanunuwansa a nan Nigeria can Onitcha da wasu state sannan ya dawo ba zato Mami da Baffa sai ganinsa suka yi babban abokinsa Khaleel ya dakko shi

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button