Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 32

Sponsored links

“Sun jiƙa mana aiki! Sun ɓata mana shiri! Ya ƙwace mana damarmu wadda sake samun samuwarta a garemu cikin sauƙi haka zata iya zame mana mai wahala!!”.

 

Kakkausar muryar Uwa mai matuƙar rashin daɗin saurare ta fara karaɗe ɗakin cikin amon sauti mai tashi sama. A firgice ta miƙe a zabure tare da zube gwuyawunta ƙasa jikinta na tsuma dan dama zaune take ido biyu tana jiran tsammani. “A gafarce ni uwa ba laifina bane, ni kaina ina cikin damuwar tangarɗar da aka samu”.

 

“Bana buƙatar jin komai daga gareki Taƙurya. Domin sakacinki ne ya jawo hakan. Nasha faɗa miki ki san suwa zaki bama aikin da ke bazaki iya yinsa kai tsaye ba. Su kuma waɗan can sakarkarun barinsu sukai wayewar gari tamkar rasa sauran damar data rage miki ne….”

 

Ɗan zabura tayi da nufin cewa wani abu, sai dai tamkar walƙiya Uwa ta ɓace a ɗakin. Hakan na nufin ranta a ɓace yake. Itama kanta ta dafe nata ran na suya da ƙara girmamar baƙin cikinta. Miyasa kowa bai bata matsala ba sai wannan ƴar shilar yarinyar da bata wuce sauron gidanta ba da feshi ɗaya take kawar da shi. Zuciyarta ta fara raya mata Uwa kodai tsoron yarinyar nan takeyi, yo inba tsoro ba taya zata dinga wani gewaye-gewaye bayan bai wuce da ƙyaftawar ido kawai ta shafe babin rayuwarta ba. Dama mutum na gagarar aljani ne banda ta fara maidata susu……

Duk wanda ya kwana ya tashi a masarauta a yau ya tashi ne da tashin hankalin da yafi na jiya sakamakon mawuyacin yanayin da Iffah ta wayi gari. Dole tun gabatowar sallar asuba aka maidata cikin clinic ɗin dake a masarautar saboda ɓallewar jini ta kowane sashe na jikinta. Da farko aman jini ta fara, sai kuma ta hancinta, sai gashi ta ido da kunne harda ma ramin cibiyarta. Hankalin Jasrah da Malikat dake tare da ita ya kai matuƙar ƙololuwar tashi. Duk da kowa yasan ciwo ne bana asibiti ba haka likitoci suka rufu a kanta domin ƙoƙarin ganin sun tsaida jinin amma abu na neman gagara. Har kusan goma na safe a gogon ƙasar babu wani cigaba, jikin Iffah ma ya fara saki alamar jininta yayi ƙasa matuƙa….

Tafiya saurayin yake tamkar zai tashi sama dan gaggawa, wani lokacin har tuntuɓe yakanci sai dai kafin ya kai ƙasa yay azamar taro kansa ta hanyar dafe duk abinda ke kusa da shi. Wurjanjan ya isa ƙofar gidan Dattijon da kowa yafi sani da suna Abu Huzaifah ya kwaɗa sallama da iya ƙarfin muryarsa har sau huɗu babu ko jiran a amsa masa.

Dattijo Abu Huzaifah Da mukafi sani da Kaka ya dakata da ga ɗinkin kwalliyar doki daya duƙufa yi ya dago suka kalla juna da Iyyani dake shara a tsakar gidan. “Kamarfa sallama naji Abu Jamaima a ƙofar gidan nan”

Kafaɗa yaɗan rausayar gefe da ajiye zungureriyar allurar da yake ɗinkin da ita. Kafin ya ce wani abu aka ƙara zungura sallamar a jajjere tamkar yaƙi. Kansa ya ƙara jijjigawa ya miƙe dajan tsaki. “Kai wasu dai mutanen sam basu da lissafi, irin wannan ai saka ɗauka tashin hankali ne”. Kaka ya faɗa cikin mita yana gyara takalmansa. Iyyani da takaici ya ƙulle itama ta bisa da kallo harya fice a soron gidan…

“Ayyub! dama kai ne kake ƙwaɗa irin wannan sallama haka? Lafiya dai ko?”.

“Da sauƙi dai Baba, amma amin afuwa bani da wani zaɓi bayan hakan. Saƙone daga Baba yaro”. Ya ƙare maganar da miƙama Kaka takardar hanunsa. Kaka ya amsa takardar yana ɗan juyata, sai kuma ya nuna hanyar shiga da faɗin, “Kaga shigo daga ciki”.

A tare suka shiga cikin gidan, Kaka ya buɗe takarda yana dubawa, yayinda Iyyani ta kawoma baƙo dake gaisheta ruwa. Kaka ya ɗan murmusa bayan gama karanta takarda tare da girgiza kansa. “Ayyub naga saƙo, sai dai kuma inaga basai naje da kaina ba. Zan baka saƙo ka kai masa nima. Ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa ya zama kaffara a gareta”

Ɗan jimm Ayyub yayi, sai dai kafin yace wani abu Kaka ya miƙe. Ɗakinsa ya shiga, kusan mintuna ashirin sai gashi ya fito da wata jakkar fata. “Kayi maza ka kai masa wannan. Kace kuma ina gaishesa”.

Cike da girmamawa Ayyub ya amsa da faɗin “Angama Baba. A huta lafiya”. Kai kawai Kaka ya jinjina masa yana murmushi. Sai da ya rakasa har ƙofar gida sannan ya dawo. Iyyani da duk ta shiga damuwa ko zama baiyiba ta jeho masa tambaya, dan tasan ma’anar wannan murmushin nasa bana farin ciki bane, yakan yisane a lokacin da wani abu ke masa ƙuna a zuciya

Bayan sallar azhar Ayyub ya iso masarauta. Zuwa yanzun har an fara raɗe raɗin mutuwar Iffah, duk da kuwa ya tadda masu maganin da suka isa suka tumbatsa da matuƙar yawa an tarasu kowa nata gwada ƙoƙarinsa da baiwar da ALLAH ya basa.

Baba Yayaroya furzar da nannauyan numfashi bayan ya amshi saƙon kaka a hanun Ayyub “Dama nasan da wuya Dattijo ya zo”.

“Amma duk da haka ka aika masa Baba?”.

“Ya cancanci a aika masan”.

“To amma miyasa yaƙi zuwa? Bayan kuma alamu sun nuna kai tsaye ma yasan abinda ke faruwa anan ɗin”.

Baba ya tsurama ɗan nasa ido na wasu sakanni, sai kuma ya girgiza kansa. “Ba lallai sani irin wanda kake tunani yayi ba. Dan nidai nasan baida wata alaƙa da abinda ke faruwa anan. Sai dai ya sani ta dalilin baiwar da ALLAH ya masa duk da shi yana gudunta ne”.

“Amma Baba….”

“Kaga Ayyub wannan ba lokacin tambayoyi bane. Bara naje muga ko za’a dace anan.”

Da kallo Ayyub yabi mahaifin nasa. Sai dai ƙasan ransa fal tambayoyine da yasan samun amsarsu zaiyi wuya a lokacin da yake buƙata. Yasan mahaifinsa gawurtaccen masanin magani ne irin na gargajiya dama na gusar da junnu. Shahararsa tasa Daular Ruman ɗaukarsa da bashi matsayin (Mai magani a gonar yaro) amma ya rasa minene dalilinsa na bama wancan dattijon girma mai tsanani duk da shi kowa bai sanshi ba sai da sunan mai ɗinka kayan doki…..

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button