Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 101

Sponsored links

Yana cikin wannan hali Mom tashigo, kamar ko yaushe murmushi dauke akan fuskarta, karasowa tayi ta zauna a hannun kujerar da yake, cikin kwantar da murya tace;

 

“Alhajina ni kadai!”……

 

Shiru yayi kamar bejitaba dan so yake tabashi space yanda ze samu damar yanke abinda ya kamata yayi…

 

“Kasan yanda nakeji a raina idan na ganka a cikin damuwa kuwa? Dan Allah ka tausayamin ka fadamin damuwarka kona samu salama a zuciyata, da yarda Allah kuma in tayaka nemo mafita”……

 

Sosai ya danji kalamanta sun sanyaya masa zuciya, shiyasa take da wani guri me girma a zuciyarsa saboda gwana ce wajan kwantarwa da mutum hankali, ko yanaso ya boye mata damuwarsa saiya kasa shiyasa babu abinda bata sani ba akansa har wanda be kamata ya fadamata ba saiya samu kansa da fadamata…

Nan ya kwashe duka yanda sukayi da Mami ya gayamata da yanda suka kare da shima Deen din har yace karya sake yazo masa gida gashin yanzu abun ya damesa…….

“Yallabai in banda abinka ai hannunka baya rubewa ka yar, be kamata kacewa son kar yazo ba kamata yayi ka bishi a hankali tinda yasan da maganar Hamida a kasa, kuma tinda tace saidai ya auri daya ai zabinka ya kamata ya aura tinda uba keda alhakin aurar da dansa, yanzu gashi ka kara bata damar da zata janyeshi sosai, tsap saita masa auren baka saniba ma!”……..

Dafe goshinsa yayi yana harhada maganganunta, tabbas abinda ta fada gsky ne, yin zuciyar da yayi kamar ya kara bata damane taci galaba akansa….

“Yanzu menene abunyi?”

Daukan wayarsa yayi ya shiga dialing number Deen, kira uku ya masa be dauka ba…..

 

Deen da suke cikin tashin hankalin neman fatima zainab wayarshi na jikinsa amma ko ringing bejiba……

 

Sosai ran dad ya baci yana ganin kamar Mami ce ta hanashi daukan wayarsa, wato tin baaje ko ina ba maganar sameera ta fito na janyeshi kenan?…. Dukda haka sai ya kasa hakura ya cigaba da kiransa,

 

Sai a kira na biyar sannan Deen yaji wayarsa na ringing, kamar ya share kawai ya fito da wayar, ganin Dad ne yasasa daukan wayar da sauri……

 

Tinda ya dauka yake zazzaga masa masifa akan rashin daukan wayarsa da wuri, yana sauraransa amma bece komai ba saboda abinda yake damunsa yafi karfin masifar da Dad yake, shiko jin abinda yake cewa bayayi dan hankalinsa baya wajan……

“My friend shut up! Bakaji abinda na fadamaka ba? Nace duk abinda kakeyi ka barsa kazo! Umarni nake baka ba shawara ba!”……

“Naji!”….

Yana fadin haka ya kashe wayar yanajin kamar zuciyarsa zata fado tsabar bacin rai, yana fama da nemanta kawai zece ya tawo, rasa abinda zeyi yaji dadi yayi kawai ya rotsa wayarsa a kasa, a take ta fashe into pieces, ko a jikinsa ya fasa Samsung din million plus sai neman ma abunda ze kara fasawa yake ko zeji dadi……

Baki sake suke kallonsa ganin ya fasa waya haka kawai dan sudai basuji yayi wata magana me tsawo a wayar dayayi ba hasalima su mami basu gane dawa yake waya ba, eesha ce tayi kokarin zuwa ta dauke masa wayar Umm ta rukota da sauri tana fadin;

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button