Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 30

Sponsored links

“Naji ni mugu ne but I’m a changed person now, I promise bazan kara miki masifa ba kuma bazan kara dukanki ba amma ki rama naki yanzu sai ki dena jin haushi”…….

 

Batace komai ba ta shiga shauda masa belt din da karfi a jikinsa, daga baya dataga kamar dukan baya shigansa tace ya mikohannunsa, mika mata hannun yayi ta shiga jibgarsa kamar mallama dalibinta…..

 

Dariya ta bashi sosai har saida ya kasa rikewa, betaba tinanin yarinyarta takai haka ba sai yau, wannan aka mata aure yanzu ai akwai matsala, harda ce mishi karya janye hannunsa sai tace ya janye, toh kawai yace mata ya cigaba da kallon ikon Allah dan an zuba mishi belt yafi so talatin a hannu and he didn’t complain kamar yanda yace…….

 

Sake sakkowa su Umm sukayi jin karar duka su a tinaninsu Deen ne yake sake dukanta, sai dai me? Gani sukayi Deen ya mika hannu tana zuba masa bulala yana murmushi kamar wanda ake yiwa abu me dadi, tabe baki mami tayi tace ‘sunfi kusa’, suka juya suka koma sama……

Saida tayi me isarta lokacin hannunsa yayi ja kasancewarsa farin mutum sannan ta dakata dan itama ta gaji…….

“Ki daure muje in koya miki karki auri foodie yace ze miki kishiya saboda baki iya girki ba, dama irina zaki aura baki da case dan babu abinda ban iya ba”…..

 

“Khaleel knows that I can cook and he loves me like that”…..

 

Nan da nan fuskarsa ta chanza, belt din data gama dukansa dashi ya dauka, a tsawace yace;

 

“Idan muna magana kina sakomin maganar wani namiji saina fasa miki baki”………

 

Tashi tayi ta shige daya daga cikin bedroom din dake kasa dan bazata tsaya ya hallakata a banza ba gashi ya dauki belt, in yace ze rama dukan data mishi ai suma zatayi yanda bata da kwarin jikinnan……

 

“Da kin tsaya ai, mara kunya fisararriya kawai!”…..

 

Zama yayi a parlourn ya kunna tv yana gadinta dan tsoro yake karta gudu dukda yaga kamar ta hakura amma ita ba abin yarda bace dan ya kula tanada wayo sosai, murmushi ne ya kwace masa daya tina abinda ya faru last night, wai yar yarinya da ita harta san tayi seducing mutum ya mata abu?, sai kuma ya hade rai tuno yanda ta rungume khaleel harya mika mata bindiga kamar wawa, yanzu duka khaleel yaji komai na jikinta, tudun kirjinta da komai?, kodai haka take yiwa maza idan tanaso su mata abu tinda rannan ce masa tayi tasan abinda zatayi a bata codeine kyauta, glass cup din dake center table ya dauka ya fasa shi ko zeji sanyi a ransa, chan kuma sai ya tashi ya fara bubbuga kofar dakin da take cikin daga murya yace;

“Ki zo ki bude kofarnan kona ballata! Yau sai kin gayamin wa da wa kika taba runguma a rayuwarki,Ki bude nace!”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button