Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 41

Sponsored links

Malam yace masha Allah,shiga hada hadan daurin aure akafara kamar yanda musulunci ya tanada,aka gayyato wa’yenda ke kusa da bakin masallaci da masu shaguna a kusa sannan aka dau………

Aka dauko goro da sauran abubuwan aka matso dasu kusa lokacin masallacin ya cika makil da jama’a, gadan gadan aka shiga hidimomin daurin aure kowa fuskarsa dauke da farin ciki zaa hada sunna, gyaran murya sheikh Abdallah yayi sannan ya fara da bismillah…….

“A’uzubillahis-sami’ul aleem, minash-shaydanir rajeem, bismillahir rahmani raheem, allahumma…”

Kallonta yan gurin suka hauyi suna murmushi, su dayake larabawa masu nuna affection dinsu a fili sai sukayi tinanin san da take masa ne yasata kasa shiru……

“Ba dole sai da waliyyi ake aure ba amma saboda yanayin rayuwa yanda komai ya zama sai a hankali yanada kyau a samu waliyy koda a cikin mahaifa ko yan uwa ko makusanta, da zasu zama shedu gudin bijirowar wani abu daga baya dukda ba fata ake ba”…….

“Mudai sheikh ka taimaka kawai a daura mana auren wallahi bamu da kowa a kusa”…..

Cewar khaleel kamar zeyi kuka…….

Murmushi sheikh jabbar yayi ya dafa kafadar khaleel yace;

 

“Gwara ku samo koda mutum daya ne habibee”…

Dan shiru khaleel yayi yana tinanin yanda zasuyi, kawai sai sameer ya fadomasa a rai, ya tina yanda sukayi da sameer akan zeyi supporting dinsa akan komai, yanzu this is the best time for that, murmushi yayi yace;

“Toh sheikh, Insha Allah akwai wanda zezo daga Nigeria”……..

“Masha Allah masha Allah”…..

Sheikh Abdallah ya fada yana kara yabawa da hankalin yaran…. Nan aka shiga sa musu albarka aka musu addu’a sosai…….

Mikewa khaleel yayi yace ta tashi su tafi…….

Har sun kai bakin kofa sheikh Abdallah ya kirasu, dawowa sukayi suka sameshi, nuna inda aka ajye sadaki yayi yace khaleel ya tafi dashi tukun, girgiza kai khaleel yayi yace a barshi a gurinsa saboda gobe zasu dawo zuwa gobe, ajyewa akayi kamar yanda ya bukata sannan suka sake sallama dasu suka fita………

Kamar jira fatima zainab take su fita daga masallacin tace;

“Yanzu shikenan ba zaa daura aurennan yau ba?”

Kashe mata ido daya khaleel yayi cikin tsokana yace;

“Haka kika matsu a daura auren?”…..

Itama kashe masa ido tayi tana dariya tace;

“Sosai ma”…..

Gumi ne ya shiga karyowa sameer tin bayan khaleel ya kashe waya, ya mike da sauri ya fara zarya a dakin kamar wani zararre, fadi yake “aure kuma! Aure! No! It’s impossible!”, sosai maganar auren ta daga masa hankali, yama zaace yana zaune khaleel yaci galaba a kansa bayan duk wahalar daya sha da kuma wanda yake kan sha, wallahi baze yiwu ba…… Haka yayita kai da kawowa har zuciyarsa ta kawo masa wani shawara da yake tinanin shine daidai, mafitar shine idan yaje ya zubawa khaleel poison a abinci ko a lemo ya kasheshi ya dauketa su tafi suyi aure, baze yiwu ace yana raye yaga khaleel ya aureta bashi ba……..

Sosai abinda ya gani ya daga masa hankali amma a haka baka ce ba, sosai mamaki ya kamasa ganin yanda mutane suka zama abun tsoro a duniya, ace alhaji habibu of all people ne da wannan aika aikan? Mutumin dayake wa kallon uba bayan dad, ashe mugune haka? Toh amma wa suke magana akai haka? Dan ko waye tabbas meshi yana cikin hatsari, da kuma ze gane waye daya taimakeshi, sai a lokacin ya gane dalilin dayasa akayi kidnapping dinsa, wato sun gano flash dinsu na tare dashi shine sukesan ganin bayansa, toh amma meyasa Alhaji Ibrahim yasa a kasheshi? Ko bakinsu daya da alhaji habibu ne?….. Wani murmushin gefen baki Deen yayi yace;

“Zakuci ubanku!!!”…….

“Toh ko ina sameer yake?”….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button