Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 45

Sponsored links

Itama ɗin dai switch up. Wasu zafafan hawaye suka silalo a kumatun ta. Ƙoƙarin sake kiran waccan number ta gwadayi knoking ƙofar da akai ya katseta. Da sauri ta yanke kiran da kashe wayar ma baki ɗaya ta ɗaga gadon ta tusasu har da takardar gaba ɗaya sannan ta sauka dan tasan bazai wuce Daneen Ammarah ba…

“Ibnati baki barci ba kenan?”.

Kan Iffah a ƙasa tai ɗan murmushi. “Yanzu zanyi Mamy karatu na kammala”.

“Masha ALLAH, ya kamata ki kwanta to dare yaja, nima zuwa zanje na kwanta”.

“To Mamy ALLAH ya tashemu lafiya”.

Koda Daneen Ammarah ta wuce Iffah ba kwanciyar tai ba, sake ɗakko wayar tayi ta cigaba da neman wancan layin da a yanzu ake cemata not available saɓanin switch up na ɗazun. Hakama number Malam Fawzan har yanzun. Daga ƙarshe dai barci ɓarawo gwanin iya sata ne ya saceta akan dole ta haƙura, sai da asuba ta tsinta wayar a ƙasa yashe….

Yau dai kam ta ƙudiri niyyar fita gaida tsohuwa Malikat Haseena da kanta, tunda dai jikinta Alhamdullah hatta saɓar ma sai inda ba’a rasa bane bai gama ba. Bayan hadimar dake gyara ɗakin ta kammala ta fita key ta sama ƙofar sannan ta shiga wanka. Dan duk da tausayin hadiman da takeji a yanzu batajin zata sake yarda da waninsu. Ta fito tana tsaka da shiryawa cikin ɗaya daga kayanta na gida akai knoking. Karasa saka abayar tayi sannan taje ta buɗe, a tare suka sakarma juna murmushi, tai ƙasa da kanta tana faɗin, “Barka da safiya Mamy”.

Daneen Ammarah takai hannu ta taɓa kanta da faɗin, “Kin tashi lafiya?”.

“Alhamdullah”.

“Haka ake so. Ga kayanki nan na amfanin yau, mun zaɓi yin hakane saboda gudun abinda zai iya zuwa ya dawo Ibnati, amma insha ALLAH kayanki na amfani na gab da kammaluwa, saiki shirya ni zanje sashen Umm Jasrah. Ki tabbatar kinci abinci sosai yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba”.

“Adawo lafiya Mamy a gaisheta”.

“Zataji, amma ki tabbatar kin canja waɗan nan kayan”.

Kai kawai Iffah ta jinjina mata. Amma a ranta tana mamakin minene aibun abayar tata? Tana cikin sabbin kayantama da take matuƙar ji da su. Shigowar hadimai biyu da kayayyaki ya katse mata mitar tata, sai dai batace komai ba bayan amsa musu gaisuwa. Fita ɗayar tai aka barta da wadda tafi yawan kasancewa da ita, tazo gabanta ta zube kanta a rissine. “Ya Zawjata-almilki bisa umarninki za’a shirya kayan”.

Karo na biyu Iffah ta amsa neman izini da umarni ga hadimai a gidan. “Ba yanzu ba, zaki mun rakkiya ga Mamma ne, ki jirani a waje”.

“Umarninki shi nake zaman jira ya Zawjata-almilki”.

Hadimar na fita ta taka inda kayan suke tana dubawa. Tunda ta samu lafiya kullum da safe za’a kawo mata kaya kala uku, washe gari za’a kwashesu koda daya kawai ta saka a sake ajiye mata wasu. Da farko ta ɗauka ko haka tsarin masarautar yake. Sai a yau bayanin Daneen Ammarah yasa ta fahimci ita akema hakan saboda tsaro. Waɗanda ranta yafi kwantawa da su ta dauka ta saka. Ta koyi ƙyau sosai musamman da suka kasance bakake da adon stones masu sheƙi da ɗaukar idanu. Ga farar fatarta data koma ja ƙaɗan saboda saɓar datai tamkar ta larabawa ta sake fitowa. Ɓoyayyun turarenta na wajen Kaka ta ɗakko ta saka, wani irin ƙamshi mai daɗi da saka zuciya nutsuwa ya fara ratsa ɗakin…

Sosai murmushi ya bayyana a fuskar tsohuwa Malikat Haseena saboda ganin Iffah akan kafafunta, takuma ji daɗin wannan ziyarar bazata data kawo mata duk da kuwa suna a sashe ɗaya ne. Iffah data kai zaune gefenta bisa tattausar dardumar da aka ƙawata falon da shi ta risinar da kai tana gaisheta da tambayarta yaya jiki?.

“Alhamdullahi ƴar albarka. Yaya naki jikin?”. Malikat Haseena ta amsa da kulawa har yanzu murmushi ƙawace da fuskarta.

“Naji sauƙi ai Mamma” (kamar yanda taji Daneen Ammarah na kiranta.

“To Alhamdullah ALLAH ya ƙara kiyaye gaba”.

Da amin duk hadiman wajen suka amsa. Malikat Haseena sallamar duk Hadiman tayi, tare da bada umarnin a shirya mata breakfast da Iffah. Hakan ya bama hadiman mamaki sosai, dan duk wanda Malikat Haseena zata buƙaci zaman cin abinci da shi ba karamin mai sa’a bane ba. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa aka kammala shirya komai, ita dai Iffah na kallon ikon ALLAH da tsagwaron mulki wajen wannan tsohuwa. A ranta kam tunani take shin wai idan haka matan suke waishi babban dodon nasu yaya za’a gansa kenan?. Bisa umarnin Malikat Haseena Iffah ta mike suka nufi wajen da aka shirya abincin. Zamansu dai-dai da shigowar amintacciyar hadimar Malikat ɗin ɗauke da wani ƙaramin kwano…

Shigar ƙamshin turaren Iffah hancin Hadima Banou ya saka jikinta fara tsuma. Hanunta na ɗan rawa ta sunkiya zata ajiye kwanon suka haɗa ido da Iffah. Zabura tayi da sauri ta miƙe kanta a sunkuye. Iffah ma dake jin jikinta na wani irin yamutsawa ta sake kallonta da kyau, haka kawai matar batai mata ba, gata wata irin doguwar mace gandaƙaiƙai kamar namiji babu wani fasalin mata tattare da ita… Malikat Haseena da rawar jikin Hadimar ya bata mamaki itama ta tsura mata idanu. Sai dai mulki da kasaita baisa ta tanka ba. Hadima Banou dake jin kamar ta zura a guje saboda yanda take jin jikinta ta zube ƙasa, cikin rawar hannu ta fara yunƙurin haɗama Malikat Haseena abinci.. Iffah dake mata kallon nazari ta dakatar da ita. “Kinga jeki kawai”.

Ai kafin ma ta rufe baki tuni ta mike zaram kamar wadda ke akan wuta. Iffah da gaba ɗaya abin ya gama ɗaure kanta ta fara haɗama Malikat Haseena abincin da kanta. Itako Malikat Haseena komai bata kawo a ranta ba game da yanayin Amintacciyar hadimar tata, saboda takan ganta a wasu yanayi daya fima hakan, dan haka ta jima da sakata a jerin masu aljanu…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button