Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 8

Sponsored links

Cikin sauri PA Lukman yace” Ban gane wakake nufi ba Sir Khamal? Cikin wani irin murya ya bashi amsa da” MY LADY BOSS!!

Kamin PA yace wani Abu ne Sir Khamal ya miƙe yana masa umarni ya biyosa da sauran kayan amfanin sa zuwa Compound ɗin Company n , yana ɗaukar brief case nashi , a zuciyar sa yana faɗin ” Sakaci na ne, i make a great mistake , dole na nemo ta ,sai na azabtar da ita da kalon izayar da bata taɓa sanin shi ba …. Na tsani na buɗe ido naga fuskar ta na mun gizo , ko a ina take in takai binnin sin nisa , sai na nemota………. Moton shi PA ya bude masa yana shigewa Driver yajah sa suna barin farfajiyar Company n…..

Inalallahi wannan wani irin mutum ne ? Cewan Sumayya tana ɗaga Lauratu da ta ganta kwance kaman matacciya , yayi mata Raga-raga sam bata iya motsa ƙafanta , wannan ai fyaɗe yake maki Lauratu , kuma kike zaune dashi? .

Kuka Lauratu keyi ta kasa magana , cike da masifa Sumayya tace ” Ke kike zaune dashi …cikin kuka Lauratu tace “Sumayya yaya zanyi dole ce tasaka hakan, inda ina da inda xanje xan gudu , Wallh banason shi , Auren haɗi aka mana babu yanda na iya , amma bana son Dan Asabe …..ta ƙare maganan tana rushewa da kuka mai ban tausayi.

A’a da yanda zakiyi , matso kiji wannan shawarar in Kim amince to ayi tafiyar dake”. Kunnen Lauratu Sumayya ta nufa tana mata magana ƙasa-ƙasa ….tana gama faɗa mata maganan , kawai taga Lauratu tayi tsalle ta miƙe tana nufar Sif ɗin ta ,tana fiddo da kayan ta!

Lauratu meye haka? Ke barni yanxu mu tafi kawai. Saurin kamata Sumayya tayi tana cewa ” ba yanxu ba , sai gobe da subahin fari… Bari na fita da sauri kar muna fukai su ganmu a fara tunanin wani abun…..

A ƙofa Sumayya ta tsaya tana kai hannun ta haɗi da ɗaukar hijabin ta tana cewa ” Bari na kai mawa Mai lapo kuɗin ta , na huta ai an maka …sakin baki Mmn fati sukayi Suna mmkin waya ba Sumayya kudi har zata biya lapun dubu Ɗari da ɗori???.

A zauren gidan ne da fitowar Sumayya sukayi kiciɓus da Ibrahim wanda ya kasance maƙocin su….a’a Sumayya kece? Eh bagini nan gani ba…ta bashi amsa tana kallon sa fuska babu harka…ganin ya tsaya kame ² ya sa Sumayya yin gaba ,sai kuma taji yana cewa ” Sumy don Allah minti ɗaya!

Dawowa Sumayya tayi tana cewa ” Ina jin ka? . Amm am am…don Allah Ibrahim kayi maganan ka sauri na keyi… Yi hƙr dama Sumayya Wallh tsawon lokaci na ɗauka in a jin son ki a zuciyata”….. Kallon shi tayi kamin tasa dariyar shakiyanci tana cewa” Ibrahim duka duka yaushe ka girma? Yaushe aka gama maka tsarki???? Da har zaka zo ka kalli mace kaman Sumayya kana cewa ” Wai kana So?? U Are nonsense”. Tana faɗin haka ta bar shi nan tsaye da baki sake…..

Wani irin gudu motocin biyu keyi a famfalen titin hanyar ,kamin naga sun haura railway station suna wani irin gudu da moton tsere ,ihu naji samari da ƴammatan wurin matasa nayi suna kirar suna kaman Haka ” FAHAD! FAHAD!! FAHAD!!!

_Littafin na kuɗi ne normal group ₦300 vip group ₦500 spc ₦1000 zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account details…6037312299 Mohammed A’isha keystone bank Idan Vtu trnsfer ne kiyi ta wannan number 09061466409 zaku na iya fara payment ɗin cox free page ba da yawa xanyi ba…_

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button