Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 8

Sponsored links

Kamar an dasa Abraham haka tsaya jikinsa na rawa kansa ya sara sosai, wannan shi ne karan farko daya yi mata kyakkyawan kallo, kallon da ba zai taɓa shafewa a cikin ƙwaƙwalwarsa musamman yanzu da yake cikin yanayin ciwon hauka, haukan kuma bai sanya ya manta wani kyakkyawan gurbi dake zuciyarsa ba.

Ko a baya bai san haka kyan jikinta da surarta yake ba. Malama Majeederh na tsaya gaban mirror ta ɗauki wani body lotion tana dubawa ɗago kan da za ta yi taga mutum tsaye a bayanta ta cikin mirrorn.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ta furta cikin tsoro ta rufe Idanunta domin bata gama tantance waye ba, ta ƙara buɗe idanu ta cikin madubi ga mamakinta hawaye ta gani kwance cikin idanunsa sai a lokacin ta kalli cikakkiyar fuskarsa.

“Little?” ta ce da mamakin domin ita ta gama sanyawa a zuciyarta baya raye a duniya. Yana tsaye bai motsa ba, hawayen idanunsa bai tsaya ba, abubuwa ne da yawa suke son dawowa cikin tunaninsa wasu tsofaffin memories na gilmawa ta cikin jijiyar dake motsawa tunanin ko wanne ɗan adam a cikin ƙwaƙwalwa.

Su yake ya tambayeta “Me take a nan? Ya yaga ta take? Waye ya taɓa ta yanzu ya yanke hannun ko waye, me ta yiwa jama’ar gari? Shin daman haka addinin na su yake, mabiyansa basa yiwa kansa adalci, basu kyakkyawa na ciki ba ina ga bare?”

Bakinsa ya a yi masa nauyi, tunaninsa ya tsaya kamar yadda take kallon cikin idanunsa haka ita ma yake kallonta,irin kallon nan da ba kowa ne ya isa ya fassara ma’anar shi ba.

“Jee” Abraham ya faɗa tare da yin inda take, kafin ta juya da nufin matsawa ko ɗaukan hijabi gaba ta jita nan naɗe jikin mutum ya ƙanƙameta a ƙirjinsa kamar wani zai ƙwace ta, tamkar zakin daya shekara yana neman abin farauta bai samu ba sai yanzu.

Duk yadda da su ƙwace jikinta kasawa tayi, fargabarta ɗaya kada wani ya shigo zargin da ake mata ya tabbata, domin babu wanda zai yarda ba da saninta Abraham ya shigo ba.

“Ka yi hauka?” “No!”

Ya bata amsa, amsar data bata mamaki tasha ce masa “Ka yi hauka ne” kai tsaye zai ce mata “Yes, Mahaukaci ne ni Jee” amma yanzu ya bata amsa da “No!”

Hakan na nufin akwai wani abu a ƙasa.

A lokacin kuma ta lura da yanayinsa, shigarsa, sauyin tunaninsa da kamanninsa everything. Majeederh tsayawa tayi tana kallon Ikon Allah, ba zata iya ciwon baki ba, ba zata iya kokawa ba don haka ta ja idanunta ta runtse ƙirjinta na ɗagawa a saitin nasa ƙirjinsa sosai kuma hakan ke taɓa Abraham, tun tuni ta san Abraham bai san wani abu mai kama da tsoro ba, bai san haƙuri ba, balle ace kayi haƙuri ya yi, bai ladama ba, bai san ya yi laifi ba, taurin kai ba zai taɓa abinda bai niyya ba. Abu ɗaya ne da shi yana da tsananin tausayi baya ƙaunar ganin hawayen mace yanzu zai riki ce.

Mamakin ganinsa kuma ya sata kasa ɗaukan mataki.

“Am not crazy Jee, ni ba mahaukaci ba, am not bad, an kai ni gidan mahaukata, kada ki bari wallahi zan kashe kowa”

Jeederh ta tattara ƙarfinta ta hankaɗe Abraham tare da nufar wajan wardrobe zata ɗauki hijabi cikin saur ya biyo ta tare da riƙe hannunta ya sa ƙafa ya daki wardrobe ɗin nan take ta tsage murfin ya faɗo. Ta sanya hannu ta zabga masa mari, ta ƙara zabga masa mari rai ɓace irin ɓacin ran da ko a gaban Abbu bata nuna ba lokacin daya koreta daga gidansa Idanunta ya kawo ruwa ya kwanta ta nuna shi da hannu tama kasa cewa komai.

Murmushi Abraham ya yi yana shafa fuskarsa wane yatsun hannunta ya kwanta sosai cikin gurɓatacciyar Hausar shi maganar a rarrabe da ƙarfi kuma ya ce..

“Beat me, beat me…If that will make you happy” ya cije baki tare da sanya hannunsa ya hargitsa kansa da zafin nama ya dinga kaiwa ko’ina duka hannunsu ya fara zubar da ji ni ya juya zuwa inda take kamar zai shigeta ya ce

“Idanunki ya bayyana laifina,ni na ce maka I’ll be back, sooner or later, bana da laifi Jee babu laifi wajeni” duk ya dagula hausar tashi wacce yasan ta fahimta. Ya kama hannunta ta ƙwace da sauri cikin kakkausar murya da riƙe kanta ba tare data bari ya fahimci halin da take ciki ba ta nuna masa ƙofa ta ce “Out, ka je can kayi haukanka mahaukaci”

“No, am not”

“You’re Mad” da ƙarfi ya ce “Am not, you stop listening to me” ya faɗa yana matse kafaɗarta idanunsa kamar za su faɗo ƙasa ya zaunar da ita saman gefen gado, tare da zubewa a gabanta ya ɗora kansa saman cinyarta kamar yadda ya sama, wani irin raunataccen kuka ya ƙwace masa, ya dinga yi kamar wani ƙaramin yaro tunda take bata taɓa ganin hawayensa ba balle kuka yau gashi yana rusa mata kuka kamar ance masa Denial ya mutu ko David ko Kiristi. Ba zata iya tantance lokaci daya shafe yana kukan ba, zuciyarta motsa rauni irin na ɗiya mace ya so kamata tausayi irin na uwa da ɗanta ƙwance akan fuskar Malama Majeederh.

Tana son bashi baki akan ya tashi ya tafi, ya ƙara yin nesa da ita fiye da yadda ya yi ta bashi labarin halin da itama take ciki, tasan faɗa ba zai taɓa yiwa Abraham ba, ko mutanen duniya ne za su taro a nan babu abinda ya dame shi.

A hankali ta sanya hannu zata ƙara ɗaukan hijabi caraf ya riƙe hannun tare da ƙwace hijabin ya zuba mata narkakkun idanunsa wanda sukai jajir while he’s still crying.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button