Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 13

Sponsored links

Shi a fad’ar sa daka ta6a Ayush gwara ka ro’ki mutuwarka,

Domin duk duniyan nan ba wanda yake so sama da d’iyarsa Ayush, ko cinyaka ce ta cije ta saiya zaro hannunsa ta cikin madubi ya mur’kushe ta 😳😳

(Anya kuwa d’aukar fansar Junaid zaiyu akan d’iyar Bara’atu kuwa 🤔).

___________________________

Ihun da Mommy tayi ne ya jawo hankulan kowa na gidan,

Ayush tana cikin cusa abinci sai da ta razana daga zaune ta mi’ke tsaye, sarkin tsoro har jikinta ya Fara 6ari tayi cikin toilet da gudu ta danna sakata!

Security gidan kuwa suma da gudun gaske suka shiga cikin d’akin direct d’akin Junaid suka nufa saboda sun san duk wani problem daga d’akin Junaid yake fitowa,

Suna shiga cikin d’akin suka tarar da abun al’ajabi, zaro idanuwa sukayi waje sun firgita da ganin Junaid a haka ga kuma mommy a shanye a ‘kasi sumammiya, cikin zafin nama suka nufi gurin da Junaid yake Gadan-gadan sun d’ago hannu zasu jawo Junaid nan sukaji an had’a kayuwansu biyu aka gwara kamar daga sama kuma basuga kowa ba, ba ‘karamin buguwa akayi musu ba kwakkwalwarsu ne ya fara juyawa kafin nan kowannen su suka fad’i sumammu, sauran two bodyguard suma ganin hakan yasa suka nufi gurin babu tsoro a fuskarsu zasu sa hannu su finciki Junaid daga jikin gini sukaji an sha’ko wuyansu duk su biyun an d’aga su sama kakaki suka farayi suna ri’ke wuyansu

,saiga mai gadi shima ya shugo da gudu cikin d’akin abunda ya ganine yasa shi tsayawa cakk ganin gardawa a sama suna lilo da ‘kafafuwansu kuma bai ga abunda ya d’agasu sama ba, nan take yasau fitsari a wando jikinsa ne ya hau 6ari,

Su kuwa sai da numfashin su ya tsaya cak sannan aka wurgar dasu kan mai gadi da yayi sumar tsaye, sai yaraff duk su biyu akan mai gadi shima saida yayi asalin suma jin Manya-manyan gardawa a samansa.

Bayan 1hour Ayush dai tana cikin toilet jin ihun da akayi yasa ta 6oye a gurin, tana tsugune har ta gaji jin babu komai yasa ta bud’e ‘kofar toilet tana Le’ke-le’ke cikin sand’a take tafiya har ta sau’ko falo babu kowa, A hankali take ‘kiran sunan “Aunty, Aunty, kina Ina ne” taji shuru ba’a amsa mataba, ta nufi kitchen tana bud’ewa taga wayam ba kowa

Anan fa ta fara rawar jiki tsoro ne ya bayyana akan fuskarta, “innalillahi wa inna’ilaihi raju’u, Allah yasa dai ba 6arayi bane suka shugo gidan, naji ihu kuma yanzu babu kowa”

Tana magana cikin kuka hawaye ne sharaf-sharaf suka fara gangaro mata a saman kunci, ta lalle’ka ko Ina amma bataga Mommy ba, ta duba agogon saman bango 12:30 ne.

Tayi hanyar waje ko zataga security hankalinta zaifi kwanciya,

“May be an kirata ne a asibiti” a cikin ranta take wannan maganar!

Abun mamaki ko dataje waje bata ga kowa ba hatta mai gadin sai haske Dara-dara ta ko Ina,

Wani irin yawu ta had’iya ga gumi kuwa daya fara tsirto mata, kakkarwa ta somayi tana tunanin kar itama a sace ta

Da gudun gaske ta koma cikin d’aki tana maida numfashi,

Ta zauna a saman kujera 1seater dafe kanta tayi ta fara rera kuka

Ita kanta ta rasa shin kukan mai takeyi

Shin na rashin ganin mutanen gidan ne ko kuma kukan tsoro ne, tana cikin wannan halin ta tuno da Junaid! Da sauri ta d’ago kanta idonta sun rine sunyi jaa “Ina yaron gidan, ko shima an sace shi” tana magana tana kallon upstairs d’in d’akin Junaid

Cikin rawar jiki ta mi’ke da sauri tayi hanyar d’akin Junaid tana taka matakala da sauri-sauri kamar zata kife,

Tana zuwa daf da d’akin tasa hannu zata bud’e naushin da Junaid yayi mata ne ya fad’o mata a rai, tsayawa tayi cak cike da fargaba ta fara tunanin “ya za’ayi na shiga d’akin wannan azzalumin d’azu ya naushe ni yanzu kuma ban san wani muguntar zai ‘kara mun b, ta juya zata bar gurin ta koma falo sai wani tunanin ya sake fad’o mata shin idan kuma shima ansace shi fa? Inma ba’a sace shi ba ai zai fita ya nemo mutanen gidan!

 

Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba ta sake buga ‘kofar still ba motsi

Almost 30minute tayi a tsaye tana sa’ke sa’ke a raanta

Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai, cikin rashin sa’a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta,

Juyowa tayi ta kalli gurin ganin Mommy a kwance yasa taji fad’uwar gaba,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button