Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 61

Sponsored links

Tana gama bada labarin ta zube a kasa tana birgima, deen da jijiyoyin kansa suka firfito tsabar bakin ciki da takaici besan sanda ya dagota ya hau bubbugata da bango, fuzgota daga hannun deen dad yayi ya shiga dukanta yana kuka yana fadin;

“Kin cucemu! Kin cuceni! Allah ya isa sakani na dake! Kin rabani da abinda iyalina abar kaunata! Kin cuceni!”…..

Fizgewa tayi daga hannun dad ta tashi tayi wani ihu ta fita a guje, binta deen yayi ya zare belt dinsa ya shiga zuga mata tana gudu yana binta, har a lokacin bata daina bada labarin wasu abubuwan da tayi daban ba, daga karshe ma saita fara kokarin cire kayanta alamun hauka ta kamata, sawa deen yayi aka bude kofa ya cigaba da zuga mata belt din harta fita daga gidan, tana fita tayi tsirara ta ruga a guje tana ihu tana kara bada labarin abinda ta aikata……….

(Gareku masu bin bokaye da kuma mallamai; wallahi ku tuba tin yanzu dan babu yanda zaayi kuyi kyakkyawan karshe, inaso kusani kuma rana dubu ta barowa rana daya tak tame kaya amma rana dayan nan yafi tsawon ranakun dubun nan sau goma, sannan duk nisan jifa kasa ze dawo, kina ganin kamar komai yana tafiya yanda boka ya miki ko mallami toh wallahi wallahi asirinki ze tonu ko badade ko ba jima, Allah yasa mudace ya doramu akan tafarkin gsky)…………

Dawowa ciki deen yayi lokacin mami ta bar parlorn cuz tana bukatar tayi digesting abinda ya faru yanzu so bazata iya saurarar dad dake neman afuwarta ba, Umm ce tabi bayanta amma ko kafin ta karasa mami ta rufe kofa, dawowa tayi daidai lokacin da deen ya shigo……

Wayen’nan sune sakonni guda biyu da aka turo mata a jere da unknown number, sakon farko ne ya bata mamaki na biyun kuma ya bata tsoro, saidai duk a cikin lulubenta ta gagara gano wanda ze iya mata message din…

 

Maimata sakon tayi sau uku kafin tayi deleting messages din sannan tayi blocking number….

 

A sanyaye ta mike ta fara shiri tana kara maimata sakon aranta, wai ta bude idonta ta fuskanci masoyinta da bata da kamarsa a duniya, toh tana da babban masoyin daya wuce khaleel ne? Mutumin daya sota tin batasan kanta ba? Babu flaws dinta dabe sani ba amma ko sau daya be taba nuna gazawarsa a kaunarta ba, ta tina lokacin da zeta rokonta akan ta dena shan codeine amma tana sa masa kuka shikenan ze bata, toh akwai soyayyar da tafi mutum yaso abinda kakeso? Bata kara tabbatar da khaleel na sonta ba saida deen ya shigo rayuwarta, ya shigo rayuwarta da wasu irin abubuwa da batasan yanda zata fassara ba, ya hargitsa mata tinaninta da nitsuwarta da shegen takurarsa da muguntarsa, a lokacin ne ta gane khaleel rare gem ne saboda a gurinsa kadai take samun farinciki idan deen ya bata mata rai, duk da haka tana ganin kimar deen sosai wanda tasan ko shi baze yarda ba, bakomai bane yasa take ganin kimarsa ba illa sadata da mahaifanta dayayi sannan haka kawai bata san abinda ze cutar dashi, batasan da hakan ba kuma sai lokacin da akazo za’a kashesu yace taja motar ta tafi shi ze ji dasu dukda yasan za’a kashesa, wannan abun ya kasa barin ranta har yau, wayennan abubuwa guda biyu ne sukasa take ganin kimarsa, amma fa hakan bashi zesa ta bari ya takata yanda yaso ba……. Tabbas bata son khaleel at first but as time goes on ta gane bata da kamarsa shiyasa ta koyawa zuciyarta sonsa, and yanzu tana jin she can do anything for him, she just wants to see him happy too……

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button