Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 42

Sponsored links

Ya fada kamar shida wani ne a gurin, sun dade basu hadu da sameer ba tin bayan yace mishi yarinyar bata wajansa, yanzu ko dole ya nemo sameer dan ta hanyar sameer ne ze gane duk wani abu dayake san ganewa………

A system ya dauko number sameer ya sata a sabuwar wayarshi ya shiga kiransa……

Sameer da har lokacin be dena kaiwa da kawowa yaji wayarsa na ringing, ba bata lokaci ya daukota dan shi mutum ne me daga ko wata waya idan an kirasa, ga mamakinsa sai yaji muryar Deen, muryar da be taba tinanin ze jita nan kusa ba……..

“Ina ka shiga ne sam?”….

Ya juyo muryar Deen for the second time bayan maganar farko da yayi be kulasa ba saboda mamakin daya shiga……

“Kai zan tambaya boss, na kira wayarka harna gaji”…..

“Yeah I lost my phone, ya ake ciki ne?,kai kaki barin naija ko?”………

“Hmmm ai gashi zan bari dan dole yanzu, dubai zanje”…..

“Me zakaje yi a dubai kuma?”….

“Wani case zan kashe!”……

“Ikon Allah! Ya labarin budurwar ka kuwa?”……

Deen ya tambaya dukda yasan baze samu information akanta a gurin sameer ba tinda yasan khaleel tabi suka gudu……

Nan da sameer yaji an tabo mishi inda ke mishi kaikayi, cikin kunar rai yace;

“Akan haka zanje dubai ai, tana tare da dan iskan chan, kaji wai aure zasuyi shine sukeso na zamar musu waliyy?”…….

Gabadaya Deen yaji jikinsa ya fara rawa, wayar ma saita nemi ta zame daga hannunsa, ashe dagaske sun bar kasar? Wannan wata irin mahaukaciyar yarinya ce zataje a daura musu gantalellen aure da wanchan shashashan, inko hakane he needs to do something, kasa controlling kansa yayi cikin daga murya kamar ze fasa wayar yace;

“A dubai ina suke sam? Are they living together? Idona idon yaran chan saina kasheshi wallahi! I must kill him!!”…….

Wani iri sameer yaji yanayin yanda Deen ya zuciya da abinda yake furtawa, ya maze yace;

“Relax man! Meya hadaku haka? Nima so nake na kashe shi”…..

Cewar sameer yana jindadi ya samu partner din ganin bayan khaleel…

“Ya shiga gona ta sam, ya shiga gonata, in ban kasheshi hankalina baze kwanta ba!!”….

“I understand boss, bansan ina suke a dubai yanzu ba but karka damu zan kiraka inyi updating dinka duk yanda ake ciki”…….

“Ka tabbatar ka kirani sam! Ka tabbatar ka kirani!”……

Deen ya fada yana kashe wayar har lokacin kuma yanajin wani daci a ransa, abu dayane ke damunsa akan zuwa dubai din da sukayi, yasan dole a guri daya suke maybe ma daki daya, wani abu ne yaji ya shake mishi wuya yaji bazai iya jira sam ya kirasa ba gwara yaje dubai din ya nemesu duk inda suke yaci ubansu duka daga ita har shi, sai ya tabbatar yayiwa khaleel jina jina sannan ze kyalesa, itako sai ya babballa kafar bin saurayi ya kuma sumar da ita, be damu ba koda zeyi jinyarta daga baya gwara ya samu yaci ubanta tukunna, in banda rashin zuciya daya fara samun shi yanzu wai har sawa yayi ake mata exam gudun kartayi losing semester amma wawuyar tana chan tare da wani gardi saboda ta rasa mafadi….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button