Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 13

Sponsored links

Yusrah ne ta amshe da cewa” jubiki fah Kaman ba mace ba ,waye zai taho inda kike a haka? Waye mahaukaci? Dole suyi baya , kince baki da iyaye , Ni na zama iyayenki , to naji duk da kasancewar kin girmemun indai zaki daina abun da kikeyi na wannan shan barasar a matsayin ki na mace , to ki zo gidan mu ki zauna dani , idan kuma kina da iyaye ina roƙon ki ki koma gare su……Sauran numfashin Bilkisu yasa Yusrah fahimtar bacci ne ya ɗauke ta saka makon allurar da sukayi mata.

Sauran likitocin ne aka hau kallon kallo ,na shin da gaske Yusrah zata ɗauki wannan bugaggiyar takai gidan su ,ita da ke cida kanta?”.

Ku ɗauko gado a sata , ku Kaita room 24 . Suka tsinkayi Muryar Yusrah ya katse su ,wanda cikin sauri suka fara cika umarnin ta….

Kallon mai hayan Safna tayi kamin tace ” Ka taimaka mana dai ashekara dubu ɗari….mlm sabo ne yace ” A’a indai yayi maku ɗari da hamsin to , saboda gidan nan fa duka ku zaku zauna ciki ku kaɗai ai hakan yayi ashekara.

Himm to bdmwa Laurat ku shiga mana da kayan ku mu fara gyarar gidan , ga kuɗin mlm sabo mun gode cewan Sumayya tana bashi kuɗin a dunƙule…washe baki sabo yayi yana godiya “.

 

 

 

 

 

Safna ki zauna keda Umma mu bari da Laurat mu shiga kasuwan gari n nan mu haɗo mana kayan abinci ,kana na dawo mu nemi gidan aiki , don Ni dai aikatau zanyi ban san kan garin ba tukunna .mlm sabo zanyi ma magana ya nema mun gidan aiki sai mun dawo.

A dawo lafiya Safna tayi masu tana shigewa ɗaki da Umma”.

Gidan malam Ilu babu masaka tsinke saboda jama’a cike harda masu lapo dasuka zo zasu sai da gidan tare da tafiya da Sumayya….Ganin ɗaki babu kowa har kayan su wannan yasa su fahimtar Sumayya ta gudu….Ɗakin Lauratu a ka duba ganin ƙofa a buɗe ko ta ɓoye cike ne , nan da shiga aka ga ɗan Asabe tsirara ƙwance a sume haihuwar uwa n shi…Salati su Rita da Mmn mujahida suka sa suna fitowa da gudu maza na shiga ɗakin don ganin halin da Ɗan Asabe ke ciki rai a hannun Allah warwassss…..

Mama Atine ce ta shigo zaf zaf itace uwar lapo tana cewa ” gafa kuɗi tun jiya Sumayya ta aikomun da dubu ɗari da hamsin sharrrr….ɗari da Hamsin???? Matan gidan suka haɗa baki cike da mmki ,kamin suce to ina Sumayya na ?.

Kwana huɗu a Zaria kuɗin Sumayya ya ƙare a cefane kuɗin moto dana kama haya…wannan yasa safiyar talata ta miƙe tana sa hijabi don fitowa neman aikin gida shara girki ko wanke wanke . Mlm sabo ne yayi mata rakiya zuwa wani gida kana yace kunga gidan idan zaki shiga a akwai wani inji da sai ya lacceki tassssss sAbosa tsaban dukiyar da Allah ya basu. Mai gidan yayi gomna yanxu haka ministar ne ,ki shiga da addu’a Allah yasa ki samu , to suna da yara? Ta tambaye shi kai tsaye… Eh kaman ɗan su ɗaya a duniya shima baya ƙasan nake tunani.

To Mlm sabo na gode. Sumayya tayi maganan tana nufar tamfatsetsen gidan kaman hotel saboda girma da tsaruwa ….Sai da masu tsaron gidan suka gama mata tambaya da lacce sannan suka nuna mata hanyar sasan matan gidan… A farfajiyar gidan ne tana can tana tafiya tana mmkin wannan wani irin daula ce da dukiya aka zuba a gidan nan kawai taji tayi kiciɓus da mutum , waya na faɗi ƙasa nan take ya tarwatse…..

Oh God! Matsalar ƴaƴan talakawa kenan duk idan suka zo wuri a Sara ce , taji wata murya cike da masifa ta ɗirar mata. Saurin kai hannun ta ƙasa Sumayya tayi tana cewa ” Kiyi hƙr ta ɗago ta na miƙa mawa BINAFA wayar ta, wanda hankaɗe Sumayya tayi tana nufan moton ta tana shigewa , don kun san ta dawo Gidan Hjy Juwairiyya da zama…..

topa! ƙaƙaƙaƙaƙa…….koya abun zata kasance ,shin mahaifiyar Sir Khamal zata ɗauki Sumayya ko ko? Ya kuma zata kasance tsakanin Sumayya da Khamal?

_Free page na dab da ƙarewa ki hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS…._ _Littafin na kuɗi ne normal group ₦300 vip group ₦500 spc ₦1000 zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account details…6037312299 Mohammed A’isha keystone bank Idan Vtu trnsfer ne kiyi ta wannan number 09061466409 zaku na iya fara payment ɗin cox free page ba da yawa xanyi ba…_

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button